11/10/2024
Yanzu na kula babu abinda yake kokarin raba kan Yan Cryptocurrency kamar magana akan Pi Coin. Wannan fa ba wani abun ɗaga hankali bane ƴan'uwa. Idan ka yarda dashi kayi, idan baka yarda ba ka bari, simple.
Sannan Jama'a muyi wa kanmu adalci mafiya yawan waɗanda suke against Pi Network bafa sunce basa mining bane, sannan basu ce ka daina ba, Idan na fahimce su, suna ishara ne akan jama'a su daure su rage burin da s**a ɗaura akai.
Sannan abinda nake son na ɗan jawo hankalin mu akai shine, mafiya yawan wanda suke mining dan Allah su rage jifan wanda suke against Pi Network da kalmar hassada suke musu. 🤣 Wallahi abin dariya yake bani.
To be honest ka taɓa jin Nicholas ya fito yace ana yi masa hassada? Kasan me yasa bai taɓa ba? Saboda idan kana magana akan hassada ne, mahassadi a kullum shine a baya, kai da kake a gaba idan kana da abin yi bama zaka waigo ba. Idan dai kullum maganar ka akan hassada ne, to tabbas baka mallaki abinda za'a yi maka hassada ba.
Kamar ni na fara mining Pi tun kafin na fara Cryptocurrency, this is the truth, na fara Mining Pi tun around 2019. Amma gaskiya ban yarda da tsarin saba, da duk abinda ya kunsa sai a December da naga yadda s**a fitar da TEKONOMICS na Pi Coin.
Ko da Pi ko babu muna siyan data, ni abinda na ɗauka dame zai rage ni idan nayi mining ɗin? Kawai dai abinda na ɗauka da yayi kyau bana ciki, gwanda ta ɓaci ina ciki. 😊
Sanin kanmu ne Community abune mai matuƙar tasiri acikin Cryptocurrency, Community ɗin da Pi yake dashi ya isa yasa nayi mining ɗinsa a yanzu (Ina magana ne akaran kaina), sannan ban san mai Dev. na Pi s**a tana da, sun fini sani akai. Amma da Pi sun bada damar turawa da ƙarbar Pi ina ganin a yadda mutane suke son Pi da yanzu an fara musayar kuɗi dashi. Na tabbata ko anan Nigeria akwai wanda zasu karɓa su bada kuɗi ko wani abu makamancin wannan.
Ni dai ina girmama fahimtar kowa akan wannan mas'alar, abubuwa nawane muka basu yarda da aamanna amma a ƙarshe s**a bamu kunya (misali ga SafemoonCash idan baku