
17/12/2022
SHEIKH JAFARU ASSADIQ IBNU JARRAH, SUNAN DA GAUSI YA KIRA KA ALLAH YA ƘARA YARDA A GARE SHI.
Lamarin idan har ka riƙe shi ya wuce raɗaɗin jan garwashi a tafin hanu. Babu wani kwakwanto idan muka saka Maulana Sheikh Jafaru Ibn Jararah a cikin sahun farko da su kai yi riƙo da wannan garwashin wuta a tafin hanunsu, domin sun fuskanci kyamata, kyara, tsangwama, tozartawa, dukka sun yi fama da sama da waɗannan laifin su kawai dan sunce su almajiran Shehu Ibrahim Niasee ne Allah ya ƙara yarda a gare shi, kuma sun yi rikon da shi a duniyar su da kiyama.
An haifi Maulana Sheikh Jafaru Ibn Jararah Allah ya ƙara yarda a gare shi wani gari da ake kira da suna Ƙotai, da yake cikin ƙasar Katsina, ban samu wani kwakwanto a cikin samun sahihancin ranar haihuwarsa, ya sauka wannan duniyar a ranar Litinin 11 ga watan Rabi'ul Awwal, na shekarar 1326, Hijiriyya. Wanda ya yi daidai 12, ga watan Afrilu na shekarar 1908, miladiyya.
Sunan mahaifinsa Sheikh Malam Jarrah, har yanzu tarihin mahaifinsa a ƙasar Katsina, ba zai taɓa