23/09/2025
DA DUMI DUMI:
Al’ummar Toungo, daga Timbokum zuwa Nayena, na shirin shiga sabon zamani na ci gaba da walwala.
Ɗan Majalisar da ke wakiltar Toungo a Majalisar Dokokin Jihar Adamawa, Hon. Kefas Kalvin (Me Yanci), ya bayyana fara manyan ayyuka da za su kawo sauyi ga rayuwar jama’a.
Ayyukan da za a fara sun haÉ—a da:
✅ Faɗaɗa Wutar Lantarki – An tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba wutar lantarki za ta isa ga al’ummomin da ke tsakanin Timbokum da Nayena. Hon. Kefas ya bayyana cewa wannan aikin ya fito ne daga roƙonsa ga Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ya amince kuma ya ba da izinin fara aikin.
✅ Katanga da Gatehouse ga GSS Toungo – An kuma tabbatar da cewa za a gina katangar makaranta da ƙofar shiga (gatehouse) a Makarantar Sakandaren Gwamnati Toungo, domin ƙara tsaro da inganci ga ɗalibai.
Wannan ci gaban na daga cikin matakai masu muhimmanci da za su kawo tsaro, sauƙi da ingantaccen ilimi ga al’ummar yankin.
Hon. Kefas Kalvin ya jaddada cewa ya jajirce wajen ganin ya cika alƙawuransa da kawo ci gaba ga mazabarsa.
> “Toungo na tashi. Mun gode Fresh Air, mun gode Mr. Yanci,” in ji jami’in yaɗa labarai na dan majalisar, Adam Umar a cikin sanarwar da ya fitar.
Future Network
Inda Gaskiya Ake Rayuwa.