19/10/2025
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Ta Soki Shirye-shiryen Zanga-zangar Neman Sakin Nnamdi Kanu
Kungiyar Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ta bayyana adawa da s**a mai tsanani kan shirin gudanar da zanga-zangar neman a saki shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu.
CNG ta ce wannan yunkuri da wasu shugabannin siyasa da na al’ada na kabilar Igbo, da masu kiran kansu ‘yan gwagwarmaya k**ar Omoyele Sowore, ke jagoranta tare da wasu ‘yan Arewa marasa kishin ƙasa wani makirci ne na yi wa ƙasa karan tsaye da barazana ga zaman lafiya da doka.
Kungiyar ta bayyana cewa Nnamdi Kanu da IPOB sun haifar da mutuwar fiye da mutane 1,200 ciki har da jami’an tsaro sama da 400, sun ƙone ofisoshin ‘yan sanda fiye da 100, kuma sun jawo asarar dukiya da ta haura ₦450 biliyan a Kudu maso Gabas.
CNG ta tunatar da cewa tun daga 2016 Kanu ya kasance mai yada ƙiyayya, tashin hankali da rarrabuwar kai ta hanyar IPOB da rundunarsa ta ESN, inda aka kashe ‘yan Arewa da dama, aka lalata kasuwanci, tare da hana zaman lafiya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta tabbatar da shari’ar Kanu ta tafi yadda doka ta tanada ba tare da matsin lamba na siyasa ba, tare da bukatar jami’an tsaro su hana duk wata zanga-zangar da zata kawo tashin hankali.
CNG ta gargadi ‘yan siyasa da masu daukar nauyin zanga-zangar da cewa za a bincike su, tare da kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya bari a yi masa barazana wajen yin doka bisa ra’ayi ko jin kai.
A ƙarshe, CNG ta jaddada cewa sakin Nnamdi Kanu ba zai kawo zaman lafiya ba, sai dai ya kara dagula ƙasa da karya tsarin shari’a. Ƙasar da ba ta mutunta doka ba, ba za ta samu zaman lafiya ba.
Sa hannu:
Comrade Jamilu Aliyu Charanchi
Koodineta Na Ƙasa, CNG
Abuja, Najeriya