Fitila Hausa News

Fitila Hausa News Fitila Hausa gidan Sahihan Labarai da Nishadi.

04/09/2026

*Rasuwar Sarkin Gumel Babban Rashi ce ga Masarautun Gargajiya da Nijeriya* – Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Mai Martaba Alhaji Dakta Ahmed Muhammad Sani II, CON, a matsayin babban rashi ga Jihar Jigawa da Nijeriya baki ɗaya.

Shettima ya ce marigayi Sarkin ya kasance daga cikin sarakunan gargajiya da s**a sadaukar da shekaru masu yawa wajen tabbatar da zaman lafiya, bunƙasa ilimi, ci gaban al’umma da ƙarfafa haɗin kan ƴan ƙasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Jihar Jigawa, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayin da Masarautar Gumel, inda ya isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya.

Marigayi Sarkin Gumel na 16 ya rasu a birnin Alkahira na ƙasar Masar a ranar 3 ga Satumba, 2026, bayan shafe kusan shekaru 46 yana mulkin masarautar. Ya hau karagar mulki ne a ranar 16 ga Disamba, 1980.

Mataimakin Shugaban Ƙasan ya ce za a tuna da marigayi Sarkin ne saboda tsawon mulkinsa, tare da hikima, zaman lafiya da kishin al’ummar da ya nuna wajen gudanar da shugabancinsa.

Ya bayyana shi a matsayin uba, mai haɗa kan jama’a, kuma mai bayar da shawarwari, wanda hikimarsa ta taimaka wajen hidimtawa al’umma da ƙasa tsawon kusan rabin ƙarni.

Shettima ya ce duk da cewa mulkin marigayin ya gudana a lokacin da Nijeriya ta fuskanci sauye-sauyen siyasa da zamantakewa da dama, ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, ilimi, karatun addinin Musulunci da zaman tare cikin lumana.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu yana matuƙar girmama marigayi Sarkin, musamman bisa gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al’umma.

Shettima ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdausi, tare da ba iyalansa, Masarautar Gumel da al’ummar Jihar Jigawa haƙurin jure wannan babban rashi.

JAM'IYYAR ADC TA SAKI SUNAYEN YAN TAKARAR GWAMNA A JIHOHIN DA ZA'A GUDANAR DA ZAƁE A 2027.ADC ta bayyana ‘yan takararta ...
04/09/2026

JAM'IYYAR ADC TA SAKI SUNAYEN YAN TAKARAR GWAMNA A JIHOHIN DA ZA'A GUDANAR DA ZAƁE A 2027.

ADC ta bayyana ‘yan takararta na gwamna a jihohi 28 a zaɓen 2027.

Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana sunayen ‘yan takararta na kujerar gwamna da mataimakansu da za su fafata a zaɓen 2027.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Juma’a, ya ce jerin sunayen ya ƙunshi ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar a jihohi 28.

FARASHIN LITAR MAN FETUR ZAI KOMA NAIRA DUBU BIYAR A SABUWAR SHEKARA.Jaridar Tribune ta ruwaito cewa farashin man fetur ...
04/09/2026

FARASHIN LITAR MAN FETUR ZAI KOMA NAIRA DUBU BIYAR A SABUWAR SHEKARA.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa farashin man fetur zai haura zuwa Naira 5,000 duk lita guda daga watan Mayu na shekarar 2027 mai zuwa.

Sai dai ƙaruwar farashin yana karkashin tsarin gwamnatin shugaba Tunibu ne idan yayi nasarar zarcewa shugaban kasar karo na biyu.

Boko Haram Ta Kai Hari Kan Tawagar Dan Takarar Gwamnan APC a BornoRahotanni sun ce wata fashewa ta afku yayin da ake zar...
04/09/2026

Boko Haram Ta Kai Hari Kan Tawagar Dan Takarar Gwamnan APC a Borno

Rahotanni sun ce wata fashewa ta afku yayin da ake zargin Boko Haram ta kai hari kan ayarin motocin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a Jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Alhamis, lokacin da ɗan takarar da tawagarsa ke kan hanyarsu ta komawa Maiduguri bayan kammala ziyarar godiya a garin Damasak, da ke kan iyakar jihar

04/09/2026

BAMUYI BAMUYI !!!

BIDIYO: A jihar Kebbi ne wata gajeruwar Bidiyo ta ɓilla inda aka hango gungun jama'a na faɗar Bamayi yayin wani taron siyasa na jam'iyyar APC.

YANZU-YANZU:  Fadar shugaban kasa ta tabbatar da shugaba Tunibu na fuskantar Shari'a game da zargin dillancin kwayoyi a ...
03/09/2026

YANZU-YANZU: Fadar shugaban kasa ta tabbatar da shugaba Tunibu na fuskantar Shari'a game da zargin dillancin kwayoyi a wata kotu dake Amurka.

Pantami Ya Samu Kashi 84% cikin  Kuri’u 58,000Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Isa Ali Ibrahim Panta...
03/09/2026

Pantami Ya Samu Kashi 84% cikin Kuri’u 58,000

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya fi samun goyon baya a wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a daban-daban da aka gudanar ta yanar gizo dangane da zaben gwamnan Jihar Gombe na shekarar 2027, inda ya samu gagarumar rinjaye kan sauran masu neman takara.

Hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta wallafa bayanan ’yan takarar da jam’iyyun siyasa s**a tsayar domin zaben gwamna da na ’yan majalisun dokokin jihohi na shekarar 2027 a fadin kasar.

DA DUMI-DUMI: Shugabannin jam'iyyar ADC na gundumoni 10 a karamar hukumar Funakaye sun fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyya...
03/09/2026

DA DUMI-DUMI: Shugabannin jam'iyyar ADC na gundumoni 10 a karamar hukumar Funakaye sun fice daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar PDP domin marawa Professor Isa Ali Pantami baya da sauran 'yan takarar jam’iyyar PDP.

A jiya Laraba shugabannin gundumoni 10 na asalin ’yan jam’iyyar ADC a karamar Funakaye sun fice daga jam'iyyar zuwa jam’iyyar PDP, domin mara wa Professor Isa Ali Pantami da Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo baya a babban zaben 2027 da take tafe da sauran 'yan takarar jam’iyyar PDP.

Shugabannin gundumonin tare da mambobinsu da adadinsu ya haura dubu 2,000, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga tafiyar Professor Pantami a wani gagarumin taro da aka gudanar a garin Funakaye.

Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Funakaye, ciki har da shugaban PDP na karamar hukumar Funakaye, shugaban Dattawa Zannan Funakaye, hamshakin ɗan kasuwa Al-Amash, wanda aka gudanar da taron a filin motocinsa, da Chikasoron Funakaye, tare da sauran manyan jiga-jigan siyasa da al’umma.

A yayin taron, waɗanda s**a sauya sheƙar sun bayyana aniyarsu ta yin aiki tukuru wajen ƙarfafa tafiyar PDP da tabbatar da nasarar Professor Isa Ali Pantami da Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo a zaben 2027.

Wannan sauyin sheƙar yana ƙara nuna yadda tafiyar Professor Pantami ke samun karɓuwa a tsakanin al’umma da masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi.

Jami'an tsaro sun k**a ɗaya dagacikin mutanen da ake zargi da kitsa satar mutane acikin masallacin jumu'ah dake garin "D...
03/09/2026

Jami'an tsaro sun k**a ɗaya dagacikin mutanen da ake zargi da kitsa satar mutane acikin masallacin jumu'ah dake garin "Dekara" Borgu Local Government, Niger State.

03/09/2026

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya mika sakon Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na ta'aziyya ga gwamnatin jihar Neja ga kuma iyalan margayi Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Kasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf Wushishi.

Ministan ya isar da sakon ta'aziyyar ne a yau Laraba, a Minna, jihar Neja.

Address

Lagos
100001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fitila Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share