
17/07/2025
Barista Ali Sa'adu Birnin Kudu
Lauya kuma ɗan siyasa, wanda aka fi sani da Barista Ali Sa’adu Birnin Kudu. Shi ne gwamnan farko na farar hula a jahar Jigawa.
Haihuwa
An haife shi a garin Birnin Kudu wanda shi ne helikwatar mulkin ƙaramar hukumar Birnin Kudu a ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1959.
Karatu
Barista Ali Sa’adu Birinin Kudu, ya yi karatunsa na firamare a garin Birnin Kudu, daga nan kuma ya samu nasarar shiga makarantar sakandare ta Birnin Kudu (Birnin Kudu Secondary School) wacce ta koma Kwalejin Gwamnati ta Birnin Kudu (Government College Birnin Kudu). Daga nan kuma ya ɗora zuwa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya inda ya yi karatun digiri a fannin doka (Bachelor Degree in Law), sannan bayan gamawarsa da shekara guda kuma ya samu tafiya makarantar aikin doka (Law School).
Fara shiga siyasa
Ya fara shiga harkar siyasa a shekarar 1983 a jamhuriya ta biyu. Ya samu tikitin tsayawa takarar majalisar wakilai a kan rusasshiyar jam'iyyar NPP a tsohuwar jihar Kano, amma bai ci zabe ba.
Ya yi takarar ne tare da marigayi tsohon gwamnan jihar Kano, Muhammadu Abubakar Rimi, wanda ke neman sake tsayawa takarar gwamna, bayan ya yi watsi da tsohuwar jam’iyyarsa ta asali ta Peoples Redemption Party (PRP), wadda marigayi Mallam Aminu Kano ya kafa da kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, wanda shi ma ya tsaya takarar kujerar majalisar wakilai ta kasa.
Aikin Banki
Ali Sa'adu yayi aiki a First Bank daga 1984 zuwa 1991.
Zamowarsa Gwamna
Kafin zamowarsa gwamna ya yi aiki da ma’aikatar Shari’a ta tsohuwar jahar Kano a tarayyar Najeriya na tsawon shekaru uku inda ya daga baya ya shiga siyasa a shekarar 1991. Ya kafa tarihin zamowarsa gwamnan farar hula na farko a Jahar Jigawa. An zaɓe shi ya zama gwamnan Jahar Jigawa a watan Disamba na shekarar 1991 a ƙarƙashin tutar jama’iyyar SDP (Social Democratic Party). A lokacin yana da shekaru 33 da haihuwa, ya k**a aiki a watan Janairu na shekarar 1992. Ya bada gudunmawa sosai wajen gina wannan jaha ta Jigawa. Mulkinsa ya ƙare a watan Disamba na shekarar 1993.
An ce yana cikin gwamnonin kalilan da ke da kusanci da kujerar mulki a matakin kasa. Sak**akon haka an ce ya samu gata mai yawa daga A*o Rock idan aka kwatanta da yawancin abokan aikinsa na wasu jihohi.
Siyasar Ali Sa’adu Birni Kudu ta samu cikas bayan juyin mulkin da sojoji s**a yi ba tare da zubar da jini ba wanda marigayi Janar Sani Abacha ya jagoranta. Bayan juyin mulkin, an haramta ayyukan siyasa a kasar.
Bayan ya bar mulki a matsayin gwamnan farar hula na farko a jihar Jigawa, Kudu ya fice daga harkokin siyasa a jihar har zuwa wani lokaci a shekarar 2003 inda ya sake gudanar da yakin neman zaben kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar NDP. Ya fafata da gwamnan jihar mai ci a lokacin, Saminu Turaki; amma ya fadi.
Bayan ya sha kaye a zaben 2003, tsohon gwamnan ya sake ficewa daga fagen siyasar jihar har zuwa shekarar 2007 inda ya ya koma jam'iyyar PDP.
Rubutawa Muhammad Cisse