04/06/2025
Masu sana'ar turaren wuta da Humra da dama basu san yadda ake gyara FARCE ba, hakan yasa wasu da yawa ke korafi kan cewa farcensu yana wari kokuma wani yanayi daban sabanin kamshi. Ga yadda ake gyarashi.
Kafin in shiga cikin Bayanin inaso kusani cewa Farce na daya kamshi cikin abubuwa masu daraja da tasiri cikin kayayyakin hadin Turaren wuta ko humra domin a yanzu farashin farce 1kg yakusa 70k kuma yawansa baikai kwanon awo daya ba.
Da farko idan kuka siyo farce guda-gudansa daga kasuwa, abu na farko da zaku farayi shine tsincewa domin wani yana zuwa da abubuwan da ba'ason su shiga ciki kamar itace ko wani datti dai haka domin wani sassa ne na jikin wata dabba ake amfani dashi.
Daga nan zaku zubashi cikin mazubi kusa ruwa maikyau ku wankeshi sosai sannan ku kara zuba masa ruwa mai yawa ku jikashi yayi kamar kwana daya ko wuni biyu, dalilin jikawar shine dukkan fata da dattin dake jikinsa duk zasu taso sama ta yadda zaku ciresu cikin sauki (ammafa zakuji wari kafin ya koma kamshi 😂). Idan kuka kona farce batare da ancire wannan fatar ba shine zakuji ana korafi cewa farce yana wari ko kauri.... Bayan kun gama cire fatar a jiki zaku tsameshi a ruwan sannan ku daurayeshi ku sake cireshi daga ruwan daurayar.
Daga nan zaku zubashi cikin tukunya sannan ku samu Lemon tsami ku yanka ku matse aciki kubar har bawon lemon a cikin tukunyar. Bayan nan zaku iya samun gawayi (coal kusaka aciki domin yana janye wari) ku saka dan kadan a ciki, saiku samo KANINFARI ku daka shi ku zuba aciki shima, sannan ku samo VINEGAR (kaltufa) shima ku tsiyaya kadan a ciki shikuma zai taimaka wajen cire ragowar datti da fatar dake jiki, daga nan zaku samu RUWAN LAFINTA kowanne iri ku tsiyaya aciki shima, daga nan saiku debo ruwa ku zuba acikin tukunyar, sannan saiku dorashi a kan wuta a tafasa shi.
Dalilin yimai duk wannan hadin shine, idan akazo tafasawa yana wari idan ba'ayimasa wannan hadin ba wajen tafasawa warin zai dameku dan a hakan ma raguwa zaiyi bawai fita zaiyi dukka ba...
Wannan shine matakin farko na gyaran farce, in sha Allahu zamu cigaba har zuwa yadda ake soyashi har ayi aiki dashi ya koma mai kamshi