Labaran Kano

Labaran Kano Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Labaran Kano, Media/News Company, Maiduguri.

03/04/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Jamilu Magaji Musa Gandawa, Bellow Saidu Bellow, Îtx Légéñd Âppdøul, Itz Classic Dady, Yariman Dan Dume

29/03/2025

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta k**a Bilal Vila da Budurwar sa Armani.

DA ƊUMI-ƊUMINSA: 'Yan Sanda Sun Cafke Mutane 14 Da Ake Zarginsu Da Hannu Wajen Ƙone Mafarauta A Jihar EdoRundunar ‘Yan S...
28/03/2025

DA ƊUMI-ƊUMINSA: 'Yan Sanda Sun Cafke Mutane 14 Da Ake Zarginsu Da Hannu Wajen Ƙone Mafarauta A Jihar Edo

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo ta bayyana cewa ta k**a mutum 14 da ake zargi da hannu a kashe matafiya 16 a kan titin Uromi/Obajana da ke Udune Efandion, a Jihar Edo.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sanda, CSP Moses Joel Yamu, matafiyan 25 ne ke cikin wata babbar mota mai lamba KKF 225 XA, daga Elele, Jihar Rivers, lokacin da aka far musu.

Rahotanni sun nuna cewa vigilante sun tare motar a Uromi, inda s**a samu wasu daga cikin fasinjojin suna da bindigogi na gida (dane guns).

An ce an k**a wasu daga cikin su, amma bayan hayaniyar da ta kaure, sai wani ya daga murya yana cewa su 'yan fashi ne ko 'yan bindiga.

Wannan yasa mutane s**a harzuka, s**a far wa matafiyan, s**a kashe 16 daga cikinsu, sannan s**a kona motarsu.

Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Edo ta la’anci wannan danyen aiki, sannan ta tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

Ba Hawan Sallah a Kano.~Abdullahi Haruna Kiyawa (PPRO)
28/03/2025

Ba Hawan Sallah a Kano.

~Abdullahi Haruna Kiyawa (PPRO)


Kun yarda da wannan maganar?
28/03/2025

Kun yarda da wannan maganar?

DA ƊUMI-ƊUMI: Jami'an tsaro sun hallaka gawurtaccen ɗan ta'addan da ya addabi jihar Zamfara mai suna Ɗan Isuhu yau Alham...
28/03/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Jami'an tsaro sun hallaka gawurtaccen ɗan ta'addan da ya addabi jihar Zamfara mai suna Ɗan Isuhu yau Alhamis.

Ɗan Isuhu yana daga cikin fitattun ƴan ta'addan da s**a yi kaurin suna wajen ta'addanci a faɗin jihar Zamfara.

Kungiyar National Coalition for Asiwaju Mandate (NCAM) ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da kowace hadaka da ke da ...
28/03/2025

Kungiyar National Coalition for Asiwaju Mandate (NCAM) ta bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da kowace hadaka da ke da burin karbe mulki kawai.

A ranar 20 ga watan Maris, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa shi da wasu jiga-jigan ‘yan adawa za su hada kai don kwace mulki daga jam’iyyar APC a shekarar 2027.

Atiku ya yi wannan furuci ne a wani taro da ya samu halartar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, tsohon jigo a kwamitin aiki na APC, Salihu Lukman, da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, tare da wasu shugabannin ‘yan adawa.

Da yake magana a taron manema labarai a ranar Alhamis, shugaban NCAM na kasa, Isaac Ikpa, ya ce duk wata hadaka da ake yi domin son rai ba don amfanin kasa ba, ba za ta yi nasara ba.

> “Muna so ‘yan Najeriya su fahimci cewa wannan hadaka da ake magana a kai ba komai ba ce illa taron ‘yan siyasa masu neman shahara a idon jama’a.”

Ya ce kungiyar NCAM na nan daram a bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shirin sabunta fata da yake aiwatarwa.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan yunƙuri na neman mulki da karfi. Na su Atiku Abubakar da El-Rufai

> “Makomar kasar mu tana cikin hadari, kuma dole ne mu tsaya tsayin daka wajen kare nagartaccen mulki, jagoranci mai inganci, da ci gaban Najeriya.”

Ikpa ya bukaci ‘yan Najeriya da su duba tarihin shugabannin da ke cikin wannan hadaka domin tantance ko sun taba kawo ci gaba ga kasa.

Ya kuma shawarci ‘yan kasa da su mayar da hankali kan mulki da ci gaban kasa, maimakon harkokin siyasa da tuni ake yi wa 2027.

Gwamnatin Kano ta ɗage dokar taƙaita zirga-zirga ta ranar Asabar ɗin ƙarshen wata saboda zuwan sallah Hoto: Sanusi Batur...
27/03/2025

Gwamnatin Kano ta ɗage dokar taƙaita zirga-zirga ta ranar Asabar ɗin ƙarshen wata saboda zuwan sallah

Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Facebook




DA ƊUMI-ƊUMI: Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya janye batun gudanar da Hawan Sallah ƙarama na wannan shekarar.Mai martaba...
27/03/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ya janye batun gudanar da Hawan Sallah ƙarama na wannan shekarar.

Mai martaba sarki Aminu Ado Bayaro yace "Wannan ya biyo bayan shawarwari daga malamai, shugabanni, dakuma duba zaman lafiyar jihar Kano.

Sarki Aminu ya ƙara da cewa hawan sallah ba abune na a mutu ko ayi rai ba. Idan har hakan zai jawo salwantar rayuka ko dukiya, tabbas ya zama dole a haƙura.

Daga ƙarshe yayi kira da al'umma da ayi amfani da wannan lokaci wajen ziyara, da sauran ayyukan addini.

Me zaku ce ?

24/03/2025

Kun yarda da wannan zancen kuwa?


Gwamnan Kano ya bada guraben aikin gwamnati ga ɗaliban da aka kai ƙasar waje karatu Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabi...
24/03/2025

Gwamnan Kano ya bada guraben aikin gwamnati ga ɗaliban da aka kai ƙasar waje karatu

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ɗauki ɗalibai 54 aiki bayan sun kammala karatun digiri na biyu a kan harkar kiwon lafiya a kasar waje.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya baiyana hakan a wata sanarwa a jiya Asabar.

Ya ce gwamnan ya sanar da bada guraben aikin ne a liyafar buɗe-baki da ya yi da daliban, wanda su ka dawo daga India bayan sun yi karatun na shekara ɗaya a jami'ar Symbiosis International University a Ranar Juma'a.

Ya ce tuni an kammala duk wasu tsare-tsare ga ɗaliban na su fara aiki a asibitocin gwamnati domin inganta harkar lafiya a jihar.

Ya kuma h**e su da su yi amfani da ƙwarewar da su ka samo lokacin da su ke karatun a India a yayin gudanar da aiyukan su.

Address

Maiduguri

Telephone

+2348101261315

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Labaran Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Labaran Kano:

Share