22/07/2026
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!!!
كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ۗ وَإِنَّمَا تُوَفَّوْنَ أُجُورَكُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۖ فَمَن زُحْزِحَ عَنِ النَّارِ وَأُدْخِلَ الْجَنَّةَ فَقَدْ فَازَ ۗ وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلَّا مَتَاعُ الْغُرُورِ
Kullu nafsin dhā’iqatul-mawt. Wa innamā tuwaffawna ujūrakum yawmal-qiyāmah. Faman zuhziha ʿanin-nāri wa udkhilal-jannata faqad fāz. Wa mal-ḥayātud-dunyā illā matāʿul-ghurūr.
Fassarar Hausa:
Kowane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma za a cika muku sakamakon ayyukanku ne kawai a Ranar Alƙiyama. To, wanda aka nisantar da shi daga Wuta, aka shigar da shi Aljanna, to, haƙiƙa ya rabauta. Kuma rayuwar duniya ba komai ba ce face jin daɗin ruɗu.
Amadadin shugaban kungiyar Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa state, Alh. Hussaini Zakari Sa'ee, da mukarrabansa, tare da Kwamanda Agaji na Jihar Nasarawa Mukaddam Alh. Hassan Abdullahi (RTA) muna sanar da rasuwan mahaifin Kwamanda Karamar hukumar Lafia LGA, sannan mataimakin Sakatare na jihar Nasarawa, Sh*tu Rayyanu da safiyar yau.
Alh. Rayyanu Isah ya rasu ne a Specialist Hospital dake birnin Lafia, hedkwatar mulki na jihar Nasarawa bayan jinya da yayi fama dashi.
Kafin rasuwar Sa, ya rike mukamai masu yawa, wanda s**a hada da Sakataren Sarkin Lafia a masarauta Lafian bare-bari da Shugaban Jama'atul Nasrul Islam na karamar hukumar Lafia.
Za'ayi mishi sallah Janaza da misalin karfe goma na safe InshaAllah.
Allah ya jikansa ya gafarta mishi, iyali da ya bari Allah ya bamu hakurin jure wannan rashi, Amin.
Munazzamatul Fityanul Islam, Nasarawa State Media Directorate.
22/07/2026.