
21/09/2025
Ana wata ga wata a Faransa..
Ya kamata a buga wasan PSG da Marseille a yau amma an dage wasan saboda rashin kyawun yanayi
Dokokin Faransa - idan aka dage wasan a yau, dole ne a gudanar da shi kai tsaye gobe
To mene ne matsalar? Gobe ne bikin Balloon Dor a Paris
PSG ta ki yarda a buga wasan gobe
Marseille ta bukaci a gudanar da wasan kamar yadda doka ta tanada
Me yasa Marseille ta nace akan wannan kwanan wata? Domin PSG tana rashin ƴan wasan
Barcola, Neves, Doue da Dembele duk sun ji rauni!
A yanzu haka a babban birnin Faransa ana cikin tsaka mai wuya tsakanin wasan Clasico na Faransa da bikin Balloon Dor gobe.