ADC Gorar Dansaka

ADC Gorar Dansaka Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from ADC Gorar Dansaka, Digital creator, gora dansaka, Malumfashi.

DAN TAKARAR MAJALISSAR WAKILAI NA ADC, HON. BASHIR YAKUBU WADA, YA KAI ZIYARAR JAJE GA AL'UMMAR GARIN MAKAURACHIA ranar ...
14/07/2026

DAN TAKARAR MAJALISSAR WAKILAI NA ADC, HON. BASHIR YAKUBU WADA, YA KAI ZIYARAR JAJE GA AL'UMMAR GARIN MAKAURACHI

A ranar litinin 13-07-2026ne Dan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Karamar Hukumar Malumfashi a karkashin tutar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Hon. Bashir Yakubu Wada, ya kai ziyarar jaje ga daukacin al'ummar Garin Makaurachi da ke Karamar Hukumar Malumfashi, sak**akon mummunan harin 'yan bindiga da ya yi sanadiyyar rasa rayuka tare da jikkata wasu daga cikin mazauna garin.

A yayin ziyarar, Hon. Bashir Yakubu Wada ya gana da iyalan wadanda s**a rasa rayukansu, inda ya bayyana alhininsa da jimaminsa bisa wannan mummunan lamari. Ya yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa mamatan, Ya jikansu da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu, tare da bai wa iyalansu hakurin jure wannan babban rashi.

Haka kuma, Hon. Wada ya ziyarci wadanda s**a samu raunuka sak**akon harin, inda ya yi musu addu'ar Allah Ya ba su cikakkiyar lafiya Inda yaroki Allah Ya ba su ikon komawa rayuwarsu ta yau da kullum cikin koshin lafiya.

A ci gaba da ziyarar, Hon. Bashir Yakubu Wada ya kai ziyara ga rundunar tsaron al'umma ta 'Yan Sakai (Vigilante), inda ya yaba matuka da irin jajircewa, sadaukarwa da kuma kokarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Ya bukace su da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya da kishin al'umma.

A yayin wannan ziyarar ta jaje, Hon. Wada ya kuma bayar da tallafi ga al'ummar garin domin rage musu radadin halin da suke ciki. Sai dai ya bayyana cewa tallafin da ya bayar ba zai iya maye gurbin rayukan da aka rasa ba, illa dai wata gudummawa ce ta nuna tausayi da goyon baya ga iyalan mamatan, tare da neman al'umma su ci gaba da yi wa mamatan addu'a.

A karshe, Hon. Bashir Yakubu Wada ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kara daukar matakan da s**a dace domin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga da tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a Karamar Hukumar Malumfashi

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Rabilu Abdullahi Madara Najeriya, Idris Dahiru Dalawaja, ...
17/06/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Rabilu Abdullahi Madara Najeriya, Idris Dahiru Dalawaja, Jesuloba Isreal, Joel Emmanuel, Theophilus Tyav

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Modu Akura, Abba Kime, Nasiru Yusuf, Abul Abbas, Dadun Ne...
10/06/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Modu Akura, Abba Kime, Nasiru Yusuf, Abul Abbas, Dadun Nefa, Ibiro Oga, Rabilu Alkasim, Anas Muhammad Ganarkiyaw, Ummi Rahmat, Aminu Boko, Aisha Abubakar, Alwujud Suleiman, Abba Idris Takwasa, Mohammed Dan Sani, Yusuf Usman, Sambo Tunau Wurno, Jamilu Aminu, Abubakar Jamilu, Usman Dan Lare, Labako Bakori, Hassan Muhammad Musa, Modu Girgidi Borno, Lame Ga Mafita, Abdullahi Mohammed, Stanley Dangden, Musa Umar, Umarfarou Umarfarou, Oladipupo Olaolu

ADC Alheri ce
21/05/2026

ADC Alheri ce

Natausayamata wallahi
05/05/2026

Natausayamata wallahi

05/05/2026

“CIKAKKEN BAYANI DAGA DATTI ASSALAFY.”

Tslnannen da ya tarwatsa rayuwar yarinyar nan sunansa Muhammad Hassan (Bossman) lambar wayansa 08185**7448 dan jihar Kano ne, ban fitar da cikakken nambar wayansa ba da kuma anguwar da yake a Kano saboda dalilai na bincike.

Ita kuma yarinyar a jihar Kaduna take, ba zan fadi cikakken sunanta da anguwarsa ba saboda kiyaye mutuncinta da kuma anguwarsu.

Bossman ya hadu da yarinyar ta sanadin media, ya fara nemanta da sunan soyayya, ya yaudareta da cewa zai aureta, ya bita Kaduna ya k**a Hotel ya fara rabata da budurcinta.

Shine mutum na farko da ya fara zina da ita, wannan bidiyo na tsiraci dake yaduwa ya kai shekara guda da yinsa, bayan ya gama |a|ata rayuwar yarinyar sai yace gaskiya shi ba zai iya aurenta ba.

Shikenan ta watsar da shi, ta samu wani zai aureta, da wannan tsinannen da ake kira Bossman yaji labarin zata auri wani, sai ya fara aika mata wannan bidiyo na barazana ta hannun kawarta, cewa idan ta kuskura tace zata auri wani zai watsa bidiyon.

A haka dai har wanda ta samu daga baya zata aura ya samu labari, kuma yace ya amince zai aureta a haka matukar bidiyon bai fita ba.

Ana haka yanzu saura wata daya a daura mata aure, to da wancan tsinannen yaji labari sai ya saki bidiyon a media don ya hanata aure ya kuma tarwatsa mata rayuwa.

Masu ganin laifin yarinyar ku san irin kalaman da zaku fadi kafin Allah Ya jarrabeku, domin 'ya'yanku da kuka haifa da kannenku mata basu fi karfin tsinannun maza su yaudaresu su bata musu rayuwarsu ba.

Muna kan tattaunawa da iyayenta don daukar matakin shari'a akan tsinanne Bossman, sai ya girbi sak**akon abinda ya aikata da taimakon Allah.

Daga Datti Assalafiy

INSHA ALLAH
02/05/2026

INSHA ALLAH

02/05/2026

YA ALLAH KASA MUGA FADUWAR TUNUBU DA APC A NIGERIA

02/05/2026

Matsalar mu ce gaba ɗaya.

Idan muna sayar da kuri’a, muna goyon bayan rashin gaskiya, ko muna zaɓe bisa son zuciya,
to muna taimakawa wajen lalata makomar mu ne.

Lokaci yayi da zamu fara gyara kanmu.

Domin gyaran ƙasa yana farawa ne daga gyaran al’umma.

Duk da kalubalen da muke fuskanta…
ina da yakinin cewa canji yana yiwuwa.

Amma wannan canjin ba zai zo hakanan ba,
zai zo ne idan aka samu sabbin tunani, sabbin shugabanni, da haɗin kan al’umma.

01/05/2026

MUNA A ADC BABU CANJI
ADC DAGA SAMA
HARKASA
INSHA ALLAH

Address

Gora Dansaka
Malumfashi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ADC Gorar Dansaka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share