29/05/2025
Sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bayyana cewa tana da cikakken shiri na fuskantar shari’ar batanci da gwamnatin tarayya ta shigar a kanta, amma ta dage cewa dole ne hukumomi su binciki zarge-zargen da ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
Akpoti-Uduaghan, wadda ke kasashen waje a halin yanzu bisa wasu harkokin kashin kanta, ta tabbatar da samun sammaci daga kotu, kuma ta bakin lauyoyinta ta bayyana cewa za ta amsa kiran kotu idan aka tsara ranar shari’ar
“Ta na da cikakken kuduri wajen bin doka kuma za ta kare kanta a gaban kotu,” in ji lauyanta, Uju Nwoduwu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. “Amma dai adalci bai k**ata ya zama na bangare guda ba. ’Yan sanda su binciki dukkan korafe-korafen da aka shigar—musamman wadanda s**a shafi manyan jami’ai irin su Akpabio da Bello.”
Tawagar lauyoyin sanatar sun nuna damuwa kan abin da s**a kira "biyayya ga masu iko", inda s**a ce sun gabatar da takwas zuwa goma sha biyu na korafe-korafe tsakanin watan Maris da Mayu 2025, wadanda s**a hada da zarge-zargen cin mutunci ta intanet, batanci, barazana ga rayuwa, cin zarafin jima’i da ma yunkurin kisa—amma dukkansu ba su samu kulawa daga ’yan sanda ko hukumomin tsaro ba.
A bangare guda kuma, sun ce korafe-korafen da Akpabio da Bello s**a shigar kan sanatar an dauka da gaggawa, kuma hakan ya kai ga gurfanar da ita a gaban kotu.
Lauyoyin sun bayyana hakan a matsayin “bambancin adalci da ke kara jefa shakku ga tsarin shari’a”, inda s**a bukaci Sufeto Janar na ’Yan Sanda da Attoni Janar na Tarayya su tabbatar da bin doka daidai ba tare da nuna bambanci ba.
Gwamnatin tarayya ta shigar da karar ne a ranar 16 ga Mayu bisa sashe na 391 na dokar Penal Code, tana zargin Natasha da furta kalaman batanci a wata hira da aka yi da ita a talabijin.
Zargin da ke kunshe a karkashin sashe na 392 na hukuncin dokar ya ambaci Akpabio da Bello a matsayin shaidu na bangaren masu kara.
Ana zargin Akpoti-Uduaghan da cewa ta yi ikirarin cewa Akpabio da Bello sun hada baki don kashe ta—zargi da ta danganta da dakatarwar da aka yi mata daga majalisa sak**akon sabani da aka samu kan wurin zama.
Haka kuma, ta zargi Akpabio da cin zarafin jima’i kuma ta riga ta shigar da korafi ga hukumomi domin a gudanar da cikakken bincike.
“Ina sa ran jami’an tsaro za su gudanar da aiki da adalci da daidaito,” in ji lauyoyinta. “Adalci dole ne ya tabbata, kuma mutane su ga an yi shi—ba tare da la’akari da mukami ko tasirin siyasa ba.”
Yayin da s**a gode wa jama’a bisa goyon bayan da suke baiwa sanatar, lauyoyin sun sake jaddada bukatarta ta cewa lallai ne a binciki dukkan korafe-korafen da ke gabanta da irin gaggawar da aka nuna wajen shigar da kara a kanta.