First Aid Group Of Fityanul Islam Borno m.m.c Local Govt

First Aid Group Of Fityanul Islam Borno m.m.c Local Govt RABIU BABAYO JAMI'IN EDITA NA TAWAGAR FAG/FIN/BORN/MEDIA.

09/12/2025
26/11/2025
26/11/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Sayyadi Dauda, Bello Yahaya, Abba Mohammed Malah

Best photography of the day 💥🔥           💥𝙑𝘼𝘾𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💥𝙏𝙄𝙈𝙀💥💥 Good Night Nat. President Fityanul Islam Of Nigerian.💥💥⚡
18/11/2025

Best photography of the day 💥🔥
💥𝙑𝘼𝘾𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💥𝙏𝙄𝙈𝙀💥

💥 Good Night Nat. President Fityanul Islam Of Nigerian.💥💥⚡

Da Dumi-Dumi: An tashi da wani labari mai rudani a Najeriya.Shin kunji wan nan batun?
18/10/2025

Da Dumi-Dumi: An tashi da wani labari mai rudani a Najeriya.

Shin kunji wan nan batun?

🤝 ZIYARA TARE DA JAJEN JINYACikin kokarin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin membobin Kungiyar Fityanul Islam, Capt...
12/10/2025

🤝 ZIYARA TARE DA JAJEN JINYA

Cikin kokarin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakanin membobin Kungiyar Fityanul Islam, Capt. Rabiu Babayo 🧢 ya jagoranci wata tawagar ‘yan agaji daga Moduganari Detachment (FAG) wajen kai ziyarar taya murna 🎉 ga wani memban kungiyar da mahaifiyarsa ta samu haihuwa 🍼.

Tawagar ta kuma ziyarci wasu daga cikin membobin da ke jinya 🏥 tare da yi musu jajen jinya 🤲 da addu’ar samun lafiya.

Wannan aiki ya nuna ƙauna ❤️, haɗin kai 🤝, da sadaukarwa na ‘yan Fityanul Islam wajen tallafa wa junansu a lokutan farin ciki da na ƙunci.

_🙏 Allah ya albarkaci sabuwar haihuwa, ya ba marasa lafiya lafiya, ya kuma saka wa dukkan masu halarta da alheri. 🤍_

✍️ Rabiu Babayo

Kai tsaye daga Wajen taron Radin Sunan Yaron Maj. Musa Usman MMC Director FAG Fityanul Islam Borno State✍️ Rabiu Babayo
03/10/2025

Kai tsaye daga Wajen taron Radin Sunan Yaron Maj. Musa Usman MMC Director FAG Fityanul Islam Borno State

✍️ Rabiu Babayo

CONGRATULATIONS SIR! 🎉Da farin cikin marar misaltuwa, muna mika sakon taya murna amadadin Shugaban Kungiyar Fityanul Isl...
02/10/2025

CONGRATULATIONS SIR! 🎉

Da farin cikin marar misaltuwa, muna mika sakon taya murna amadadin Shugaban Kungiyar Fityanul Islam Reshen Jihar Borno, Prof. Sheikh Abba Saleh Ahmad Abulfathi RTA Maiduguri, ga ɗaya daga cikin jajirtattun shugabanninmu na jihar Borno, Dr. Ababa Sani Abagoni, Borno State Secretary Fityanul Islam, bisa samun wannan gagarumin nasara ta zama ASSOCIATE PROFESSOR.

🤲Allah Ya ƙara basira, hikima da nasarori a wannan sabon matsayi, Ya sanya ya zamo alheri ga al’umma baki ɗaya.

✍️ Rabiu Babayo

21/09/2025

Barka Da Safiya

SANARWAR!!!
21/09/2025

SANARWAR!!!

TUNATARWAAzumin Tasu’a da AshuraKungiyar Fityanul Islam of Nigeria tana tunatar da daukacin al’ummar Musulmi a fadin dun...
03/07/2025

TUNATARWA

Azumin Tasu’a da Ashura

Kungiyar Fityanul Islam of Nigeria tana tunatar da daukacin al’ummar Musulmi a fadin duniya, musamman ‘yan agaji da mambobin Kungiyar Fityanul Islam, muhimmancin yin azumin Tasu’a (Juma’a, 4 July, 2025 – 9 Muharram 1447H) da Ashura (Asabar, 5 July, 2025 – 10 Muharram 1447H).

Manzon Allah Saw ya azumci Ashura kuma ya umarci Musulmi su azumce ta. Daga baya ya ce:

“Idan na rayu zuwa shekara mai zuwa, zan azumci ranar tara 9 (Tasu’a) ma.”(Muslim

Saboda haka Sunnah ce Musulmi su azumci Tasu’a da Ashura, ko ku azumci Ashura kawai idan ba za ku iya duka biu ba.

Muna kira ga Musulmi su yi kokari su azumci wadannan ranaku, tare da addu’a domin zaman lafiya da cigaban Musulunci.

Allah Ya karbi ibadunmu. Amin.

✍️ Rabiu Babayo

BARAR ADDU'O'I BISA SACE KAWUN KHADIJAH MUHAMMAD BUKARSubhanallah! Allahumma ajirni fī muṣībatī.Muna cikin alhini da dam...
17/06/2025

BARAR ADDU'O'I BISA SACE KAWUN KHADIJAH MUHAMMAD BUKAR

Subhanallah! Allahumma ajirni fī muṣībatī.

Muna cikin alhini da damuwa matuƙa bayan samun rahoton sace kanin baban Khadijah Muhammad Bukar, wadda take rike da mukamin Deputy Director Admin, Women Wing, FAG FITYANUL ISLAM, reshen Jihar Borno.

Wannan mummunan lamari ya faru ne a wani kauye mai suna Goam cikin Jihar Borno, inda aka tabbatar da cewa ya kwashe tsawon kwanaki uku a hannun ‘yan ta’addan Boko Haram kafin a samu tabbacin lamarin a yau.

A madadin daukacin shugabanni da mambobin Fityanul Islam na Jihar Borno, muna miƙa wannan barar addu’a, ga daukacin al’umma da mambobin Fityanul Islam da su ci gaba da yin addu’o’i na musamman domin ceton wannan bawan Allah daga hannun masu aikata ta’asa. tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya kubutar da shi daga hannun azzalumai cikin koshin lafiya, ba tare da wata cuta ko lahani ba.

Allah Ka dawo mana da shi lafiya, cikin sauki da aminci!

✍️ Rabiu Babayo

Address

Moduganari Opposite Civil Defence Heat Quarter
Maiduguri
T

Telephone

+2348103488964

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First Aid Group Of Fityanul Islam Borno m.m.c Local Govt posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to First Aid Group Of Fityanul Islam Borno m.m.c Local Govt:

Share