03/03/2022
FIKIRAR HARKA TANA SAMUN CI GABA:
To har walayau kuma, abin da ainihin aka kafu a kai aka ginu akai, don ita fikira tana samun cigaba, daga loƙaci zuwa loƙaci. Mukan ta ƙoƙarin mu bayyanawa mutune, cigaba a fikira ba canzawar fikira ba ne, akwai banbamcin tsakinin sauyi, wato canzawa gaba ɗaya, da kuma cigaba, to wasu in s**a ga an samu cigaba s**an ce an canza ne.
To waɗannan irin kalmomin muna ƙoƙarin mutane su fahimci banbanci tsakanin canji, wato abin nufi da canji, mutum a ce ai ya canza, ma'ana ya tashi daga abin da ya ginu akai a da, ya koma wani abu daban. Don wasu suna kallon mu akai, suna ma zargin mu da cewa; an canza, wato ma'ana an canza daga abin da aka taso akai. Wato kamar an canza manufa ko ma alƙibla kenan, daga inda ake nufi, sai aka zo aka sauya, aka ce ana kaza.
“ Alal misali, 'yan zuhudu su sun ga da can ana rayuwar Taƙashshur da gujewa duniya da sauransu, amma kuma yanzu sai s**a ga ana shan shagali ( a ganin su fa)? Ba wai shagalin ake sha ba. Sai s**a ga an fara jin daɗi, har ma ka ga mutum ma ainihin yana girki da Gas, saboda tsananin shan shagali da jin daɗi.
“ Ko kuma ka gan shi har yana hawa mota, kuma ka ga gidansa ma har akwai shimfiɗa, shimfiɗar ma ta ledar Roba. S**a ce ah! Ai an canza, an saka leda a gida! Kuma ana girki da Gas! Sannan kuma ana hawa mota Bitil! Kuma har akan yi abinci ma har da Ƙwai a cikin abincin! To shi kenan, sai s**a ce ai an sauya, an saki hanya. To wanda s**a san abin da nake faɗi yanzu, sun san abin da nake faɗa, don sun san wasu sun yi irin waɗannan abubuwa ɗin, sai s**a tafi, s**a ce Zuhudu kawai!
Wasu kuma ana nan, ana nan s**a zo, s**a ce an canza, da can Ahlus-sunnah ake yi, yanzu kuma an ko ma ana shi'a! Da can an ginu ne akan sunnah Malikiyya, sai kuma yanzu aka zo, ana cewa shi'a “ Ja'afariyya, saboda haka an canza daga abin da ake akai. Sai s**a tafi abin su. 'Yan Zuhudu s**a tafi, 'yan Tawayiya s**a tafi.
Cikin Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a wani audio da yi acikin garin Zaria loƙacin ana fosanta.
__@ faruq Sani Kudan ( Abban Jeedah)