15/10/2025
Zubaida Hasan ta fuskanci tiyata har sau 12 cikin shekara ɗaya kafin ta iya sake yin murmushi tun bayan da ta gamu da iftila’in mummunar ƙuna daga wutar murhun kalanzir lokacin tana ƴar shekara 9 a shekarar 2001.
Zubaida, wace take zaune ɗa iyayenta a cikin wani ƙauye a ƙasar Afghanistan ta gamu da iftila’in ne a yankin da ke fama da ƙarancin ƙwararrun likitoci da kayan aiki.
Mummunar ƙunar ta haifar da matsananciyar tattarewar fata har ta kai fuskarka da wuyanta da hannu ɗaya dukka sun manne da jikinta. Murmushi ba zai yiwu ba kuma ba za ta iya rufe idanuwanta ba, lamarin da ya sauya kamanninta tare munana fuskarta.
Cikin kulawa da tausayawa, mahaifinta ya ƙetara da ita daga Afghanistan har zuwa ƙasar Iran domin ta samu kulawar ƙwararrun likitoci.
Sai dai, bayan shafe kwanaki 20 a wani babban asibitin Iran ɗin, likitocin s**a ce ba za su iya ba ta kulawar da take buƙata ba, saboda da haka kuma s**a bai wa mahaifinta shawarar da ya dangana har lokacinta ya yi.
Sai dai, mahaifin nata bai ɗauki shawarar likitocin Iran ɗin ba, domin bai yi ƙasa a gwiwa ba! Ya sake garzaya wa da ita zuwa asibitin sansanin sojin Amurka da ke Kabul. Duk da ya fuskanci ƙalubalai iri-iri amma daga ƙarshe ya samu taimakon likitocin sojin Amurkan da ƙungiyar Red Cross da kuma wata gidauniyar taimakon masu ƙuna inda s**a yi haɗin gwiwa s**a taimaka aka kai Zubaida har zuwa Amurka domin samun kulawa.
A can Amurkan, an samu nasarar yi mata tiyata har 12 a Cibiyar Ƙuna ta Grossman Burn Center da ke Sherman Oaks Hospital a yankin California inda Dr. Peter Grossman ya jagoranci tiyatar har sau 12 cikin shekara ɗaya tak!
Waɗannan jerin tiyatar har sau 12 ya haifar da gagarumar nasara fiye da yadda ake zato, domin bayan tiyatar, Zubaida ta samu dawowar kyawun fuskarta kusan ɗari bisa ɗari tare da iya yin murmushi kamar yadda take iya yi a da.
Ba ita kaɗai ba, mahaifinta ma ya yi murmushi da matuƙar murna bisa gagarumar nasarar da aka samu bayan ɗebe ƙauna da rayuwar Zubaida a farkon iftila’in