
23/07/2025
Shugaban jam'iyyar APC na jahar Kano Abdullahi Abbas ya fara aiki a hukumar kula da kayan Noma ta Ƙasa
Babban Kwamandan Hukumar kula da Tsaftar Kayayyakin Noma ta Ƙasa (NAQS), Dr. Vincent Isegbe, a yau ya karɓi shugaban kwamitin gudanarwa na NAQS, Alhaji Abdullahi Abbas, a ziyararsa ta farko a hukumance zuwa Hedkwatar hukumar da ke Abuja.
Shugaban kwamitin ya samu tarba mai kyau daga Babban Kwamanda tare da sauran membobin hukumar gudanarwa da jami’an da ke hedkwatar. A yayin zaman tattaunawa, Babban Kwamanda ya gabatar da cikakken bayani kan tsarin hukumar, ayyukanta, manufofin dabarunta, tare da irin rawar da take takawa wajen kare tattalin arzikin noma na Najeriya.