08/11/2025
Su wane ne ke fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Anambra?
Hotunan ƴan takarar gwamnan AnambraAsalin hoton,SOLUDO
Bayanan hoto,Hotunan ƴan takarar gwamnan Anambra
Sa'o'i 5 da s**a wuce
Ana gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.
A wannan zaɓen, mutum 16 ne gaba ɗaya ke neman kujerar gwamnan Anambra ciki har da gwamna mai ci, Chukwuma Soludo, wanda ke neman tazarce.
Dubban jami'an tsaro ne aka jibge a jihar domin zaɓen, yayin da manyan 'yan takara s**a rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, domin tabbatar da zaɓen cikin lumana da mutunta juna.
Ga wasu muhimman abubuwa da s**a kamata a sani game da 'yan takarar da ke fafatawa a zaɓen na gwamnan Anambra na 2025.
Charles Soludo ( Jam'iyya APGA)
Chukwuma SoludoAsalin hoton,CHUKWUMA SOLUDO
Chukwuma Charles Soludo shi ne gwamna na biyar da aka zaɓa ta tsarin dimokuraadiyya a jihar Anambra.
Yanzu haka yana neman wa'adi na biyu a karo na biyu kenan.
A lokacin zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APGA, Gwamna Soludo ne ya lashe zaɓen a lokacin domin babu wanda ya ƙalubalance shi.