23/12/2025
Ku daure ku karanta akwai darasi
TABBAS ALLAH YA ISA😭😭😭😭.
21-12-2020.
Safiyar jiya LAHADI Misalin karfe goma nasafe wani Mai mota yayi fatali da kayan tallan raken wani MATASHIN DATTIJO, maimakon Mai motar yabashi hakuri Sai yaci magani yaqi yace komai, dukkan yazube akwata Mai raken yazo gaban Mai motar yace ME YASA KAZUBAR MIN DA RAKE? MAI MOTAR ya kalleshi yace uban wa yace ka tare Hanya? Me rake yake Babu inda na tare hanya kaidai kawai ka zalinceni, kawai ka biyani Nan danan Mai motar ya haushi da zagi Yana cewa Anqi abiya din, Cikin hawaye Mai raken yace Bakasan Wahalar danasha nasami jarinba Amman ka zubArnin ka cuceni ka cutarda rayuwata, MAI MOTAR yaci gaba da zaginsa, MAI RAKE ya kalleshi yace DA KARFIN IKON ALLAH SAI UBANGIJI YA GAGGAUTA YIMUN SAKAYYA😭😭 ALLAH YA ISA!! ALLAH YA ISA!! ALLAH YA ISA!!! sau uku Yana fade, Babu yadda banyiba akan Mai MOTAR ya Dena zaginsa sannan ya biyashi hakkinsa, Amman Sai yahada har dani Yana zagi, munaji muna gani Mai motar yayi gaba abinsa bai biyashi komaiba yatafi,
MAI RAKE YACI GABA DA ZUBDA HAWAYE😭😭, Tausayinsa ya kamani Sai nazaro kudi na biya kudin raken duka sannan na qara Masa da wani Abu, Wallahi Sai Naga Yana kukan farin ciki akaro na biyu yanata yimun Addua,a, tareda cewar ubangiji ya ninka maka fiyeda abinda ka tallafamin, Nayi gaba na barshi yanata Addua,a.
BANfi minti uku ba daidai Tal,udu jaction naci karoda wata tsohuwar qawata da mukayi FCE KANO da ita, munfi minti goma muna Hirar yaushe gamo, da zamu rabu tace Bari in baka kudin Mai, wallahi Sai data ninkamin abinda na baiwa Mai rakennan sau goma Sha shida tareda wasu chanji, take Sai Adduar Mai rake ta fadomin dayace ubangiji ya ninka mafa fiyeda abinda ka bani, Azuciyata nace TABBAS ALLAH YA ISA!!!.
Bari kuji wani hukuncin Allah, ko minti uku banyiba, Sai Naga taron mutane akan t**i anata zuwa dubawa, nima banyi qasa A guiwaba Sai na leqa, Iko Sai Allah Mai motar da ya buge Mai rakene kwance Ana Yi Masa fifita gaban motar yatashi daga aiki, hannusa ya karye, Wai Ashe dukan wani bangon t**i yayi Shi kadai yayi accident.
Na sake kallonsa, ya shaidani na shaidashi nace sannu malam Allah ya kiyaye gaba, TABBAS ALLAH DA ISA YAKE.
nayi gaba abina inata tunanin kudirar UBANGIJi.
Yakamata muji tsoron Allah mu daina Raina kalmar ALLAH YA ISA!!
Wani mutumin daka Raina bakasan matsayinsa agurin Allah ba, sannan bakasan kowaneneba, kowanne mutum da irin baiwar da Allah yayi Masa, kowanne mutum yanada wata baiwa wacce Kai bakada ita.
Ubangiji ya tsaremu da sharr
✍️✍️✍️✍️
SAMI ROGO AIKAWA
YARON KIRKI