Fudiyya Kudan

Fudiyya Kudan Wannan shine official page na Da'irar Kudan ƙarƙashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

SHIRYE-SHIRYEN TATTAKIN BANA: AN GABATAR DA ZAMA NA MUSAMMAN A GARIN DABAI.Daga Muhammad Muneer AbdullahiZaman da aka ga...
29/07/2026

SHIRYE-SHIRYEN TATTAKIN BANA: AN GABATAR DA ZAMA NA MUSAMMAN A GARIN DABAI.

Daga Muhammad Muneer Abdullahi

Zaman da aka gabatar da shi da yammacin Talata, 28 ga watan Yulin shekarar 2026, ya samu halartar ’yan’uwa da wakilan ɓangarorin Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sayyid Zakzaky (H) daga da’iroin da s**a haɗa da Kudan, Dabai, Ɗanja, Hunƙuyi, Kokami, Kahutu, Gozaki, Dutsen-Kura, Ɗanmaigauta da Unguwar Allura.

A yayin zaman, kowane ɓangare ya gabatar da rahotonsa kan yadda suke da buƙatar ’yan’uwa masu tattaki su kasance domin sauƙaƙa musu ayyukansu.

Sannan an gabatar da rahoton yadda tattakin shekarar da ta gabata ya kasance, da irin ƙalubalen da aka fuskanta domin kauce musu.

Sashen kiwon lafiya ya buƙaci masu tattakin su guji zuwa da ƙananan yaran da ba za su iya taka da ƙafafunsu ba, sannan mata masu ƙaramin ciki da waɗanda cikinsu ya kusa isa haihuwa.

An buƙaci masu tattakin su kasance cikin tsari da yanayi na juyayi.

- Ya kamata ɗan’uwa ya sani cewa Tattakin Arba’in ibada ce babba.

- An shawarci masu hannu da shuni su himmatu wajen ciyar da masu wannan ibada.

Haka zalika, masu larura ta musamman su yi haƙuri su sadaukar da guzurinsu ga wasu domin musharaka a ladan.

©️ Zaria Media Forum
14/02/1448
29/07/2026

26/07/2026

Ku kalli Bidiyo sa'ilin da Sheikh Zakzaky ke fitowa daga gidansu (gidan mahaifin sa) dake kwarbai cikin birnin Zariya.

Yau Lahadi 26 July 2026.
Aqil Abdulkadir.

Alhamdulillah Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Zakzaky (H) a Birnin Zazzau Bayan Shekaru 12
26/07/2026

Alhamdulillah

Jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Zakzaky (H) a Birnin Zazzau Bayan Shekaru 12

JAGORA (H) YA ZIYARCI GIDAJEN 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI A ZARIA Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Cikin je...
26/07/2026

JAGORA (H) YA ZIYARCI GIDAJEN 'YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI A ZARIA

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Cikin jerin ziyarori da ya gudanar a birnin Zazzau a yau Lahadi 11 ga Safar 1448 (26/7/2026), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya je Ta'aziyyar Marigayi Malam Ƙasim, Limamin Zazzau, da ke Unguwar Juma.

A yayin ziyarar Jagora ya yi addu’ar Allah Ya jiqansa da rahama, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, tare da addu'ar rahama ga dukkan Muminai da s**a riga mu gidan gaskiya.

Bayan nan Jagora (H) ya ziyarci unguwanni da su ka haɗa da Unguwar Ƙwarbai, inda ya ziyarci ƙabarin Malam Musa, marikin tutar Shehu Danfodiyo zuwa Zazzau.

Daga nan Jagora ya ziyarci gidan Madaki Sa'idu da ke Unguwar Magajiya, da gidan Goggo Hari shima a unguwar Magajiya, da gidan Baba Abdulqadir (Babban yayan su) da ke Ƙwarbai 2. Sannan Jagora ya kai ziyara gidan Mama, Hajiya Hari Jamo (RH) a unguwar Jushi, duk a cikin garin Zaria.







11/safar/1448
26/07/2027

TARON TUNAWA DA SHAHIDAN QUDS 2014 KARO NA 12 A ZARIA Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Jagora Shaikh Ibrah...
25/07/2026

TARON TUNAWA DA SHAHIDAN QUDS 2014 KARO NA 12 A ZARIA

Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabi a taron tunawa da waƙi'ar Ƙudus ta 25 ga watan Yulin 2014. Taron ya gudana ne a yau Asabar 25/7/2026 a muhallin Darur Rahma da ke Dambo, a Zariya.

Jagoran ya fara jawabinsa da nuna alhini dangane da waƙi'ar Ashura da kuma wafatin Imam Hassan Mujtaba (A.S). Sannan ya tunatar dangane da arba'in da ake fuskanta, da kuma jana'izar shahidin wannan al'umma, Shahid Sayyid Ali Khamene'i (RH).

Jagora ya jaddada cewa: "wannan taron, taro ne na tunawa da waƙi'ar da ta auku a ranar 28 ga watan Ramadan, 1436 daidai da 25 ga watan Yulin 2014. Shekaru 12 ke nan cif-cif a ƙidayar miladiyya."

Har wa yau, Jagora (H) ya tunatar da yadda aka soma muzaharar Ƙudus a Nijeriya, wadda aka fara gudanar da ita a Juma'ar farko bayan watan Ramadan a Zariya. Daga bisani kuma ta faɗaɗa zuwa sassan ƙasar nan sakamakon ƙaruwa da yawan jama'ar da ke halarta. Haka kuma ya yi bayanin yadda al'amarin Falasɗinu ya samu karɓuwa a tsakanin al'umma.

"Muzaharar Ƙudus na duniya nuna goyon baya ne ga al'ummar Falasɗinu wanda ƴan share wuri zauna ke musgunawa da zaluntar su tsawon shekaru fiye da 70", inji Jagora.

Ya ƙara da cewa: "Ana nuna cewa, ba a yadda da zalunci ba ne."

Har wa yau, a wani ɓangare na jawabinsa, Jagora ya tunatar da al'umma dangane da waƙi'ar da ta auku a rana irin ta yau. Ya ce, muzaharar Ƙudus ta wannan shekarar (2014), a nan ƙasar ne kawai aka auka mata. Ya ce: "wannan abin da ya faru bai ɓoyun ma al'umma ba. Ashe ba su dandara ba bayan shekara guda s**a sake diran mana da nufin share kowa da kowa. Da ma manufar ke nan a waƙi'ar 25 ga watan Yulin 2014 sai ya ƙare kan mutum 34", ya nusasshe.

Dangane da masu afkawa muzaharar Ƙudus domin faranta ran Isra'iliyawa, Jagora (H) ya ce, abu ne mai sauƙi: "tunda mu muna nuna goyon baya ga Falasɗinawa a Juma'ar ƙarshen watan Ramadan, sai ku ware watarana ba Juma'ar ƙarshen watan Ramadan ba sai ku goyi bayan Isra'iliyawa".

Jagora (H) ya jaddada cewa, ba za a ba mu tsoro da mutuwa ba: "ko ku yi harbi, ko kar ku yi harbi, za mu fito". Sannan ya ce, irin wannan taro, taro ne da ake tuna rayayyu da nassin Alƙur'ani. Ya ƙara da cewa: "idan aka ce an ga shahidi da ido, ba ma shakka", ya lurantar.

Jagora (H) ya ce, ko an kashe mutum ko kuma aka bar shi da rai, a ƙarshe dai zai mutu. Ya ce: "Abin alfahari ne a kashe ka a tafarkin Allah". Jagora ya nanata cewa, muna nan daram a wannan tafarki da aka kashe waɗannan shahidai. Ya ce: "muna nan daram a wannan tafarki da kuka bayar da rai a kai, ko a karrama mu, ko mu mutu a kan wannan tafarki, amma ba za mu sauya ba".

Dangane da masu kisan kai kuwa, Jagora (H) ya ce, su tuba, amma idan ba su tuba ba, za su yi hasarar duniya da lahira.

A ƙarshe, Jagora ya jaddada cewa: "wannan taro namu alama ce ta so, muna son waɗanda s**a sadaukar da rayuwarsu a wannan tafarki. Kuma kowannen mu hanƙoransa ke nan. Muna tunawa da wannan, muna ganin muna samun lada ne".

Bayan kammala jawabin, Jagora (H) ya gaisa da malamai, fastoci da sauran baƙin da aka gayyata zuwa taron, tare da iyalan Shahidai. Daga nan sai ya gudanar da ziyarar ƙaburburan Shahidan da ke kwance a Darur Rahma, sannan aka sallami al'umma.

Tun da farko, an fara taron da buɗe shi da addu'a, sannan aka yi karatun Alƙur'ani Mai Girma. Bayan haka aka gabatar da display daga lajanoni, tare da Faretin girmama Shuhada, sai kuma tamsiliyya da ta shafi waƙi'ar. Bayan kammala ziyarorin, Jagora (H) ya rufe taron da addu'a.







11/safar/1448
25th/07/2026

Waki'ar Quds 25/07/2014Wasu hotunan karbar gaisuwar ta'aziyyar Shahidan Quds na ranar 25/7/2014 a gidan Shaikh Ibraheem ...
25/07/2026

Waki'ar Quds 25/07/2014

Wasu hotunan karbar gaisuwar ta'aziyyar Shahidan Quds na ranar 25/7/2014 a gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky a kwanaki daban-daban.

SANARWA:بسم الله الرحمن الرحيم Ana gayyatar Al'umma halartar taron tunawa da Shahidan Qods na 2014, gobe Asabat 10/Safar...
24/07/2026

SANARWA:

بسم الله الرحمن الرحيم

Ana gayyatar Al'umma halartar taron tunawa da Shahidan Qods na 2014, gobe Asabat 10/Safar/1448 (25/07/2026), a Darur-Rahama da ke Dambo, Zariya.

Lokaci: 8am zuwa 12pm.

Mai Jawabi: Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H).







10/Safar/1448
24/07/2026

21/07/2026

Educational Excursion to Zaria Aviation College

A few days ago, the students of Madarasatul Fudiyya embarked on an educational excursion to Zaria Aviation College. The visit was organized to broaden the students' knowledge and expose them to the aviation industry.

During the excursion, the students toured various sections of the college, learned about aircraft operations, aviation safety, and the different career opportunities available in the aviation sector. They also had the opportunity to interact with aviation professionals and ask questions about their experiences.

The excursion was both educational and inspiring. It provided the students with practical knowledge that complemented their classroom learning and motivated many of them to dream of future careers in aviation.

Address

Kudan
812104

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fudiyya Kudan posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share