30/11/2025
Allahu Akbar Wal-Hamdu lillah wa Subhanallah, ko kuma Subhanallah Wal hamdu lillah wa La'ilaha illal Lahu Wallahu Akbar (awata ruwayar).
★ Imam Tirmizy ne ya ruwaito wannan hadisin, acikin Jami'ut Tirmizy juzu'i na 2 shafi na 509.
Awajen Imamut Tirmizy yake cewa "An ruwaito hadisai da dama game da SALATUT TASBEEHI amma yawancin hadisan basu inganta ba. (Akwai rauni awajen masu ruwayar).
★ IMAM ABU-DAWUD shima ya ruwaito hadisin ta wata hanyar daban (wacce ba irinta Tirmizy ba. kuma Malamai sun HASSANA hadisin.Aduba cikin SUNANU nasa, juzu'i na 2 shafi na 96, hadisi na 1,297.
★ IMAMUL HAKIM ya ruwaito irin wannan hadisin ta hanyar ABDULLAHI BN UMAR BN ALKHATTAB (ra). Kuma yace WANNAN HADISIN YA INGANTA. BABU WATA QURA-QURA ACIKIN ISNADINSA.Daga cikin Hujjojin da suke tabbatar da INGANCIN HADISIN, shine yawaitar Sahabbai da Tabi'ai wadanda suke yin wannan Sallar, kuma suke koyar da ita ga Almajiransu.ABDULLAHI IBNUL MUBARAK (RA) ya kasance yana yin wannan sallar kuma yana koyar da ita ga Almajiransa.
Kuma dukkan wadanda s**a Ruwaito wannan Sallar daga Ibnul Mubarak, Mutane ne Ingantattu. kuma kowa yasan cewar Ibnul Mubarak ba zai koyar da duk abinda bai Inganta ba.
(Aduba cikin MUSTADRAKUL HAKIM ALA SAHIHAYNI juzu'i na daya, shafi na 464).
★ IMAM IBNU MAAJAH (rah) shima ya ware BABI GUDA ACIKIN LITTAFIN HADISINSA. wanda acikinsa yayi magana akan Salatut Tasbeehi tare da kawowa hadisai ingantattun daban daban.(Aduba cikin Sunanu Ibni Maajah juzu'i na 1 shafi na 442, hadisi mai lamba 1,430)
★ IMAM ALBAIHAQEE (rah) shima bayan ya kakkawo hadisan da s**ayi magana akan SALATUT TASBEEHI yace : "Kasancewar Salihan bayin Allah irinsu Ibnul Mubarak suna yinta, kuma an ruwaito ta daga garesu, Shima hujjah ne akan cewa hadisin Marfu'i ne kuma ya inganta.
(aduba cikin SHU'ABUL IMAN juzu'i na 1 shafi na 427).IBNUL MUNDHIRY (RAH) shima ya ruwaito wannan hadisin sannan yace An ruwaito shi ta hanyoyi Sahihai masu yawa daga Sahabbai daban daban.Kuma Malaman Hadisi da dama sun hanyoyin.(aduba cikin ATTARGHEEB WAT TARHEEB juzu'i na 1 shafi na 267).
Albaniy yayi kokarin raunata wata daga cikin Isnadan hadisin, yace wai akwai wani Majhuli acikin isnadin. Amma Malamai da dama suna sun mayar masa da maganarsa.
★ IMAM SUYUTY ya kawo sunayen Manyan HUFFAZU (maluma MAHADDATAN hadisi) sama da guda 20 wadanda s**a inganta Hadisan SALATUT TASBEEHI. acikinsu akwai:
1. HAFIZ ABU SA'EED AS-SAM'ANY.
2. HAFIZ KHATEEB ALBAGHDADY.
3. HAFIZ IBNU MUNDAH.
4. HAFIZ IBNUS SALAH.
5. HAFIZ ABU MUSAL MADANY.
6. HAFIZ ZARKHASHY.
(Aduba cikin LA'ALI'UL MASNU'AH juzu'i na 2 shafi na 42 zuwa na 45).A takaice dai SALATUT TASBEEHI ibadah ce mai falala wacce ruwayarta ta inganta daga Manzon Allah ﷺ.
©Comr.Abdulmalik lawal malumfashi