30/10/2025
Tinubu ya umarci sabbin hafsoshin tsaro su zama masu hazaƙa wajen yakar ta’addanci da barazanar tsaro
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da ya nada su kasance masu samar da sabbin dabaru da jajircewa wajen tinkarar ta’addanci da barazanar tsaro da ke addabar kasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karrama sabbin hafsoshin tsaro da mukamansu a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.
Tinubu ya bayyana wannan yunƙurin a matsayin wata sabuwar aniya da jajircewar gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga ‘yan Najeriya baki ɗaya.
“Yau ba wai bikin ba da mukamai kawai muke yi ba, muna sabunta kudirinmu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasa. Sojojinmu sun bayar da gudunmawa mai girma wajen kare ƙasar nan, wasu ma sun sadaukar da rayukansu don zaman lafiyar Najeriya,” in ji shi.
Shugaban ya yaba da kokarin dakarun soji wajen dawo da zaman lafiya a yankunan da aka taba samun rikice-rikice da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, yana mai cewa hakan ya raunana ƙungiyoyin ta’addanci da ke ƙasar.
Sai dai ya gargadi sabbin hafsoshin cewa barazanar tsaro tana ta sauyawa, inda sabbin ƙungiyoyin ‘yan bindiga da masu tayar da hankali ke fitowa musamman a Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da wasu sassan Kudu.
“Ba za mu bari wannan barazanar ta ci gaba yaduwa ba. Dole mu yi gaggawa mu murƙushe su tun kafin su yi ƙarfi. Mu sare kan macijin tun wuri,” in ji Tinubu.
Ya kuma shawarce su da su yi amfani da fasahar zamani da sabbin dabaru domin su kasance gaba da waɗanda ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali na ƙasa.
“Ina so ku zama masu samar da sabbin dabaru, masu hangen nesa da jarumtaka. ‘Yan Najeriya suna jiran sakamako, ba ƙorafi ba,” in ji shugaban.
Shugaban ƙasar ya kuma sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa rundunonin soji da kayan aiki da duk wata bukata don cimma nasarar aiki.
A jawabinsa bayan karramawar, Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Olufemi Oluyede, wanda ya yi magana a madadin sauran hafsoshin, ya tabbatar da cewa za su yi aiki tare don magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.
“Ina tabbatar wa Shugaban ƙasa da ‘yan Najeriya cewa za mu yi iyakar kokarinmu wajen kawar da duk wani nau’in laifi da ta’addanci a Najeriya, domin a samu damar bunƙasar harkokin tattalin arziki da zaman lafiya,” in ji shi.
A cikin waɗanda aka karrama akwai Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu; Babban Hafsan Rundunar Ruwa, Vice Admiral Idi Abbas; Babban Hafsan Rundunar Sama, Air Marshal Sunday Aneke; da kuma Babban Daraktan Leken Asiri na hukumar Tsaro, Laftanar-Janar Emmanuel Undiandeye.
Bikin ya samu halartar iyalan hafsoshin da matayensu, inda s**a rantse da alkawarin bin doka da tsayawa kan rantsuwar ofis a gaban Shugaban ƙasa.