
09/07/2025
SEN. ABDUL NINGI CONTACT & MOBILIZATION PROJECT TA KADDAMAR DA SABON JERSEY GA ‘YAN KWALLONTA,
Kungiyar fafutuka mai neman hadin kan jama’a, Sen. Abdul Ningi Contact & Mobilization Project 2027, ta kaddamar da sabon jersey ga ‘yan wasan kwallon kafa na kungiyar, tare da shirya wasan sada zumunci a filin wasa na Sir Abubakar Tafawa Balewa Stadium, Bauchi.
Wasan sada zumuncin ya gudana tsakanin kungiyar da Green Fillers, inda aka buga wasa cikin aminci, nishadi da girmama juna, wanda ya kara dankon zumunci tsakanin matasa.
Hakika, wannan lamari na daga cikin kyawawan ayyukan kungiyar wajen karfafa hadin kan matasa da bunkasa harkar wasanni a jihar Bauchi, domin ganin matasa sun kasance masu koshin lafiya, hazaka da kishin ci gaban jiharsu.
Kungiyar Sen. Abdul Ningi Contact & Mobilization Project 2027 ta cancanci yabo bisa jajircewarta wajen aiwatar da shirye-shirye na ci gaban matasa da al’umma baki daya, tana aiki tukuru ba tare da kasala ba domin ganin jihar Bauchi ta ci gaba a kowane fanni.
Ayyukan kungiyar suna daga cikin kokarin tabbatar da nasarar Sen. Abdul Ahmed Ningi a kowane lokaci da mataki, da ikon Allah. Allah ya tabbatar da nasara.
Sen. Abdul Ningi Contact and mobilazation project 2027 Media Team ✍️