
16/08/2024
YABA KYAUTA: Ga Waƙar Ga Rangadawa Ɗan Bello
Daga Abubakar Shehu Dokoki
•Jama'a mu gaida Dan Bello cikakken Jarumi.
•Ga 'yan Arewa yanzu ya zama tamkar malami.
•Wanda yake musu yaƙi babu wuƙa ko makami.
•Ya bankaɗo sirrin masu źàlunci wasu har ya sa su tagumi.
•Wayyoni Allah Duniya hàŕàm- a harami.
•Allah suna cutar mu kasa musu dogon źulumi.
•Shi kuma Dan Bello Allah Ka ba shi kariya Ka kare shi daga kowanne irin takunkumi.
•Ɗan Bello, Sadauki na gaske gwanin juriya!
•Masoyin Arewa da duk faɗin Nijeriya!
•Rashin irin.ku shi ya wargaza mana Nijeriya!
•Mun yi kuka mun zubar da hawaye da idaniya!
•Abin baƙin ciki kasarmu tana Hannun ƴan Sharholiya!
•Ba kowa gabansu sai son tarin dukiya!
•Sun barmu ba wuta, ba ilmi bare kiwon lafiya!
•Sun bautar da mu da yunwa mutane suna ta hajijiya!
•Mun yi da na sanin zaɓen su cikin su duk ba mai gaskiya!
•Kowa nace ciki har ehen...ɗik baki ɗaya!
•Allah Ka jiƙan su Tafawa da sauran Mazajen jiya!
•Mun yi kuka, rashin su har yau ba mu tsira ba.
Yaa Allah Ka ba shi kariya ba dan Halinmu ba.