12/06/2026
Illolin Hassada Guda Goma
1. Hassada Tana rage imani Hassada tana raunana tsoron Allah da yarda da ƙaddararsa.
2. Hassada Tana hana nutsuwar zuciya – Mai hassada kullum cikin damuwa da baƙin ciki yake saboda ganin ni'imar wasu.
3. Hassada Tana haifar da ƙiyayya – Hassada tana haddasa gaba da ƙeta tsakanin mutane.
4. Hassada Tana lalata zumunci – Dangantaka tsakanin 'yan uwa da abokai kan rushe saboda hassada.
5. Hassada Tana jawo zunubai – Kamar gulma, ƙage, cin mutunci da ƙulla sharri.
6. Hassada Tana hana godiya ga ni'imomin Allah – Mai hassada yakan manta da ni'imomin da Allah Ya yi masa.
7. Hassada Tana sa mutum ya ƙi gaskiya – Wani lokaci hassada tana hana mutum karɓar gaskiya daga wanda yakewa hassada.
8. Hassada Tana cutar da lafiya – Yawan damuwa da baƙin ciki na iya shafar lafiyar jiki da ta zuciya.
9. Hassada Tana hana ci gaba – Maimakon mutum ya mayar da hankali wajen inganta kansa, sai ya shagaltu da abin da wasu suke da shi.
10. Hassada Tana kai mutum ga halaka duniya da lahira – Idan ba a tuba ba, hassada na iya zama sanadin asarar lada da samun azaba.
Maganin hassada:
1. Yawan tuna Allah da yin zikiri.
Yarda da ƙaddarar Allah.
2. Yin addu'a ga wanda aka yi wa hassada.
3. Godiya ga ni'imomin da Allah Ya yi maka.
4. Son alheri ga Musulmai kamar yadda kake so wa kanka.
"Ku guji hassada, domin hassada tana cinye ayyukan alheri kamar yadda wuta take cinye itace." (Hadisi)
Allah ya kiyaye mu daga Hassada.