06/05/2022
Zaɓen Najeriya na 2023: APC da PDP na amfani da sabon salo na aiwatar da sauye-sauye
Sa'o'i 6 da s**a wuce
Manyan jam'iyyun siyasar Najeriya
Manyan jam`iyyun siyasar Najeriya biyu, wato APC da PDP sun fitar da wani sabon salo na aiwatar da sauye-sauye a cikin jadawalinsu na babban zaben da ke tafe.
Irin wannan sauyin kan shafi lokutan gudanar da zaben fid da gwani ko sayar da fom ga masu neman tsayawa takara, wanda wasu `yan kasar ke cewa yana daure musu kai.
APC da PDP, duka sun buge da wata dabi`a ta sassauya ranakun da suke tsayarwa don aiwatar da wadansu muhimman hidimomin da s**a shafi shirin tunkarar babban zaben 2023.
Jam'iyyun dai sun fara wani abu mai k**a da wasan `yar gala-gala ne tun lokacin da suke shirin gudanar da manyan tarukansu, na zabar shugabanninsu inda jam`iyya mai mulki ta yi ta sanya rana tana fasawa.
TALLA
A halin da ake ciki ma jam`iyyun biyu sai da s**a sassauya ranaku ko na wa`adin sayar da fom ga masu neman takara ko kuma uwa-uba, wato ranakun da za su gudanar da zabukan fid da gwani a wadansu matakai.
Zaɓen 2023: Jam'iyyun siyasar Najeriya sun ce sun kammala shiri
Dokar zaɓen Najeriya: Mece ce makomar ministocin Buhari da ke son tsayawa takara?
Zaɓen 2023: Ra'ayin 'yan APC ya bambanta kan ɓangaren da zai karɓi mulkin Najeriya
A kan maganar karba-karba ko shiyyar da za su kebe wa takarar shugaban kasa ma jam`iyyun sun yi ta yunkurawa kai ka ce gobe-gobe za su fadi matsayinsu amma shiru kake ji.
Irin wannan tafiyar kuran sai an yi gaba a koma baya, ko motsi da labewar da manyan jam`iyyun ke yi sun fara daure kan wasu `yan Najeriya.
To sai dai kuma masana siyasa, a nasu bangaren sun ce da sani jam`iyyun suke haka hasali ma dabarar yaki ce.
Dr Abubakar Kari, malami ne a jami`ar Abuja, ya shaida cewa, wadannan jam'iyyu k**ar suna fagen fama ne, kuma shi yaki yana bukatar shiri a don haka su wadannan jam'iyyu suna wadannan 'yan canje-canje ne domin su yi dai-dai da abubuwan da ke faruwa a cikin fagen siyasa.
Ya ce "abu na biyu kuma kowacce jam'iyya a cikin manyan guda biyu na la'akari da abubuwan da daya jam'iyyar ke yi domin ganin kodai ba a bar ta a baya ba, ko kuma ta samu galaba tun ma tafiya ba ta yi nisa ba."
Dr Abubakar Kari ya ce a yanzu duk wani taku da daya jam'iyya ta yi to zai iya yin tasirin a kan dayar.
Tuni dai jam`iyyar APC ta ce ba ta kwanto ko likimo da nufin kwashe wa wata kafa.
Ita ma jam`iyyar PDP ta ce ba ta shakkar kowa don haka a je a kara kawai.
Duk noke-noken da ake ganin k**ar manyan jam`iyyun na yi ta hanyar jinkirta daukar mataki ko sassauya ranakun gudanar da zabukan fid da gwanin dai, za a iya cewa yana da iyaka.
Tun da hukumar zabe ta gicciya sharadi da kuma wa`adin 3 ga watan Yuni, da kowacce jam`iyya za ta mika wa hukumar sunayen masu yi mata takara.