06/04/2026
👉BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA MASU SON KAWO GYARA A ƘASATA NIGERIA🫷
Bismillahirrahmanirrahim.
Tabbas duk wanda yake da kishin wannan ƙasar mai albarka abin ƙauna zai damu akan irin yadda wannan ƙasar take kuma zai shiga cikin ɗemuwa da baƙin ciki ba wannan ƙasar kaɗai ba hadda ƙasashen musulmi baki ɗaya.
Don shi ne naso kasancewata ɗaya daga cikin masu tunanin samar da gyara awannan ƙasar dama sauran ƙasashen musulmi n***a ya kamata inyiwa makamanta na bayanin yadda Yakamata mu samar da wannan gyaran da kuma hanyoyin da ya kamata mu bi da kuma matakan da zasu taimaka wajan samar da gyaran a aikace ba tunani kawai ba.
Amma kafin yin bayanin waɗannan ababen ya kamata mu amsama kan mu waɗannan tambayoyin:
Shin dagaske gyaran muke so?
Shin ba muna tunanin gyaran bane don ba adamawa damu bane?
Shin munshirya ma samarda gyara?
Shin manufar mu gyaran ne ko ta hanyar mu ko ta hanyar wanin mu?
Waɗannan tambayoyin dole ne ga duk wanda ke son samar da gyara ya amsa su domin su ne babban mabuɗin da zai ba shi damar shiga a cikin wannan tunanin kuma ya zaburar da shi zuwa ga hakan.
DOKOKINDA SU NE SUKE GUDANAR DA DUNIYA.✍️
Wannan duniyar da kake gani tana canzawa daga hali zuwa hali rana tafito tafaɗi wata yafito daga baya yaɓace taurarin da ke sararin samaniya iskan da ke bugawa damanar da ke zowa ta wuce wani yamutu wani yarayu wani yasamu wani yarasa duka suna gudana ne akan wasu dokoki wanda sanin su shi ne babban sababi wanda ke taimakawa wajan samar da canji,a baya anyi dauloli da yawa wannan daular tatsayu wannan kuma taroshe wadda tatsayu ta tsayu ne saboda waɗannan dokokin wadda tarushe ta rushe ne saboda waɗannan dokokin haka Allah ya halicci wannan duniyar,riƙo da su shi zai taimaka muna mu samar da gyara da canji.
Waɗannan dokokin ga su kamar haka:
A-doka ta tsarin duniya.
B-doka ta tsarin addini.
Waɗannan su ne abubuwan da ke gudanar da duniya, duk wanda yake son samar da canji amma yace bazaiyi riƙo da su ba toh tamkar mai mafarki ne,wanda yayi riƙo da ɗaya daga cikin su zai samu tawaya a cikin gyaran sa,wanda ya riƙe su toh shi ne wanda zai samarda canjin da ake buƙata,wannan zai bayyana idan muka zo bayanin waɗanda s**a samarda canji ga Al'ummar su.
Amma kafin komai ya kamata mu suranta wannan ƙasar ta mu surantawa mai kyau saboda shi zai sa mufahimci ta inda zamu farawa,a nawa hoton ina ganin wannan ƙasar da ma kasashen musulmai tamkar jirgin ruwa ne yana tafiya akan ruwa sai ya haɗu da wani tarin yashi sai yamaƙale ko kace kamar mutum ne ya faɗo daga sama sai yakare kaga ba zai yiyu ba ace yanzu ake son ya miƙe tsaye ba dole ne sai anbi matakai kamin ya miƙe.
MATAKAN GYARA.✍️
Tabbas ɓarna ita take da sauƙi amma gyara yana da wahala dole akwai buƙatar abi wasu hanyoyi domin samar da gyaran.
Matakin farko:shi ne matakin gyara na ɗaiɗai ku,dole ne Ni da na keson kawo gyara infara da kaina takwana saboda wanda bai gyaru ba ba yadda zai gyara wani,saboda haka wajibi ne ingyara kaina in zamo mai kyawawan dabi'u da halaye in zamo mai adalci mai gaskiya da riƙon amana mai hangen nesa wanda yake da cikakkar yadda da Allah dadai sauran sifofin kwarai ababen yabawa.kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yake cewa"Allah mai tsalki ne baya karɓa sai mai tsalki"kuma kamar yadda Allah yake cewa"sanidai kaɗai Allah yana karɓa ne daga masu kiyaye dokokin sa".saboda haka samar da gyara zaɓi ne daga wurin Allah shi kuma Allah baya zaɓar ƙazanta da gurɓatattar zuciya.
Mataki na biyu:gyara na jama'a,duk wanda ya kalli yadda mutanen mu suke zai samu tabbacin cewa suma suna buƙatar gyara,kai da ke son samarda gyara dole kana buƙatar waɗanda za su taimaka maka, kaga dole ne suma ya zamanto sun gyaru kuma suna da tunanin gyara,idan ba haka ba toh wahala ce kawai za ka sha.
Mataki na ukku:gyaran gwabnati,wannan shi ne mataki na ƙarshe kuma dole sai ansamar da matakan farko sannan azo ta kansa,ni ina ganin duk wanda ke son ya samar da gyara a irin wannan yanayin toh kodai aikin banza ne zaiyi ko kuma ba zai samarda gyaran da ake so ba.
Kamar yadda ya gabata munyi bayanin dokokin da da su ne duniya take gudana wanda yake riƙo da su shi zai kai mu zuwa ga matakan gyara yana da kyau ace musan yadda zamu samar da su.doka ta farko tana nufin ilimin boko doka ta biyu kuma tana nufin ilimin addini, domin samar da su wajibi ne asamar da wani tsari wanda zai taimaka wajen samar da su da kuma inganta su.
Misali da za ace zaka kashe 30 million naira don neman kaci zaɓe toh matsayin ka na mai son samar da gyara na haƙiƙa toh bai kamata kayi haka ba, ya zakayi kasamu yara masu shekara biyar biyar kaɗauki wani adadi ka ɗau nauyin karatun su boko da Arabi idan kaba su wasu shekaru zaka samar da al'umma wadda take tana iya samar da wani gyara a cikin Al'umma.waɗancan ruɓaɓɓin suna wucewa waɗanan
suna ƙara ƙarfin da za su iya samar da wani juyin-juya halin da zai zamo gyara ga wannan ƙasar mai albarka abin ƙauna da ƙasashen musulmi baki ɗaya.
MADOGARA WAJAN SAMARDA CANJI.✍️
Abinda wanda ke son samar da canji zaiyi riƙo da shi shi ne littafin Allah da sunnar annabin Rahma mai tsira da Amincin Allah,babu wani littafi da ke jagora zuwa ga samar da gyara kamar Alkur'ani,bari inbaka misali,acikin suratul-isra'i Allah ya gaya muna cewa banu-Isra'ila za suyi ɓarna amma acikin surar sai yagaya muna za a samu wasu waɗanda za su zo su kawo canji to acikin surar Allah ya ambaci sunan Alkur'ani sau goma shaɗaya don ya nuna muna cewa idan muna son samar da canji dole ne sai munyi riƙo da Alkur'ani.
SIFOFIN MASU SAMARDA CANJI.✍️
acikin suratul-isra'i Allah ya siffanta muna bayinsa da za su samarda canji sai ya kira su da "عبادنا"wato bayin mu saboda haka bayin Allah nagari sune waɗanda za su iya kawo muna canji ga yanayin da muke acikin sa.
Sai munkawo rubutu na gaba.
Allah muke roƙo da ya kawo muna gyara a cikin wannan ƙasar da ƙasashen musulmi baki ɗaya Allah ya azurta mu da shugabanni na gari masu adalci kuma masu tausayin mu.
مبارك عمر بلا✍️👏
06/04/2026.