Kamalancy

Kamalancy K**alancy sabon shafin jarida ne da aka kirkira dan kokarin kawo maku sabbin kayatat'tun labaran Dun

Shekaru Biyu A Gwamnatin Da Ta Dawo Da Martabar Jihar  KanoA lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau karagar mulki a r...
04/06/2025

Shekaru Biyu A Gwamnatin Da Ta Dawo Da Martabar Jihar Kano

A lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023 al’ummar Kano sun fara ganin sauyi na gaske. Sauyin da ya tabbatar da aiki, tsare-tsare, da kula da lafiyar al’umma da tattalin arziki wannan ba mulki ba ne na alkawari kawai, wannan mulki ne mai cike da aiki da cika alkawari.

A cikin shekaru biyu kacal, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa mulki nagari ba a magana ba ne, aiki ne da kishin al'umma

A bangaren noma da ban ruwa, sama da hectare dubu an samar da su domin noman rani, tare da gine-ginen dam-dam a kananan hukumomi fiye da goma sha biyu.

A fannin lafiya, an cire dubban masu rijista na bogi, an dauki matakan inganta kulawa da marasa lafiya, tare da shigar da dubban talakawa cikin tsarin lafiya kyauta.

Gwamnatin Abba ta kawo karshen matsalar rashin magunguna a asibitoci, ta kafa cibiyoyi na musamman da samar da injinan iskar oxygene masu amfani da hasken rana.

An ba da kulawa ta musamman ga yara da mata masu fama da cututtuka ta hanyar shirin ABBACARE, tare da tallafawa masu sikila da marasa galihu.

Tsarin rajista da kididdiga na zamani (EMR) ya kara inganta tsarin lafiya da sarrafa bayanai a asibitoci fiye da goma.

Gaskiya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf yana aiki tukuru, yana gina jihar Kano bisa gaskiya, adalci da amana. Wannan gwamnatin ba ta yi alkawarin da ba ta cika ba cikin shekara biyu da fara mulkin jihar Kano!

ABAISWORKING
📅 29th May, 2025
Wanda ya shuka nagarta, shi zai girbi tagomashi

AJAM Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Nasarorin Da Ta Cimma Wajen Dawo da Zaman Lafiya a ArewaGamayyar Kungiyar Ayyukan ...
01/06/2025

AJAM Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Nasarorin Da Ta Cimma Wajen Dawo da Zaman Lafiya a Arewa

Gamayyar Kungiyar Ayyukan Arewa (AJAM) ta jinjina wa Gwamnatin Tarayya bisa manyan nasarori da ta samu wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa, wanda da can ya kasance cike da matsalolin ta’addanci da miyagun laifuka.

Kungiyar ta bayyana musamman rawar da Ma'aikatar Tsaro ke takawa wajen aiwatar da manyan ayyukan tsaro masu amfani da fasahar zamani a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya.

A cikin wata sanarwa da mai jagorantar kungiyar, Lauretta Bako ta fitar a ranar Alhamis, AJAM ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro a yankin, wanda hakan ya biyo bayan dabarun rundunonin tsaro da gwamnatin ke aiwatarwa.

"A yau muna rayuwa a wani sabon yanayi na tsaro fiye da da, inda aka kore Boko Haram zuwa matsugunan duhu, yayin da shugabannin masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga s**a hallaka ko s**a tsere."

"Nasarorin da aka samu wajen kawar da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da kuma sarkakiyar hanyoyin aikata laifi, tare da farfado da tattalin arzikin yankuna, ya nuna ingancin wannan tsari."

A cewar AJAM, daya daga cikin ginshikan wannan nasara shine Operation FANSAR YAMMA, wanda ya samu nasarori da dama, ciki har da hallaka sanannen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Dogo Isah, tare da wasu ‘yan ta’adda 44 a jihar Zamfara.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kashe fitattun masu aikata laifi ciki har da masu sayar da mak**ai da shugabannin ‘yan bindiga ya tarwatsa manyan hanyoyin aikata laifi, tare da isar da sako ga sauran masu laifi cewa gwamnati ba za ta yarda da rashin tsaro ba.”

Tasirin wadannan matakan tsaro ya wuce kidayar alkaluma kawai; yana da tasiri kai tsaye ga rayuwar yau da kullum ta ‘yan kasa. Hanyoyi k**ar hanyar Kaduna-Abuja, wanda da can aka fi jin tsoro, yanzu sun fi aminci ga matafiya, hakan kuma yana taimakawa wajen kasuwanci da zirga-zirga.

Kasuwanni a wurare irin su Giwa, Birnin Gwari da Jibia suna samun sabuwar rayuwa, inda shugabannin al’umma da jama’a ke tabbatar da ingancin tsaro. Farfadowar harkokin kasuwanci na da nasaba kai tsaye da nasarorin da sojoji s**a samu tare da samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci.

Gina Brigade na National Mission Force a Samaru Kataf shima ya taka rawa wajen warware matsalolin tsaro a Kudu ta Kudancin Kaduna, wanda ya haifar da ingantattun yanayin zamantakewa da tattalin arziki. A cikin watanni ukun farko na shekarar 2025 kadai, an hallaka ‘yan ta’adda 122 kuma an k**a fiye da 1,000 daga cikin masu laifi.

A matsayinmu na Arewa Joint Action Movement, muna tare da kokarin da Ma’aikatar Tsaro ke yi wajen kare al’ummominmu da dawo da fata a zukatan jama’a. Muna fahimtar cewa har yanzu akwai kalubale, amma nasarorin da aka samu sun haskaka mana hanya. Zamu ci gaba da goyon bayan manufofi da matakan da za su kawo zaman lafiya, tsaro da cigaba mai dorewa a Arewarmu.

Peter Obi Ya Karyata Jita-Jitar Zama Mataimakin Atiku A Zaben 2027 – Inji Obidient MovementDaga Comr Haidar H Hasheem Ob...
19/05/2025

Peter Obi Ya Karyata Jita-Jitar Zama Mataimakin Atiku A Zaben 2027 – Inji Obidient Movement

Daga Comr Haidar H Hasheem

Obidient Movement ta bayyana cewa rahoton da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a zaben 2023 Mr. Peter Obi ya amince ya zama mataimakin Alhaji Atiku Abubakar a wani sabon hadin gwiwar siyasa da ake kokarin kafa wa gabanin zaben 2027, karya ne kuma babu gaskiya a cikin rahotan.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Nana Kazaure, Daraktar Sadarwa da Tsare-Tsare ta kungiyar, ta fitar a ranar 19 ga Mayu, 2025, inda ta bayyana cewa rahoton ya kasance kirkirar wasu marubuta ne kawai, kuma hakan yana iya janyo rudani da kuskuren fahimta a tsakanin jama'a.

Ta ce ko da yake ana ci gaba da gudanar da tattaunawa cikin lumana da wasu manyan ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki don samar da hadakar da za ta ceto Najeriya, babu wata tantama cewa Mr. Obi bai amince da mukamin mataimaki ba, kuma babu wata yarjejeniya da ta shafi hakan.

Sanarwar ta bayyana cewa manufar Mr. Obi da Obidient Movement ita ce samar da cikakken hadin kai don yaki da mulkin rashin nagarta, cin hanci da rashawa, yunwa, talauci, matsalar kiwon lafiya, da karancin ilimi ga yara ba siyasar karbar mukami kawai ba.

Kungiyar ta sake jaddada cewa Mr. Obi har yanzu na cikin jam’iyyar Labour Party, kuma idan zai sauya sheka ko jam’iyya a nan gaba, zai bayyana hakan da kansa.

Daga karshe, Obidient Movement ta bukaci 'yan Najeriya da kafafen yada labarai da su kauce wa yada jita-jita da rahotannin da ka iya tada tarzoma saboda rashin tushe, su maida hankali wajen taimakawa tare da gina Najeriya mai inganci da adalci.

Ranar: 19/05/2025
Sa hannu: Nana Kazaure, Daraktar Sadarwa da Tsare-Tsare, Obidient Movement

Ministan Tsaron Nigeria, Mohammed Badaru Abubakar, Ya Karɓi Baƙuncin Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Harkokin Jinƙai...
30/04/2025

Ministan Tsaron Nigeria, Mohammed Badaru Abubakar, Ya Karɓi Baƙuncin Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya Kan Harkokin Jinƙai

A ranar Talata, 29 ga Afrilu 2025, mai girma Ministan Tsaro na Ƙasa, H.E. Mohammed Badaru Abubakar, CON, mni, ya karɓi baƙuncin Mr. Mohamed Malick Fall, wanda shi ne Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya kuma mai kula da harkokin jinƙai.

Tattaunawar wanda aka gudanar a ofishin Ministan dake Ship House, Abuja, ta mayar da hankali ne kan yadda Najeriya za ta ƙara tallafawa ayyukan jinƙai da Majalisar Ɗinkin Duniya ke gudanarwa a ƙasar.

Me za ku ce kan ajiye mukamin da Dr Hakeem Baba Ahmed yayi?Dr Hakeem Baba Ahmed, shine tsohon mai magana da yawun kungiy...
04/04/2025

Me za ku ce kan ajiye mukamin da Dr Hakeem Baba Ahmed yayi?

Dr Hakeem Baba Ahmed, shine tsohon mai magana da yawun kungiyar Dattawan Arewa, shine za kuji kullum yana kalubalantar Gwamnati a duk inda tayi kuskure a gidajen Rediyo da Television da kafofin sada zumunta.

Tun ranar da Tinubu ya bashi mukamin mai bashi shawara ya turashi Ofis din Kashim aka daina jin duriyarshi, ya daina cewa komai akan sha'anin kasar.

Yasha caccaka da shagube iri-iri a wurin al-umma, yau da safe kwatsam sai ga sanarwar ya ajiye mukaminshi a jaridar Daily Trust.

Ministan Tsaron Najeriya Ya Kai Ziyara Depot Na Sojojin Najeriya Dake Garin ZariyaMai Girma Ministan Tsaro, Mohammed Bad...
25/03/2025

Ministan Tsaron Najeriya Ya Kai Ziyara Depot Na Sojojin Najeriya Dake Garin Zariya

Mai Girma Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar CON, mni, ya kai ziyarar tantancewa ta yini guda a Depot na Rundunar Sojojin Najeriya da ke Zariya a yau, Talata, 25 ga Maris, 2025.

A yayin ziyarar, Minista da tawagarsa sun samu cikakken bayani daga Kwamandan Depot, Manjo Janar AB Mohammed, kan tsarin aiki, gudanar da ayyuka, da horon da ake bai wa sojoji a cibiyar.

Cikin tawagar Ministan akwai Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Tsaro, Ambasada Gabriel Tanimu Adudu; Mai Ba da Shawara Kan Fasaha, Janar AT Jibril (Rtd); da Babban Jami’in Ma’aikata, Birgediya Janar AA Garba.

Mati Ali
PA Media & Publicity to the Hon Minister of Defense.

Tinubu Ya Ƙuduri Aniyar Inganta Tsaro Tare Da Bayar Da Horo Na Musamman Ga Sojojin Najeriya ~ Badaru Ministan Tsaro, Moh...
24/03/2025

Tinubu Ya Ƙuduri Aniyar Inganta Tsaro Tare Da Bayar Da Horo Na Musamman Ga Sojojin Najeriya ~ Badaru

Ministan Tsaro, Mohammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na kokarin samar da kayayyakin yaki na zamani, don inganta jin dadin jami’an tsaro, da basu horo na musamman domin inganta tsaro a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da horon Special Operations Force a Jaji, Kaduna, wanda za'a horas da sojoji dabarun yaki na zamani, yakar ta’addanci, leken asiri, da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Shirin zai fara da dakaru 800 daga cikin jimillar 2,400 da ake sa ran horaswa, kuma gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar samar da mak**ai, na’urorin leken asiri, da horas da sojoji kan sabbin dabaru.

Badaru ya jaddada cewa wannan horo zai karfafa tsaro, kare ‘yancin kasa, da kuma tabbatar da zaman lafiya a Najeriya da makwabtanta. Ya bukaci dakarun da ake horaswa su jajirce, domin su zama garkuwa ga kasa.

Mati Ali
PA Media & Publicity to the Hon. Minister

Sabuwar Jam'iyyar Maja Ta Su EL-RUFAI DA ATIKU Yaudara Ce Ba Talakawa Ne A Gabansu Ba... Gamayya ce ta masu neman muƙami...
22/03/2025

Sabuwar Jam'iyyar Maja Ta Su EL-RUFAI DA ATIKU Yaudara Ce Ba Talakawa Ne A Gabansu Ba
... Gamayya ce ta masu neman muƙami da mulki da neman takara, ba al'umma ko talakawa ne a gabansu ba.

Ya ku al’ummar Arewa, ku dubi halin da ake ciki ku tambayi kanku, shin har yanzu za mu ci gaba da bari wasu ‘yan siyasa su rika amfani da mu don biyan bukatunsu? Yanzu da aka saka dokar ta ɓaci a Jihar Rivers, sai gashi Nasiru El-Rufai da Atiku Abubakar sun hada kansu da wasu domin su caccaki gwamnatin Tinubu.

Ina s**a kasance lokacin da ake kashe al’ummar mu a Kaduna, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto? A lokacin da aka yi ta satar mutane, garkuwa da su, da hallaka iyayenmu da ‘ya’yanmu, ina ku ke? El-Rufai, kana gwamnan Kaduna, lokacin da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a jiharka, ba ka taba yin taron manema labarai domin nuna damuwarka ba. Atiku, lokacin da kake cikin gwamnati a baya, ba ka taba kokarin kawo mafita ga Arewa ba.

Amma yau da aka cire gwamnan Rivers, sai gashi kun fito kuna ihun adalci! Shin, lokacin da kuka ke mulki Atiku yana mataimakin shugaban kasa, ba kun cire gwamnonin jihohi k**ar Bayelsa da Plateau ba? El-Rufai da Atiku, lokacin da kuka ke mulki a zamanin Obasanjo, har gwamnonin jihohi uku kuka tsige! To me yasa a lokacin hakan ya zama daidai, amma yanzu da Tinubu ya yi, sai ku ce rashin adalci ne? To menene banbancinku da shi Tinubu ɗin, ko dan shi daga Kudancin Najeriya yake, ku kuma daga Arewa?

Shin me kuka yi lokacin da aka cire tallafin man fetur? Me yasa baku taba yin magana ba lokacin da aka jefa talaka a cikin wahala? Domin kun san cewa baku ne za ku sha wahalar ba, shiyasa kuka yi shiru. Amma yanzu da bukatarku ta taso, sai gashi kun fara taron manema labarai da shirye-shiryen kafa wata jam’iyyar maja.

Atiku da El-Rufai, kuna son sake hada wata jam’iyyar maja domin me? Ba ku ne kuka kafa APC ba? Ba ku ne kuka ce ita ce mafita ga Najeriya ba? Yanzu da ku ka gaza cimma burin ku, sai ku dawo kuna kokarin yaudarar mutane da wata sabuwar jam’iyyar?

Ya ku ‘yan Arewa, muna gane wasan waɗannan mutanen, ka da mu sake bari su yi amfani da mu don biyan bukatunsu karshe su watsar damu. Mun koyi darasi daga baya, kuma wannan karon, ba za mu bari su yi amfani da mu ba!

Haɗin Gwiwa Don Cigaban Kasa..... Mai Girma Ministan Tsaro ya gana da Ministan Kudi domin inganta hadin kai tsakanin ma’...
21/03/2025

Haɗin Gwiwa Don Cigaban Kasa
..... Mai Girma Ministan Tsaro ya gana da Ministan Kudi domin inganta hadin kai tsakanin ma’aikatun gwamnati don inganta tattalin arzikin kasa da tsaro

Mai Girma Ministan Tsaro, H.E. Mohammed Badaru Abubakar, CON, mni, ya kai ziyarar girmamawa ga Mai Girma Ministan Kudi, Mista Adebayo Olawale Edun, a ofishinsa da ke Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, Abuja, a yau Juma’a, 21 ga Maris, 2025. Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa hadin gwiwar ma’aikatu don ci gaban kasa.

Ba Zamu Lamunci Bita Da Ƙullin Da Hukumar EFCC Ta Ke Yiwa Gwamnan Bauchi Ba ~ BATA..... Fitacciyar Kungiyar Nan BATA Ta ...
21/03/2025

Ba Zamu Lamunci Bita Da Ƙullin Da Hukumar EFCC Ta Ke Yiwa Gwamnan Bauchi Ba ~ BATA
..... Fitacciyar Kungiyar Nan BATA Ta Caccaki Hukumar EFCC Kan Binciken Zargin Badakala Na Kimanin Biliyan 70 A Gwamnatin Jihar Bauchi

Kungiyar Bauchi Accountability and Truth Awareness Front (BATA) ta soki hukumar EFCC kan binciken da take yi a kan wasu jami’an gwamnatin Bauchi, tana zarginta da amfani da binciken a matsayin wata makarkashiya ta siyasa.

K**a Alhaji Sirajo Mohammed Jaja, Babban Akanta na Jihar Bauchi, ya haifar da cece-kuce, inda BATA ta bayyana binciken zargin almundahanar Naira biliyan 70 a matsayin yunkurin da aka shirya don rage darajar gwamnatin Gwamna Bala Mohammed.

“Wannan ba maganar gaskiya ba ce, siyasa ake yi,” in ji Lawal Sani Ningi, Shugaban BATA. Kungiyar ta zargi EFCC da tsara wannan bincike a daidai lokacin da ake fuskantar manyan batutuwan siyasa a jihar, abin da ke kawo shakku kan sahihancin binciken.

Gwamna Bala Mohammed na Cikin Kaka-Nika-Yi

BATA ta nuna damuwa kan yadda EFCC ta ke kokarin danganta binciken da Gwamna Bala Mohammed. Kungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin wata dabara da za ta kau da hankalin jama’a daga ci gaban da gwamnan ke samu a bangaren mulki, gina abubuwan more rayuwa da jin dadin al’umma.

“Gwamnan ya kasance mai kishin jama’a, kuma wadannan zarge-zarge marasa tushe na kokarin hana mutane ganin nasarorinsa,” in ji Ningi.

Kungiyar ta jaddada cewa, yaki da cin hanci da rashawa dole ne a gudanar da shi bisa adalci da gaskiya. Ta zargi EFCC da kasa gabatar da kwakkwaran shaidar da ke tabbatar da zargin da take yi, tana mai cewa binciken ya dogara ne kacokan kan zato da jita-jita.

Kira Ga Adalci da Farkar da Jama’a

BATA ta bukaci EFCC da ta yi aiki bisa ka’idojin adalci da gaskiya, tana rokon hukumar da ta sake duba hanyoyin da take bi. Kungiyar ta kuma yi kira ga al’ummar Bauchi da su kasance masu lura tare da gujewa yaudarar jita-jita.

“Mutanen Bauchi sun cancanci shugabanni da za a auna su bisa ayyukansu na jin dadin al’umma, ba tare da tsoma siyasa a lamarin su ba,” in ji kungiyar.

BATA ta jaddada goyon bayanta ga Gwamna Bala Mohammed da sauran jami’an jihar, tana mai alkawarin ci gaba da fafutukar ganin an samu gaskiya da adalci a tafiyar da shugabanci.

Wannan cece-kuce na kara tayar da muhawara kan rawar da siyasa ke takawa a yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, inda da dama ke tambayar ko ana yin adalci ko kuma ana amfani da wannan yaki don biyan bukatun wasu ’yan siyasa.

Ka Nesanta Kanka Da Rikicin Siyasar Wike ~ Gargadin CNG Ga Tinubu Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta bukaci Shugaba Bola...
19/03/2025

Ka Nesanta Kanka Da Rikicin Siyasar Wike ~ Gargadin CNG Ga Tinubu

Gamayyar Kungiyoyin Arewa (CNG) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da cewa rikicin siyasa da ke tattare da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, bai shafi tafiyar da mulkinsa ba.

Wannan kiran ya biyo bayan dakatar da Gwamnan Jihar Ribas da mataimakinsa da Shugaba Tinubu ya yi a daren Litinin.

A cikin wata sanarwa da Shugaban CNG na Ƙasa, Jamilu Aliyu Charanchi, ya sanyawa hannu, kungiyar ta bayyana cewa dabarun siyasar Wike ba su wakiltar muradin al’ummar Jihar Ribas ko na yankin Niger Delta gaba ɗaya ba, illa son zuciya da rashin son zaman lafiya.

Muna kira ga Shugaba Tinubu da ya fahimci cewa ayyukan Wike sun fi karkata ne ga burin kansa fiye da muradun jama’a.

Yana da matuƙar muhimmanci a tabbatar da bin ƙa’idojin dimokuradiyya da doka, maimakon yin biyayya ga ɗan siyasar da ke neman moriyar kansa,” in ji Charanchi.

CNG ta bayyana matsalar da Wike ke jefa siyasar Najeriya a ciki a matsayin babbar gwaji ga jagorancin Tinubu. Kungiyar ta ce hanyar da za a bi don rage tasirin Wike ita ce samar da haɗin kai da aiki tare domin gina kyakkyawar makoma.

Duniya na sa ido don ganin irin matakan da Shugaba Tinubu zai ɗauka wajen tabbatar da shugabanci nagari da kuma cika burin ‘yan Najeriya,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki, ciki har da ƙungiyoyin fararen hula, ‘yan siyasa da jama’a, da su fifita zaman lafiya da dimokuradiyya a maimakon tada zaune tsaye.

Wannan rikicin ya zama gargaɗi ga kowa da kowa cewa ya k**ata mu fifita tattaunawa da fahimtar juna a maimakon rikici da rarrabuwar kai,” CNG ta ƙara da cewa. Ta kuma gargaɗi Shugaba Tinubu da ya yi hattara kada ya bari alaƙarsa da Wike ta haifar da barazana ga zaman lafiyar ƙasa.

Ba za mu yarda burin mutum guda ya jefa ƙasar nan cikin rudani ba. Muna shirye mu goyi bayan duk wani mataki da zai inganta zaman lafiya da jin daɗin ‘yan Najeriya,” in ji sanarwar.

CNG ta jaddada cewa rikicin da ke faruwa na iya yin illa ga tsaron ƙasa da tattalin arziƙi.

Ayyukan mutum guda bai k**ata su zama abin da zai rinjayi alkiblar ƙasa gaba ɗaya ko su hana aiwatar da manufofin da za su amfanar da jama’a,” CNG ta jaddada.

Sanarwar ta kuma yi nuni da rawar da Wike ya taka a gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, inda ta zargi dabarunsa na siyasa da haddasa matsalolin da s**a kai ga faduwar Jonathan a zaɓe.

Shugaba Tinubu dole ne ya kasance a cikin shiri, musamman ganin yadda al’umma ke sanya ido kan matakan da zai ɗauka dangane da halin da ake ciki a Jihar Ribas,” in ji kungiyar.

NUF Ta Yi Allah-Wadai Da Ƙoƙarin El-Rufai Na Sake Yaudarar Al'ummar Arewa Bayan Ya Yi Watsi Da SuKungiyar Hadin Kan Arew...
18/03/2025

NUF Ta Yi Allah-Wadai Da Ƙoƙarin El-Rufai Na Sake Yaudarar Al'ummar Arewa Bayan Ya Yi Watsi Da Su

Kungiyar Hadin Kan Arewa (NUF) ta nuna rashin amincewarta da ƙoƙarin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yake yi na nuna kansa a matsayin mai ceton Arewa bayan watsi da al'ummar Arewa da yayi tare da cin mutuncin shugabannin Arewar.

Shugaban kungiyar, Comrade Yusuf Umar, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa wannan sanarwa ta zama kira ga duk shugabannin Arewa da al’ummarta da su yi la’akari da lokacin mulkin El-Rufai da kuma dabi’un da ya yi watsi da su yayin da yake amfani da mulki ba daidai ba ga al'umma.

Ya ƙara da cewa, yadda El-Rufai ya nuna rashin sanin darajar wasu manyan shugabanni a lokacin da s**a rasu ko kuma s**a fuskanci koma baya a siyasarsu, k**ar marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua da kuma Shugaba Goodluck Jonathan, ya nuna rashin tausayi da kuma rashin mutuntawa, wannan kuwa ya saba da kyawawan dabi’un Arewa.

Shugaban NUF ya bayyana cewa, "A kokarinsa na neman amincewa daga jama’a, El-Rufai yana ƙoƙarin sauya labarinsa, yana neman yardar shugabanni da mutanen da ya taɓa wulakantawa. Amma bai k**ata a manta da irin rainin da ya yi wa gadojin shugabancin Arewa ba, musamman irin mutanen da s**a sadaukar da kansu don hadin kai da cigaban Najeriya, k**ar Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, da sauran manyan shugabanni ba.”

Ya kara da cewa, El-Rufai ya fi fifita burin kansa fiye da girmama ƙwaƙƙwaran tarihihin shugabannin Arewa. Zantukansa marasa la’akari da irin gwagwarmayar waɗancan shugabanni sun nuna cewa yana da matsala ta fifita bukatarsa akan muradun jama’a.

Kungiyar NUF ta yi gargadi cewa shugabanci na gaskiya yana cikin tawali’u da girmama al’adu da tarihin jama’a. Salon mulkin danniya da El-Rufai ya yi amfani da shi, wanda ya hana masu s**ar sa damar bayyana ra’ayinsu, ya haifar da durkushewar farin jininsa a siyasa. Yunkurinsa na komawa a matsayin mai ceton Arewa ya zama wani abu da bai dace ba kuma cin zarafi ne ga mutuncin al’ummar yankin.

A karshe, kungiyar NUF ta bukaci dukkan shugabannin Arewa su fifita muradun jama’a a kan son zuciya, su girmama tarihihin shugabannin da s**a gabata, kuma su jajirce wajen ganin cewa yankin Arewa ya ci gaba da kasancewa a kan tafarkin haɗin kai, mutuntawa, da sanin ya k**ata.

NUF ta jaddada cewa za ta ci gaba da fafutukar ganin shugabanci na adalci da mutunta kyawawan dabi’un Arewa, tare da kiran ‘yan Arewa gaba ɗaya da su tsaya tsayin daka wajen rike shugabanninsu da alhakin mutunta ƙimomin yankin.

Address

Malumfashi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kamalancy posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kamalancy:

Share

Category