05/09/2025
Na ga wani darasi a kan mutanen nan sosai;
Idan kuka lura, zaku ga duk wanda daukaka ta fizga, shi ake nema ayi ta danganta kai da alaka dashi.
Sanda Gangalion yana tashe, shaguna da daidaikun mutane s**a rika nemansa suna video dashi saboda su jingina jikinsa su ma a sansu. Wasu kuma da wannan s**a yi amfani s**a tallata kasuwancinsu.
Haka Umar Bush. Har hotels zaka ganshi an kaishi ana jiyar dashi dadi kala-kala. Ya bar Kano ma gaba daya ya koma Abuja. Har ta kai ga an kirashi Villa an bashi wai matsayi, ko dai mene, an kirashi an bashi.
Yanzu kuma lura da Dan4ne da Maha. Yau ka ga wancan mai kudin ya kira su, gobe wancan ya kirasu ana video suna musu alheri suna amfani da daukakarsu suna tallata kawukansu, kamfanoninsu da kasuwancinsu.
Darasi;
A rayuwar nan, ba wanda ba zai nuna maka kauna ba a sanda ka samu daukaka. Kowa yana son daukaka a abunda ya saka gaba amma muna manta babban kalubale na ita kanta daukakar. Babu abunda yake jawo masoya na bogi, na karya, kamar daukaka. Mafi yawancin wanda zaka gani a jikinka, amfanuwa suke so suyi da kai ba wai kauna ce daga zuciya ba.
A sanda kake fama da kokarin gina kanka, ba wanda zai damu da kai. Amma daga sanda ka samu nasara, kowa zai nemi jingina da kai. Wani ma yana can yana amfani da sunanka amma baka sani ba, kuma ba mamaki soyayyar karya ce a zuciyarsa. Amma idan ya danganta kansa da kai zai samu wani abu a wajen wasu, shi yasa zai nuna ya sanka ko kuna da alaka.
Dukkan wadannan da na bada misali dasu haka take a kansu. Nan gaba kuma wasu za'a dakko a ajiye su. Daga sanda tauraruwar ta sauka daga kansu, daga sannan ne za'a watsar dasu. Kuna gani dai kwanaki aka rika maganar Umar Bush har ya koma gidan jiya. Masu amfani dashi din sun yi sun jingine shi kuma shikenan.
Babu wani abu da zai nuna maka soyayyar gaskiya daga mutane a sanda kayi nasara. Amma taka tsantsan yana da kyau a sanda duniya take yi da kai. Mafi yawan masu dariya tare da kai ba masoya bane, matsayinka suke kalla s**a makale maka sabida amfana da kai.
Allah sa mu dace.
✍️Mahmud galadanci