Sahl Noor

Sahl Noor “Wannan shafi an kirkire shi ne domin yada ingantaccen ilimin Musulunci bisa Al-Qur’ani da Sunnah cikin sauƙi da hikima.”

*GOMAN FARKON DHUL-HIJJAH.*Dukkanin wani mutumin kirki na ƙwarai wanda yake neman kusanci ga ubangijinsa Allah maɗaukaki...
21/05/2026

*GOMAN FARKON DHUL-HIJJAH.*

Dukkanin wani mutumin kirki na ƙwarai wanda yake neman kusanci ga ubangijinsa Allah maɗaukakin sarki, yakan yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya ribaci waɗannan kwanukan ta hanyar aikata kyawawan aiyuka na gari, da kuma kamewa daga munanan aiyuka na banza, lallai yin hakan yana samar wa da bawa yardar ubangijinsa da kuma amincinsa"
-
"Kayi ƙoƙarin ribatarsu kaima, ta yadda za ka kasance cikin masu yin ƙoƙari wajen neman yardar Allah buwayi da ƙara kusanci zuwa gare shi"
-
"Haƙiƙa Sa'eed Bin Jubair Allah ya ƙara masa yarda, ya kasance idan kwanaki goman farkon watan zul-hijjah s**a shiga, yana yin jihadi jihadi mai tsanani (wajen bautar Allah da biyayya gareshi da dukkanin dangogin aiyukan ɗa'a ga Allah acikinsu) hatta ma har irin abin da ya kasance ba ya iya yin irinsa, (hatta irin abin da yake gagararsa aikata shi, to ya kasance yana aikata shi acikin waɗannan kwanakin koda kuwa cikin wahala ne domin neman kusanci da Allah mahaliccinsa)"
سنن الدارمي: (41/2)

05/05/2026

04/05/2026

04/05/2026

04/05/2026

Address

Lagos

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sahl Noor posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share