20/10/2019
RAHOTON MUSAMMAN: Mun Zabi Gwamnati ta Kone Mana Jari Karkaf -Kungiyar Bola-bola
Daga Wakilinmu
Dubban 'yan Kungiyar Bola-bola, Metal Scrab and Craftmanship da ke Abuja, masu aikin sarrafa tsoffin karafuna, robobi da irin su alminiyan, ba za su taba mantawa da ranar Asabar, 5 Ga Oktoba, 2019 ba.
A wannan rana ce gangamin jami'an tsaro na JTF daga Hukumar Tsaftace Abuja, s**a yi wa kasuwar wadda ke Jabi ko kuma masana'antar dirar dakarun yaki, su ka banka mata wuta, ta kone kurmus.
Ba karamar asara daruruwan masu harkoki su ka yi a wannan kasuwa da za a iya raina-kama-ka-ga-gayya ba.
Dalili, wuri ne da ake saye, sayarwa da kuma sarrafa kayan karambosuwa, a takaice dai jari-bola kenan. Amma dubban jama'ar da ke harkar da kuma irin dimbin dukiyar da aka yi asara, ta na da yawan gaske.
Makonni uku kafin a kone kasuwar kurmus, jami'an tsaron sun je da katafita s**a ruguje dukkan wurin kakaf. Amma ba a kone musu wurin ba.
Sai dai kamar yadda wakilin mu ya ji da bakin sa daga wasu da s**a yi dimbin asara a wurin, sun tabbatar da cewa an yi musu satar kayayyaki a wurin, kuma sun zargi ma'aikatan rusau din.
Musa Amadu, wanda aka fi sani da suna Dogo, ya shaida wa wakikin mu cewa ya dibga asara ta kudi ba kadara ba, naira milyan 1,600,00, kuma sace kudin aka yi.
"Sun zo su na harbe-harbe, har da dukan mu a ranar. S**a hana kowa shiga. Sannan s**a sa katafila s**a rika rushe mana wuri. Ba su bar mu mun shiga ba. Bayan sun tafi na shiga na samu an kwashe min kudi na."
Ya ci gaba da cewa akwai jami'an da s**a je da jaka, s**a rika kwasar wayoyin mutane su na zubawa jakar su.
"Sau hudu kenan ana kawo mana hari ana rushe mu tun daga hawan Shugaba Muhammadu Buhari a 2015. Amma wannan na baya da s**a kona mana dukiya, ya fi muni matuka. Saboda sun zo da katafila ta masu yawan gaske.
GWAMNATIN APC TA WULAKANTA MU -Salisu Adamu
Mataimakin Shugaban Kungiyar na Jabi da ke kasuwar kayan karambosuwar da aka kona, Salisu Adamu, ya shaida cewa sun yi amfani da karfin su da dukiyar su da kuri'in su, sun zabi Gwamnatin APC har a 2019. Amma ta kwance musu zani a kasuwa. Ta talauta dubban masu harkar jari-bola.
"Kafin zaben 2019, har gagarimin taro 'yan kungiyar mu ka shirya 'Parade Ground', wanda dubban mu mu ka je domin nuna goyon baya ga Buhari da APC. Haka da zabe ya zo duk mu ka je mu ka zabi APC.
" Amma tun ba a je ko'ina ba, an rushe mana wurin sana'a, an kone mana jari na milyoyin nairori. Kuma gwamnatin da mu ka sha wahalar zabe. Shin yaya ta ke son dubban matasan da ke wannan harkokin su yi ne a rayuwar su?"
Shi kuwa daga daga cikin mambobi, kuma iyayen kungiyar, Alhaji Babangida Bature, ya shaida wa wakilin mu cewa, ya kamata Gwamnati ta sani cewa ta haddasa wa matasa dubbai asarar rashin aikin yi.
"Wadannan matasa da aka kona wa kaya, a karkashin kungiya su ke. Kuma ta na da rajista da CAC. Kungiyar nan ta na bada hadin kai ga jami'an tsaro. Akwai jarin sama da milayan 300 a cikin harkar nan a Abuja da sauran jihohi.
"Duk wani kokarin tsaftace harkar ana yi, kuma hukuma ta sani. Yaran nan su na taimakawa wajen tsaftace Abuja da kewaye.
"Na san a ko'ina akwai batagari da na kwarai. To kungiya na kokarin ta, kuma ba a sayen kayan sata. Ya kamata gwamnati ta sake tunanin yadda za ta gyara wannan harka, ba wai a raba dubban jama'a da sana'ar su ba.
Binciken da wakilin mu ya yi, ya gano cewa akwai masana'antun sarrafa karafuna da yin robobi wadanda ke sayen kayan karafa da tsoffin robobi a wurin su.
Akwai Rida National Plastic, Lagos, Hart Plastic, Kano, Songhai Plastic, Ogun, Saz EPZ, Kano, BBY Plastic, Kano da kuma Rumbu Sacks, Kano.
Sakataren kungiyar, Malam Misbahu, ya shaida wa wakilin mu cewa akwai ka'idojin shiga kungiyar da s**a hada da rajista, wanda zai tsaya wa sabon mamba, hoto, fam, sannan sai ID card, bayan an gamsu da halin sa. Ya ce su na da mambobi a Abuja za su kai 10,000.
"Amma idan aka hada da na Kananan Hukumomin Abuja shida, mun fi 200,000." Inji Misbahu.
Shi kuwa Shugaban Kungiyar, Auwalu Abdullahi, ya shaida wa wakilin mu cewa kungiyar su mai hedikwata a Jabi, kusa da ofishin Jaridar THISDAY a Abuja, sananne ne a kasar nan, domin cikin iyayen su ma har da Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari.
Ya ce bai kamata gwamnatin da ta yi wa al'umma alkawari samar wa milyoyin matasa aiki, kuma ta koma ta na ruguza sana'o'in da dubban matasa s**a kirkirar wa kan su da kan su ba.
Ya yi kira da a ja matasa a jika, domin rashin aikin yi na kara yawaitar kangararrun yara a cikin al'umma.
Ko ma dai me kenan, a ranar 10 Ga Oktoba, wannan kungiya ta rubuta takardar korafi zuwa ofishin Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Dama kuma ko a can baya kungiyar ta sha yin taruka da jami'an tsaro, har ma da shi ministan kan sa sun yi.
Kokarin jin ta bakin sauran wadanda abin ya shafa bai yiwu ba. Amma za mu kawo mu ku na su ba'asin nan gaba.
Shin ya gwamnati za ta yi da dubban matasan da s**a rasa sana'a, abinci da sauran kudin yin bukatu na dole, sanadiyyar rushe 'yan Bola-Bola da ke Jabi?