SANIN yakamata

SANIN yakamata Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from SANIN yakamata, Digital creator, Hausa, Lagos.

21/03/2025
16/09/2024
SOJOJI SUN BINDIGE WANI BATUREN YANSANDA A JIHAR ZAMFARAWannnan al'amari ya faru lokacin da sojojjin su Ka tsayar da wan...
29/08/2024

SOJOJI SUN BINDIGE WANI BATUREN YANSANDA A JIHAR ZAMFARA

Wannnan al'amari ya faru lokacin da sojojjin su Ka tsayar da wani baturen yansanda mai suna H Liman, a wani shingen bincike wato checkpoint na dan marke da ke cikin Karama Hukumar Bukkuyum a Jihar Zamfara, Amma maimakon ya tsaya nan take ya karawa motarsa wuta ya ki Tsayawa, ko da ya ke an gano matsayinsa ne bayan gaza cimma mummunar manufarsa

Ganin matakin da ya dauka nan take sojojin s**a yiwa wasu askarawa waya da ke gaban su a kan t**i, su rufe Hanya ga mota nan zuwa mai iri kaza, ga sunan tafe su ma, lamarin da bayan askarawan sun tsare shi ba hanyar ficewa ya kuma hangi sojojjin da ya tserewa, nan take ya fice daga cikin motar ya ranta da gudu lamarin da sojojjin su ka bude masa wuta.

Bayan gudanar da bincike a cikin motarsa an ga wasu bindigu guda biyu Kira Ak47 Ya shiga da su Jihar Zamfara, alhali kuma a Jihar Kebbi Ya ke aiki.

Credit Muhammad B Lawan Zamfara

29/08/2024

ALBISHIRINKA MAI YIN SALLAR WALLAHA

*ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ*

Sallar Wallaha sallace ta nafila da ake yinta idan rana ta fito ta dan daga kadan,Hukuncinta Sunnah ce mai karfi daga cikin Sunnonin Manzon Allah SAW,kuma ana daina sallar Wallaha gab da zawalin rana daga tsakiya kuma anfi son yinta idan rana tayi zafi sosai lokacin da mutane s**a shagaltu da aiyukan duniya,mafi karancinta raka'a biyu ce mafi yawancinta baya da iyaka, amma Manzon Allah SAW yayi raka'a takwas amma mafi kyakkyawan abin koyi shine Manzon Allah SAW.

1-ALBISHIR NA FARKO
*Babu mai kiyaye sallar Wallahi sai bayin Allah masu komawa zuwa ga Allah acikin al'amuransu*

Daga Abi Hurairataﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ, daga Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yana cewa:
*(Babu mai kiyaye yin sallar Wallaha sai masu komawa zuwa ga Allah, domin salla ce ta bayin Allah masu komawa zuwa ga Allah)*
@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ

2-ALBISHIR NA BIYU
*Yin sallar Wallaha raka'a biyu a Masallaci yana daidai da ladar aikin Umara cikakkiya*

Yin sallar wallaha a Masallacin ba tare da dauwama akan hakan ba, yinta lokacin zuwa wani lokacin sunnah ne kuma babu laifi,amma dauwama kullum yinta a Masallaci yau da gobe ya sabawa sunnah, Allah ne Mafi sani.

Daga Abi Umamata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ daga Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ yace:
*(Wanda ya fita daga gidansa, yana da alwala zuwa ga sallar farillah, ladar kamar ladar aikin hajji ne mai alfarma,amma wanda ya fita don sallar nafilar wallaha a Masallaci ba abinda ya fitar da shi sai dan ya sallaci sallar wallaha, ladarsa kamar ladar aikin Umara ne,.......)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﺑﻮﺩﺍﻭﺩ ﻓﻲ ﺳﻨﻨﻪ ‏( 558 ‏) ، ﻭﺣﺴﻨﻪ ﺍﻻﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻏﻴﺐ ﻭﺍﻟﺘﺮﻫﻴﺐ ‏( 320 ‏)

3-ALBISHIR NA UKU
*Sallar wallaha hanya ce ta samun kariya ta Allah ta musamman tun daga farkon yini har zuwa karshen yini*

Daga Abid Dardaa'i da Abi Zarri ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﻤﺎ daga Manzon Allah ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ yace:
*(Allah mai girma da Buwaya yace:YA KAI DAN ADAM,KAYI MIN RAKA'A GUDA HUDU A FARKON YINI ZAN ISAR MAKA

28/08/2024

ZUWA GA MASU FAMA DA SHA'AWA,
Samari da yan mata zawarawa hadda matan Aure 👌

Ya Allah kabawa wanda ya samu halin karanta
wannan rubutu ikon yin sharing zuwa ga sauran groups.

Samari da yan' mata suna yawan turawa malamai tambayoyi iri daban daban akan yadda suke fama da tsananin sha'awa.

Wasu daga ciki s**an ce suna istimna'i wato wasa da al'aura wai don su gujewa aikata zina, bayan zinar suke aikatawa.

Istimna'i (wasa da al’aura) ya haramtu ta kowace irin siga kuma yinsa zai jawo azaba da ukuba ranar alkiyama matukar dai mai aikatawa bai tuba ba ya daina.

Fitar da maniyyi ta kowace irin siga haramun ne saidai ta hanyar aure kawai.

Akwai Bala'o'i masu tarin yawa dangane ta masu wasa da al'aura.

Idan ka" kasance ko kin kasan ce kina fama da matsananciyar sha'awa kuma babu halin yin aure to akwai hanyoyi masu tarin yawa da zaku bi don gujewa fadawa tarkon shaidan.

Ga wasu daga cikin jerin su.

• Ku guji zama a daki ku kadai, ba tare da mutun yana wani aikin dazai ja hankalin sa ba.

• Ku guji yawan sanya sha'awar jima'i acikin ran ku.

• Kuyi iya qoqarin daza kuy wajen kawar da kai daga shafukan da suke yada hotuna masu nuna tsiraici.

• Yawan yin azumin nafila yana mutuqar taimakawa wajen nesanta mutun daga wannan dabi'a.

• Kadena yiwa kowace irin mace kallon sha'awa, haka kema kidena yiwa kowane irin namiji kallon sha'awa.

Mutun zai iya rayuwa cikin qoshin lafiya batare da yana fitar da maniyyi ba har zuwa sanda zaiyi aure, muddin dai mutun yana tunawa da azabobi da Allah ya tanada ga wadan da s**a kasa riqe sha'awar su.

Sha'awa irin ta samari da yan mata daga shaidan take, domin tana daya daga cikin manyan tarkunan sa da yake halakar da mutane dasu.

Amma dukkani wanda ya ji tsaoran tsayuwa da ubangijinsa ya hana zuciyarsa abin da take so daga sha’awa da istimna’i lallai aljanna ita ce makomarsa matsuguninsa da izinin Allah madaukaki

Rubutawa batayi mana wahala ba muna fatan sharing zuwa groups bazai yimuku wahala ba👏

Sabbin bayanai dake zagayawa a kafafen yaɗa labarai masu nagarta dangane da yunƙurin  Gwamnatin tarayya na cigaba da biy...
20/08/2024

Sabbin bayanai dake zagayawa a kafafen yaɗa labarai masu nagarta dangane da yunƙurin Gwamnatin tarayya na cigaba da biyan tallafin mai cikin sirri, wani sabon shafi ne da ke sake fito da nuƙu-nuƙu da rashin aminci dake gudana ƙarƙashin mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Wannan na cin karo da matsayar shugaban ƙasar a jawabin da ya yiwa ‘yan ƙasa, bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata, inda ya kafe akan cewa ba zai dawo da biyan tallafin ba.

Tun kafin wannan jawabi nasa, akwai bayanai dake cewa tuni aka cigaba da biyan wannan tallafi ta hanyar da bata dace ba. Kuma abun takai ci al’umar ƙasa na shan fetur da tsada.

Bambanci da ake samu tsakanin abinda shugaban ke fada da kuma abubuwan da yake aikatawa na nuna irin gurɓataccen shugabancin dake gudana a ƙar ƙashin sa.

A lokacin da ‘yan ƙasa ke fama da tsadar rayuwa da kuma ƙarancin man fetur, jan ƙafar da gwamnatin ke cigaba da yi wajen buɗe matatar mai ta Patakwal abun kunya ne ga ƙasar nan, wanda kuma ya rataya akan Tinubu kai tsaye a matsayin sa na minitan harkokin mai na Najeriya.

Har ila yau, musun da kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) ke yi na ƙara ta'azzara wahalhalun da ‘yan kasa ke sha ta fuskar ƙarancin man fetur da tsadar sa.

Yayinda ake gwabza muhawara tsakanin yan kasuwa na cikin gida dake goyon bayan matatun mai na ƙasa, da kuma wanɗanda ke goyon bayan cigaba da shigo da man daga kasashen waje, shirun da shugaban kasar ya yi akan wannan batu abun damuwa ne sosai.

Yana da kyau ace shugaba Tinubu, wanda ke da alhakin warware ire-iren waɗan nan matsaloli domin kare martabar ƙasa, ya fito ya samar da mafita kamar yadda ake tsammani.

Ɓoye ɓoyen da kamfanin mai na ƙasa ke yi akan taƙamaiman halin da ake ciki tare da rahotannin karkatar da maƙuden kudaden da aka ware su domin gudanar da wasu muhimman ayyuka zuwa biyan tallafin mai na cigaba da dagula al'amura.

Idan waɗannan rahotanni s**a kasance gaskiya, ba shakka federaliyyar kasar nan na cikin mawuyacin hali. Saboda haka, yana da matukar muhimmanc

18/08/2024

Ko Kasn Tsawon Lokacin Da Yakamata Ka Dauka Kana Jima'i Da Matarka?

🔞+ ONLY:

Wani abu da yawanmu maza bamu gane ba shi ne yawan lokacin da ya kamata kayi akan matarka a yayi gudanar da jim'i da ita.

Duk da yake babu wani bincike daya tabbatar da hakikanin tsawon lokacin da magidanci zai tsawita akan matarsa ma'ana yana jima'i da ita, sai dai kuma binciken ya tabbatar da cewa mafi karancin lokacin da namiji zaiyi yana jima'i shi ne daga mintuna 3 zuwa 7, duk bamijin da ya kasa daukar wannan lokacin yana saduwa da matarsa to tabbas yanada matsalar daya kamata yaga likita.

Haka zalika mintuna 7 zuwa 13 sune yawan tsawon da idan namiji yayi a lokacin saduwa bai takurawa matarsaba shi ma baj jigata kansa ba, kamar yadda bincike ya nuna. Kamar yadda nazarin ya kara tabbatar da cewa mintuna 10 zuwa 30 akan mace ana jima'i da ita lokuta ne da s**a wuce hankali ga maza masu irin wannan jimawan akan matansu. Sai dai wadannan tsawon lokatan basu hada da lokutan wasannin motsa sha'awa ba, ana lissafin lokutan ne daga lokacin da shi maigida ya shigar da azzakarin mashigar.

Babban abunda ya kamata maza magidanta su kuma fahimta anan shine, ba wai ana nufin cewa dole ne sai maza sun dauki tsawon wadannan lokutan akan matansu ba, ko kuma su takaita kamar yadda kamar yadda binciken ya nuna ba, abun da ya kamata maza su fahinta shine ana bukatar kowani magidanci ya iya fahimtar tsawon lokacin da matarsa take iya samu gamsuwa a jima'ince.

Akwai wasu matan a cikin mintuna biyu kacal sun biya bukata, akwai matan da a lokutan wasannin motsa sha'awa ma sun kawo, kamar yadda ake samun wasu matan muddin ba an dauki sama da sa'a guda ko rabin sa'a ana gurzarsu ba basusan ma anayi ba.

Don haka ne masana suke bada shawaran cewa, ko wani magidanci dole ne ya fahimci matarsa sosai a jima'ince ta haka ne kawai zai iya gamsar da ita na babu cuta babu cutarwa. Ganin shi gamsar da mace a yayin jima'i dole ne akan dukkannin wani magidanci

Ga mazan da suke yin shaye shaye kamin suyi jima'i su

17/08/2024

Wasu Kurakuren Da 'Yan Mata Suke Yi Idan Saurayin Da Suke So Ya Gujesu:

Wasu matan s**an yi wasu kurakure a kokarisu na shawo kan samarinsu alokacin da s**a gujesu haka nan kawai ba tare da wani laifi ba.

Muddin har namiji ya yanke shawran rabuwa dake, kada ki sake kiyi wadannan abuuwan domin dawo da soyayyarki:

1:Kuka:
Kada ki sake kiyiwa saurayin daya gujeki ba tare da wani dalili ba kukan rabuwa dake. Koda zakiyi kukan saboda bacin rai kada ki bari wani yaji ko ya gani.

2: Bin Abokansa:
Kada ki sake kice zaka bi abokansa domin su masa magana ya dawo. Idan ma kina yawan gaisawa da abokanensa a wannan lokacin ki daina saboda kada ma wani cikinsu yace zai miki zancensa.

3: Bibiyansa A Shafukansa:
Kada ki sake ki rika bibiyansa a shafukansa na sada zumunta. Ki tabbatar da ki doɗe shi yadda bazaki riƙa ganin abubuwan da yake yi ba.

4: Ci Gaba Da Tunaninsa:
Tabbas cireshi a rai a lokacin g isuda zai yi wuya. Amma hakan shine zai kare miki mutuncinki.
Ki tabbatar kin kauda duk wani abunda zai saki tunawa da shi a wayarki, a dakinki, a wajen aikinki ko a inda k**e kasuwancinki.

5: Kin Baiwa Wasu Mazan Dama:
Wasu matan da zaran sun samu matsala da masoyinsu sai su yiwa maza kudin goro su daina kula maza da sunan duka haka suke, Wannan kuskure ne.

Kada kiyi saurin fadawa soyayya,kada kuma ki Hana wasu mazan damar sonki.

A duk lokacinda kika matsawa namijin da haka kawai yayi shawaran rabuwa dake dole ya dawo kuci gaba da soyayya da sunan kina sonshi. Zaki fiskanci matsalolin da s**a fi na farko daga gareshi. Domin yanzu zai dauka idan babu shi bazaki iya rayuwa ba. Sannan mutuncinki zai zube a wajensa zai rika miki abunda ya gadama. A irin wannan lokacin ne zai bukaci yin zina dake saboda yasan bazaki ki ba.

Duk namijin da ya rabu dake kikayi banza da shi. Shine zai shiga damuwa musamman idan baki yi sake kin bashi gabanki ba. Koda kin bayar kada ki taba yada mutunciki.

SHARE 🌿

YAYIN DA JANAR BABANGIDA YA CIKA SHEKARU 83 A YAUYadda Rashin Bibiyar Tarihi Ya Sa Ake Zaginsa, Bayan Ya Fi Kowane Shuga...
17/08/2024

YAYIN DA JANAR BABANGIDA YA CIKA SHEKARU 83 A YAU

Yadda Rashin Bibiyar Tarihi Ya Sa Ake Zaginsa, Bayan Ya Fi Kowane Shugaban Kasa Aiki A Nijeriya
.. ga wasu daga cikin ayyuka dubu na IBB a kasar nan

Shugaba Babangida Ne Aka Taba Samu Ya Aikata Ayyukan Alheri Masu Amfani Har Guda 1,000 A Zamanin Mulkinsa Na Shekaru Takwas, Inda Bayan Shugaba Babangidan, Babu Koda Wani Shugaba Guda A Duk Tarihin Nahiyar Afirka, Da Kuma Tarihin Kafatanin Shugabannin Da S**a Taba Ko Kuwa Suke Kan Kujerar Shugabancin 'Kasashensu A Halin Yanzu, Wanda Ya Kwatanta Haka, Idan Banda KBE da Sir Ahmadu Bello Sardauna Ya Gina Kuma Ya Samar Da Ayyukan Alheri Guda Dari, A Fadin Yankin Arewa; Ahmadu Bello University Zaria, Daya Kenan Na Sardaunan, Sai Kuma Wasu Guda 99 Da Yawancinsu Gwamnonin Arewa Goma Sha Tara Sun Yi Watsi Da Su, Inda Haka Ya Sa S**a 'Bal'balce, Yayin Da S**a Siyar Da Wasu; Irinsu Bank Of The North!

Ga Jerin wasu Ayyukan Alher Na IBB:-

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ne Ya Gina Villa Abuja kuma ya soma tarewa a cikinta, Shi Ne Ya Samar Da Gine-Ginen: Eagle Square, Federal Secretariat, FCDA Secretariat, National Mosque, National Church, National Assembly, Supreme Court, Court of Appeal, Barrack Guda Goma A Abuja, Wuse Market, NNPC Tower.

Shugaba Babangida Ne Ya Samar Da Irin Su:- NAFDAC, DIFRRI, MAMSER (NOA), CCT, CCB, CCN, Gifted Children's School, Suleja, NHIS, NEXIM, NDIC, NDLEA, FRSC, ECOMOG, Ministry of Women Affairs, NWC, National Mathematical Center, NDE, Ministry of Agriculture & Rural Development, NAFSESS, NSFCP, FUMTP, NPB, FEPA, NALDA, CDS, RMRC, CMEWS, NEPC, FMIDS, Petro-Chemical Plant, Kaduna, Petro-Chemical Plant, Eleme, Osaka Dam, Ajaokuta, Shiroro Hydro Power Station, Niger, Dukkanin Sakatariyoyin Gwamnatocin Jihohin Najeriya, Da Kuma Kafatanin Sakatariyoyin Da Yanzu Haka Ake Amfani Da Su A Kowace karamar hukuma, Delta IX Gas Turbine Plant, Bai Taba Siyo Tataccen Man Fetur Daga Wata Kasar Waje Ba, Duk Man Fetur Din Da Aka Sha Zamanin Mulkinsa, A matatun

Ga Jerin wasu Ayyukan Alher Na IBB:-

Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida Ne Ya Gina Villa Abuja kuma ya soma tarewa a cikinta, Shi Ne Ya Samar Da Gine-Ginen: Eagle Square, Federal Secretariat, FCDA Secretariat, National Mosque, National Church, National Assembly, Supreme Court, Court of Appeal, Barrack Guda Goma A Abuja, Wuse Market, NNPC Tower.

Shugaba Babangida Ne Ya Samar Da Irin Su:- NAFDAC, DIFRRI, MAMSER (NOA), CCT, CCB, CCN, Gifted Children's School, Suleja, NHIS, NEXIM, NDIC, NDLEA, FRSC, ECOMOG, Ministry of Women Affairs, NWC, National Mathematical Center, NDE, Ministry of Agriculture & Rural Development, NAFSESS, NSFCP, FUMTP, NPB, FEPA, NALDA, CDS, RMRC, CMEWS, NEPC, FMIDS, Petro-Chemical Plant, Kaduna, Petro-Chemical Plant, Eleme, Osaka Dam, Ajaokuta, Shiroro Hydro Power Station, Niger, Dukkanin Sakatariyoyin Gwamnatocin Jihohin Najeriya, Da Kuma Kafatanin Sakatariyoyin Da Yanzu Haka Ake Amfani Da Su A Kowace karamar hukuma, Delta IX Gas Turbine Plant, Bai Taba Siyo Tataccen Man Fetur Daga Wata Kasar Waje Ba, Duk Man Fetur Din Da Aka Sha Zamanin Mulkinsa, A matatun man da Nijeriya Ke Da Su Aka Tace Shi, Duk matatun man Nijeriya Suna Aiki 100% A Sanda Ya Sauka Daga Karagar Mulki.

Shugaba Babangida Ne Ya Kirkiro Jihohi Goma Sha Uku, A Duk Fadin Nijeriya, Inda Kafin Hakan, Da Kuma Bayan Hakan, Babu Wani Shugaban Nijeriya, Wanda Ya Girmama Al'umma, Ta Hanyar Maida Garuruwansu Su Koma Jihohi, Don Kowa Ya Samu 'Yanci, Amfanin Gwamnati Ya Zo Kusa. Ga Jerin Jihohin Da Ya 'Kirkiro Kamar Haka:

Jihar Adamawa.

Jihar Katsina.

Jihar Jigawa.

Jihar Yobe.

Jihar Kebbi.

Jihar Delta.

Jihar Edo.

Jihar Taraba.

Jihar Kogi.

Jihar Abia.

Jihar Osun.

Jihar Enugu.

Jihar Akwa Ibom.

Shugaba Babangida Ne Ya Yawaita kananan hukumomi Har Yawansu Ya Kai 774, Babu Mamaki Kai Da Ke Karanta Rubutun Nan, Idan Ba Domin Hakan Da IBB Ya Yi Ba, Da Wata'kin Har Yanzu Jiharku Babu Ita A Jerin Jihohin Najeriya Da Muke Da Su A Yanzu, Haka Nan Kuma, Da Yanzu Kana Cikin Wata karamar hukuma Ne A Jone, Amma Sai Ga Shi Saboda Kishin Ci Gaban Rayuwarka IBB 'Din Da Babu Mamaki Har Da Kai Ake Zama Ana Cin Mutuncinsa Da Zaginsa, Shi Ne Dai Mai Kaunarka, Tunda Ga Shi Nan Ya Kirkiro Muku jihar Da karamar hukuma Wanda Hakan Ce Ma Ta Ba Ka Damar Samun Bakin Magana!
Shugaba Babangida Ya Bar Dollar Amurka Kan Farashin ₦18, Sannan Ba A Ta'ba Ganin Layin Man-Fetur Ba, Koda Kuwa Sau 'Daya Ne, Duk A Tsawon Watanni 96 Da Ya Yi, Yana Mulkar Najeriya. Shi Ne Shugaban Da Ya Fara Samar Da Boreholes A 'Kauyukan Da Pipes 'Din Famfo Bai 'Karasa Ba, Har Ila Yau, A Zamanin Mulkinsa Ne 'Yan Najeriya Da S**a Ga Ruwan Famfo A Ko'ina Ba Wahala, Sai Mutum Ya Bud'e Ya Kunna Ya Yi Amfani Da Shi, Idan Ya Gama Sai Ya Yi Tafiyarsa Ya Bar Kan Famfon A Kunne Yana Ta Zubar Da Ruwa A Banza, Saboda Irin Yadda IBB Ya Jajirce Ya Tabbatar Da Ganin Ruwan Famfon Ya Wadaci Kowa, Kuma Ya Shiga Kowane Lungu Da Sa'ko!

Amma A Haka Ne Muke Zagin IBB 'Din.

Daga Khalid Abdullahi

16/08/2024

Mazaje Kuji Tsoron Allah Ku Sauke Nauyin Haƙƙin Iyalin Ku Dake Kawunan Ku.....

A kusan kullum rana ina haɗuwa da abubuwan tashin hankali da ya shafi auratayya musamman ta rayuwar Malam Bahaushe, Al'amarin mu Hausawa yana da ban tsoro da yawa mazaje basu sauke nauyin haƙƙin iyalin su da yake kawunan su.

Daga ranar da aka ɗauka maka aure cewa ake, cin ta, suturta da wurin zama ya tashi daga hannun iyayenta ya dawo kanka wannan wani Alƙawali ne Ka ɗaukar ma kanka a gaban jama'a da mala'iku da Aljannun da s**a halarci wurin Ɗaurin Auren Ku, toh amma tayaya zaka zo ka karya Alƙawalin da ka ɗauko cikin ɗaruruwan Mutane da sauran ababen hallita.

Mazaje da dama yanzu da zarar sun ɗurawa mace ciki sai su barta da ɗawainiya da kanta kuma abun takaici idan an gudu an bar matan wasu ake zuwa wasu wuraren a ƙara ɗauka wannan wane irin tunani ne Hausawa suke dashi.

Akwai Matan da aka kawo mani koken cewa Mijin su ya tafi ya barsu sama da Shekara Biyar ba Labari ba zuwa ba aike, abokin shi ma da yasan inda yake idan anyi mashi Magana sai ya noke yaƙi bada bayanin Inda yake, malam shiru mulunkwai ba zuwa ba aike.

Wannan wace irin rayuwa ce haka kullum haihuwa ake amma babu mai bada tarbiyya saboda Uba ya gudu Uwa itace zatayi ta Faɗi tashi wajen ganin yaran sun Rayuwa, idan Allah ya jaraba su suma ƴaƴa matan wasu daga ciki su samu miji irin Mahaifin su haka zasu ƙare cikin Wahala.

Address

Hausa
Lagos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SANIN yakamata posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share