28/05/2025
Ɗaukar doka a hannu da matasan RANO s**ayi na kashe DPO daidai yake da abinda mutanen garin UROMI s**ayi ma mutanen arewa.
Banbancin mutum da dabba shine HANKALI, Idan har mutane baza suyi amfani da hankalin da Alllah yabasu wajen tantance abinda yake daidai da kuma akasin hakan ba. Tabbas yadace a kira masu ɗaukar doka a hannun da sunan DABBOBI!
Idan har bamu martaba Jami'an tsaron da suke fafutukar kare rayukan al'umma, dukiya da kuma walwala na yau da kullum ba, BAMU chanchanci amsa sunan ƴan kishin ƘASA ba!
Naji takaici sosai lokacin dana kalli video yadda fusatattun matasan garin RANO suke dukan marigayi DPO cikin rashin tausayi da ƙin girmama hukumar ƳAN SANDA, abin takaici ne sosai kaga wanda kake fafutukar bashi kariya amma shi yana ƙoƙarin ganin bayanka! A duk lokacin da wani ya zalunceka babu inda kake tunanin zuwa kai ƙara fa ce ofishin hukumar ƴan sanda domin a bimaka haƙƙin ka! Ko wanne irin tarkace mutane s**a kwaso babu inda suke zuwa sai wajen ƴan sanda domin shigar da ƙorafi, amma a hakan wasu suke aibanta aikin ƴan sanda wasu ma cin zarafi sukeyi ga hukumar ƴan sanda, Duk da dai a kowanne gida ana samun ɓata gari amma inada yaƙinin mutanen kirki sunfi yawa cikin hukumar ƴan sanda.
Ina Kira ga hukumar ƴan sanda da gwamnatin jihar Kano dasu tabbatar da doka tayi aiki akan mutanen dasu ka kashe mai girma DPO domin hakan yazama izina ga masu ƙoƙarin sake ɗaukar doka a hannu.
Abba Hikima
Fauziyya D. Sulaiman
Hauwa Halliru Gwangwazo