28/03/2025                                                                            
                                    
                                                                            
                                            Kungiyar National Coalition for Asiwaju Mandate (NCAM) ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da kowace hadaka da ke da burin karbe mulki kawai.
A ranar 20 ga watan Maris, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa shi da wasu jiga-jigan ‘yan adawa za su hada kai don kwace mulki daga jam’iyyar APC a shekarar 2027.
Atiku ya yi wannan furuci ne a wani taro da ya samu halartar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, tsohon jigo a kwamitin aiki na APC, Salihu Lukman, da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, tare da wasu shugabannin ‘yan adawa.
Da yake magana a taron manema labarai a ranar Alhamis, shugaban NCAM na kasa, Isaac Ikpa, ya ce duk wata hadaka da ake yi domin son rai ba don amfanin kasa ba, ba za ta yi nasara ba.
> “Muna so ‘yan Najeriya su fahimci cewa wannan hadaka da ake magana a kai ba komai ba ce illa taron ‘yan siyasa masu neman shahara a idon jama’a.”
Ya ce kungiyar NCAM na nan daram a bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shirin sabunta fata da yake aiwatarwa.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan yunƙuri na neman mulki da karfi. Na su Atiku Abubakar da El-Rufai
> “Makomar kasar mu tana cikin hadari, kuma dole ne mu tsaya tsayin daka wajen kare nagartaccen mulki, jagoranci mai inganci, da ci gaban Najeriya.”
Ikpa ya bukaci ‘yan Najeriya da su duba tarihin shugabannin da ke cikin wannan hadaka domin tantance ko sun taba kawo ci gaba ga kasa.
Ya kuma shawarci ‘yan kasa da su mayar da hankali kan mulki da ci gaban kasa, maimakon harkokin siyasa da tuni ake yi wa 2027.