01/07/2025
IRAN DA ISRA’ILA: Yaƙin kwana 12 bazai kasance na ƙarshe ba
Daga
Inuwa Waya
Yanayi da dalilan da s**a kawo dakatar da bude wuta tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ƙasar Isra’ila bayan yaƙin kwana goma sha biyu (12) sun bayyana ga duniya. Duk da ɓata-garin labarai da kafafen yaɗa labarai ke fitarwa dangane da ɓangaren da suke goyon baya, gaskiyar ita ce, duka ɓangarorin biyu — Iran da Isra’ila — sun nuna gajiya. Abin lura a nan shi ne cewa Isra’ila ta fi nuna gajiya har ta gayyaci Amurka da ta shiga yaƙin.
Da yaƙin ya ci gaba, babu wanda zai iya fadin yadda zai kare. Bayan dakatar da bude wuta, kowanne ɓangare ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara. Donald Trump ya bayyana cewa bama-bamai da Amurka ta harba a manyan cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran sun lalata shirin nukiliyarta gaba ɗaya. A cewarsa, zai dauki kusan shekaru 20 kafin Iran ta sake farawa da aikin haɓaka uranium. Haka kuma Isra’ila ta ayyana kanta a matsayin mai nasara, inda ta bayyana cewa kisan manyan masana nukiliya da kwamandojin soja na Iran ya jefa Jamhuriyar Musuluncin cikin mummunan rauni.
A ɓangaren Iran, ita ma ta ayyana nasara. Gaskiyar cewa sun kalubalanci Isra’ila kuma s**a jawo mummunan asara ga gine-gine da ofisoshin soja a cikin ƙasar, wata babbar kwanciyar hankali ce a wajensu. Harin da s**a kai a sansanin sojin Amurka da ke Qatar ma ya ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen ikirarin nasara.
Ikirarin nasara daga kowanne ɓangare abin fahimta ne. Abin damuwa shi ne yanda ɓangarorin s**a shiga muhawarar kalmomi bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Duk da cewa Trump ya ce sun rushe shirin nukiliyar Iran, ya kuma ce Amurka ba za ta yi wata-wata ba wajen sake kai hari idan Iran ta ci gaba da haɓaka uranium. Ya kara da cewa, saboda kalaman raini daga Shugaban addinin Iran a kansa, ya yanke shawarar kin dage takunkumin da ake wa Iran.
Isra’ila ta maimaita furucin Amurka, har ma ta kai ga yin barazanar kashe Ayatollah Khomeini da kifar da gwamnatin Iran gaba ɗaya tare da haddasa rikici a ƙasar. A ɓangaren Iran kuwa, ta rage muhimmancin harin da Amurka da Isra’ila s**a kai kan cibiyoyin nukiliyarta. Wasu majiyoyi daga Tehran sun ce Iran tana jiran dama mai tarihi don ta gama da barazanar Isra’ila har abada. Majiyar ta kara da cewa Iran na da wani sabon tsarin mak**ai masu linzami da zai iya ketare tsarin kare sararin samaniyar Isra’ila.
Game da batun sa ido kan shirin nukiliya, Iran ta dakatar da duk wata hulɗa da hukumar IAEA. A cewar Tehran, adalcin hukumar ya lalace gaba ɗaya. Sun kira ta wata hanya ce da Isra’ila da Amurka ke amfani da ita. Shugaban IAEA, Rafael Grossi, ya ce bama-baman Amurka sun jawo mummunar barna ga cibiyoyin nukiliya na Iran, amma Iran za ta iya farfadowa da aikin cikin watanni. Ya kara da cewa ilimin masana nukiliya na Iran ba za a iya gogewa daga kwakwalwarsu ba.
Kafafen yaɗa labarai ba su kauce ba daga wannan rikici. A cewar Washington Post, an gano muhawarar sirri tsakanin manyan jami’an Iran da ke nuna cewa harin Amurka bai yi barna k**ar yadda ake tsammani ba. Wasu kafafen Amurka ma sun fitar da bayanan sirri da ke cewa harin ya yi illa kadan ne kawai ga cibiyoyin Iran. Wadannan jayayya da kalamai masu karo da juna suna nuna yiwuwar sake buda wata sabuwar gabar fada.
Babu shakka, idan aka sake barkewar yaƙi tsakanin Iran da Isra’ila, zai zama mai muni, tashin hankali da halaka. Kowanne ɓangare yana jiran damar kawar da ɗayan gaba ɗaya. Zai haifar da asarar rayuka da lalacewar dukiya da ba a taba gani ba. Gabas ta Tsakiya za ta koma fili na yaƙi. Idan har wannan yanki da ke da rijiyoyin man fetur, matatun mai da injunan wutar lantarki ya k**a da wuta, tattalin arzikin duniya zai shiga mawuyacin hali. Rufe mashigin Strait of Hormuz, wanda zai iya faruwa idan rikicin ya ƙaru, zai shafi kusan kashi 20% na mai da duniya ke amfani da shi.
Yanzu ne lokaci mafi dacewa na dakile wannan barazana. Manyan ƙasashe na duniya na da damar shawo kan wannan rikici. Wannan ba lokacin rarrabuwar kai ba ne, ko na neman biyan bukatun ƙashin kai. Ba a k**ata a ɗauki rikicin Iran da Isra’ila a matsayin abin da bai shafe kowa ba. Idan yaƙin ya faru, zai canza tsarin duniya gaba ɗaya. Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman kwamitin tsaro (UNSC), dole ta haɗa kai ta fitar da matsaya ɗaya don ceto duniya daga mummunar illar wannan yaƙi. A stitch in time saves nine. Duniya da mazaunanta ba za su yarda da kuka na karya ba idan an bar yaƙin ya faru. Zubar da jinin marasa laifi a kowane irin salo ya ishe mu.
Hotunan da ake nunawa a talabijin da shafukan sada zumunta abin firgita ne da takaici. Dole ne kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen hana duniya komawa daji, inda mugunta da dabbanci ke zama ruwan dare. Tsarin rayuwar bil’adama yana auna ne ta yadda mutane ke guje wa kashe-kashen da rushe abinda aka gina a doron kasa.
Majalisar Ɗinkin Duniya, don Allah ku ceci bil’adama.