
30/03/2024
Zan taimakawa Tinubu domin samun Nasara a Gwamnatin sa ~Cewar Shugaba Buhari.
A jiya ranar Juma’ar da ta gabata ne tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya biyo bayan bayanan da ya yi a bainar jama’a ta Hanyar yin waya da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wayar tarho, inda shi da kan sa ya mika sakon taya murna ga shugaban a lokacin da ya cika shekaru 72 da haihuwa.
A yayin tattaunawar, tsohon shugaban kasar ya ce ya jajirce matuka wajen ganin an samu nasarar gwamnatin APC karkashin shugaba Tinubu.
Dangane da haka, shugaba Buhari ya yi addu’a da addu’o’in samun nasara ga Tinubu, inda ya ce yin addu’a ga shugaba ya zama wajibi domin nasararsa da lafiyarsa ta al’umma ce (kowa), ya kuma kara da cewa abubuwan da sabuwar gwamnati ta samu dole ne a kalli nasarorin da kasa ta samu.