27/05/2025
A yau Litinin, 26 ga Mayu, 2025, Uwar Gidan Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Uba Sani, tare da tawagarta sun kai ziyara karamar hukumar Kubau domin kaddamar da shirin bada tallafi mai taken “A KORI TALAUCI” ga mata a yankin.
An shirya bayar da tallafin ne a matakin farko ga mata 200, inda kowacce mace za ta amfana da naira dubu 100. Sai dai, ganin yawan matan da s**a halarta da kuma jajircewarta na tallafa wa mata domin su dogaro da kansu, Hajiya Hafsat Uba Sani ta kara yawan wadanda za su amfana zuwa 300.
A yanzu haka, adadin matan da s**a amfana da wannan tallafi a karamar hukumar Kubau ya kai 300, kuma kowacce daga cikinsu ta karɓi naira dubu 100, wanda jimillar kudin ya kai naira miliyan talatin (₦30,000,000).
Uwar gidan gwamna ta tabbatar wa matan cewa, gwamnatin Malam Uba Sani za ta ci gaba da tallafa musu domin karfafa gwiwar su wajen dogaro da kai, lamarin da ya kasance daya daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa.
A cikin jawabansu daban-daban, Akawun jihar Kaduna, Hon. Bashir Suleiman Zuntu, da Shugaban Karamar Hukumar Kubau, Hon. Musa Sale Banki, sun bayyana farin cikinsu da godiya ga Uwar Gidan gwamna bisa wannan gagarumin tallafi da ta bai wa matan Kubau. Sun kuma tabbatar mata da cewa, matan za su yi amfani da tallafin yadda ya kamata. Haka kuma, sun tabbatar da ci gaba da samun goyon bayan al’ummar karamar hukumar Kubau ga jam’iyyar APC daga sama har kasa a karkashin jagorancin Gwamna Malam Uba Sani (Damo Sarkin Hakuri).
A nasu bangaren, matan da s**a amfana da tallafin sun bayyana matukar godiyarsu ga Hajiya Hafsat Uba Sani, tare da alkawarin amfani da tallafin yadda ya dace. Haka kuma sun sake jaddada cewa karamar hukumar Kubau ta jam’iyyar APC ce a jiya, yau, da gobe In Sha Allah.
Taron ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar Kaduna da karamar hukumar Kubau, wanda s**a hada da: Mataimakin Shugaban karamar hukumar, Sakataren mulki na karamar hukumar, kansiloli da Sarakuna iyayen Kasa.
A ƙarshe, matan karamar hukumar Kubau sun tabbatar wa Uwar Gidan Mai girma gwamna da cewa:
Uba Sani Sau Biyu Ne ✌️
Jam’iyyar APC Daga Sama Har Kasa✌️
APC Uwa Daya, Uba Daya✍️
Daga kubau
Prince Prince 👑