05/06/2020
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH
Hakika muna mika godiyar mu ga mahalicinmu Allah (SWA) Sannan tsira da amincin Allah su tabbata ga annabin mu annabi Muhammad (SAW) da ahlinsa da sahabbansa da mutanen kirki har izuwa ranar sakamako amin. ina so in tunatar da kawunan mu game da azumi sitti shawwal wanda manzon Allah saw yace duk wanda ya azumci ramadana kuma ya bishi da azumi shida na watan shawwal za'a bashi ladan kamar ya azumci shekara guda.abin lura:-
AZUMIN WATAN RAMADAN 29/30 + AZUMIN WATAN SHAWWAL 6 = AZUMIN SHEKARA 1 = wata goma sha biyu , kwana 360+. kuma mun san cewa Allah swa ya fada acan karshen suratul an'am cewa duk wanda yazo da aikin lada guda 1 to zai ninka masa sau 10.
hakika jamaa lallai kam ya kamata mu dage mu kwashi wannan falalar daga Allah swa.gamu dai acikin watan yanxu muka ci 1 bisa 3 mu dage mu axumci wannan kwanakin da fatan Allah yasa muna daga cikin wadanda Allah ya 'yanta acikin wannan wata da ya wuce Allah ka shiryemu ka sa Aljannace makomar mu,ka kawomana mafita ka azurta mu da shuwagabanni na gari ka kaddara alkhairi a rayuwar mu amin.. don Allah idan anaga kuskure ayi hakuri kuma asanar dani ta comment ALLAH YAYI MANA ALBARKA NI DAKU AMIN NAKU ''Dalibus sunni''