
23/06/2022
Kuskure Mafi Muni Da ‘Yan Arewa Za Su Tafka Shine Zaben Tinubu A Matsayin’ Shugaban Nijeriya
Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Tabbas ‘yan Arewa za su tafka babban kuskure idan har s**a zabi Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya.
Domin na tabbata matsalar arewa ba matsalar Tinubu bace kuma bazata taba zama matsalar shi ba.
Ta yaya zaku gasgata wannan maganar tawa.
1) Yau kusan shekaru 15 kenan yankunan arewa na fama da matsalar rashin tsaro ta kowace fuska.
Domin yankin arewa maso gabas na fuskantar matsalar ta'addancin Boko Haram' Yankin arewa maso yamma na fuskantar matsalar ta'addancin masu garkuwa da mutane' Yankin arewa ta tsakiya na fuskantar matsalar rikicin kabilanci.
Tambaya anan itace shin sau nawa Tinubu ya taba nuna damuwar shi akan wannan matsalar da yankunan arewa ke fuskanta? Kuma sau nawa ya ziyarci sarakunan arewa ko gwamnonin arewa domin bada tashi gudun muwar ko jajantawa akan matsalar da yankunan arewa ke fuskanta?
2) Ayankin arewa an kashe yara kanana' da tsuffi' An kashe limamai da sarakunan garuruwa' An kashe shugaban yan bangan gari' An kashe mace a gaban mijin ta' An kashe miji a gaban matar shi' An kashe uba a gaban dan shi' An kashe da a gaban uban shi amma kun taba jin Tinubu ya nuna damuwar shi akan wannan?
3) A matsayin Tinubu na dan Nijeriya koda ya taba ikirarin cewa bai yadda da Nijeriya a matsayin kasa daya ba wanda ayyukan shi sun tabbatar da haka' Amma Tinubu ya fito daga yankin kudu maso yammacin Nijeriya ne watau yankin yarbawa.
A yankin kudu maso yammacin Nijeriya akwai jihohi guda 6 watau Lagos- Osun- Ogun- Odo- Ekiti- Oyo wa'innan sune jihohin da suke yankin da Tinubu ya fito' Amma abun mamaki anan shine duk lokacin da yan arewa zasu fada cikin wani hali na rashin tsaro a cikin wa'innan jihohin ko sau daya Tinubu bai taba nuna damuwar shi akai ba ballan tana ya jajantawa manyan arewa.
Akwai abubuwan da s**a faru da yan arewa a cikin jihar Lagos daga 1999 zuwa 2007 alokacin Tinubu shine gwamnan jihar Lagos' Nasan da