KHM TV

KHM TV KHM TV HAUSA - Kamfanin Jarida Ce Mai Zaman Kanta, Da Take Watsa Ingantattun Labaran Duniya. An Bude Wannan Tashar Ne A Ranar Asabar 17th June, 2023.

Labari Da Duminsa: Laftanar Yerima, ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi a Abuja.  Vanguard News ✍️
16/11/2025

Labari Da Duminsa: Laftanar Yerima, ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi a Abuja.

Vanguard News ✍️

RAHOTO: Yadda wasan kwallon kafa na Gwabna Uba Sani ya gudana a Babban filin wasan kwallon kafa na Garin Lere, wanda Hon...
16/11/2025

RAHOTO: Yadda wasan kwallon kafa na Gwabna Uba Sani ya gudana a Babban filin wasan kwallon kafa na Garin Lere, wanda Hon. Danladi Musa Zannan Lere (S.A Protocol ga gwamnar jihar Kaduna)

Cikakken Sakamakon Wasan Yau Lahadi 16 ga watan Nuwamba 2025:

FC HARRY 1 – 0 FC KARIMBO UNITED

Wasan gobe:

FC DAMO vs SUGAU UNITED

Ku cigaba da kasancewa tare da KHM TV HAUSA.

16/11/2025

Yayin da Shugaban Karamar Hukumar Lere dake jahar Kaduna Hon. Jafaru Ahmed yake cika shekara daya a Mulki. Sabon Birni Ward APC Stake Holders sun Karrama shi da lambar yabo na musamman a jiya Asabar.

KHM TV HAUSA

KHM TV TA HALARCI WAJEN TARON ZUMUNTAN MATAN ECWA:Kafar Watsa Labarai ta KHM TV HAUSA ta Ziyarci farfajiyan taron Matan ...
16/11/2025

KHM TV TA HALARCI WAJEN TARON ZUMUNTAN MATAN ECWA:

Kafar Watsa Labarai ta KHM TV HAUSA ta Ziyarci farfajiyan taron Matan Zumunta na ECWA da Ake Gudanar dashi duk shekara, inda wannan Karon aka gudanar a Garin Unguwar Bawa, KHM ta samu tattaunawa da wasu daga cikin mahalarta taron, kamar yanda zamu kawo muku acikin Bidiyo.

Yanda wata babbar mota ɗauke da dabbobi ta faɗo daga saman gadar Hotoro da ke Kano, dabbobin da suke cikinta raguna da a...
16/11/2025

Yanda wata babbar mota ɗauke da dabbobi ta faɗo daga saman gadar Hotoro da ke Kano, dabbobin da suke cikinta raguna da akuyoyi sun tarwatse a ƙasan gadar.

Kawo yanzu dai babu labarin asarar rai a hatsarin. Allah ya kiyaye gaba.

A chigaba da fafutukar Neman zuwa Gasar cin Kofin Duniya da misalin karfe 8:00 na daren wannan rana ta Lahadi tawagar Su...
16/11/2025

A chigaba da fafutukar Neman zuwa Gasar cin Kofin Duniya da misalin karfe 8:00 na daren wannan rana ta Lahadi tawagar Super Eagles ta Nijeriya za ta fafata da kasar Congo, a neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya na 2026.

Nawa da nawa kuke sa ran za a tashi daga wannan wasa?

16/11/2025

BAYAN FAGE: Yadda ma’aikatanmu ke aiki tukuru ba dare ba rana, domin kawo muku sahihan rahotanni daga gida da waje.

Ku ci gaba da bibiyar tashar KHM TV HAUSA – cikar burinku shine muradinmu.

Dan Asalin Karamar Hukumar Lere ya jagoranci hura wasa a matakin kasa:Mansoor Abubakar, ɗan asalin Karamar Hukumar Lere,...
16/11/2025

Dan Asalin Karamar Hukumar Lere ya jagoranci hura wasa a matakin kasa:

Mansoor Abubakar, ɗan asalin Karamar Hukumar Lere, Saminaka dake jihar Kaduna, ya jagoranci hura wasan Bichi First vs Yobe Desert a jiya, 15–11–2025, a garin Kano.

Wannan wasa na daya daga cikin gasa mai daraja ta biyu a Najeriya, wato National Nigeria League (NNL), inda ƙwarewarsa ta kai shi wannan matsayi.

An tashi da sakamakon: Bichi First 3 – 0 Yobe Desert.

Dukkan ƙungiyoyin biyu sun nuna gamsuwa da jin daɗi da irin kwarewa da kwantar da hankali da ya nuna yayin hura wasan.

Muna fatan ganin shi ya kai ga hura wasannin NPFL nan bada jimawa ba, da kuma ci gaba da samun nasarori masu girma har zuwa turai.

Wane fata za ku yi masa?

KHM TV HAUSA

Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad, ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, da ya kawo Tauraron kw...
16/11/2025

Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad, ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, da ya kawo Tauraron kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, da sauran ‘yan kwallon kasar Portugal Najeriya su yi wasa.

A cewar sa, hakan zai taimaka matuka wajan farantawa ‘yan Najeriya rai musamman kamin zaben shekarar 2027.

Malam Bashir yace dalilin sa, shine mafi yawan ‘yan Najeriya masoya Cristiano Ronaldo ne.

Shin ya kuke ganin wannan maganar?

DA DUMI-DUMI: Shugaban Kungiyan "Kautal Pulaaku Fulbe Association of Nigeria Reshen Jihar Kaduna Abbas J. Julde ya yi ti...
16/11/2025

DA DUMI-DUMI: Shugaban Kungiyan "Kautal Pulaaku Fulbe Association of Nigeria Reshen Jihar Kaduna Abbas J. Julde ya yi tir da Allah wadai ga duk wanda ke cikin gurbatattun mutanen da s**a aikata ta'addanci ga al'umman garin Gidan Waya ta Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.

Ya jajantawa yan'uwan wadanda abin ya shafesu. Allah Ya kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su. Shugaban Kungiyan yana kira ga jami'an tsaro da su dauki matakin da ya dace ga duk wanda aka samu hanunshi a cikin wannan ta'addanci.

KHM TV HAUSA

16/11/2025

An horas da ma'aikatanta KHM TV HAUSA akan kara sanin makaman aiki domin kara inganta ayyukan kafar.

KHM TV HAUSA

15/11/2025

Tattaunawa na musamman tare da Yusuf Abdullahi Dialogue game da yanda taron zaben Shuwagabannin Jam'iyyar PDP na kasa yake gudana kai tsaye daga Oyo dake jahar Ibadan.

KHM TV HAUSA

Address

Lere Local Government
Lere

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KHM TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share