11/09/2025
Karanta Cikakken Tarhin Samuwar Takutaha da Dalilin da Yasa ake Yinta Harzuwa YanzuAsali, kusan shekaru dubu da s**a gabata, Kano ba gari bane, Shirayi ne kawai, kamar yadda marubucin wakar Bagauda ta Kano ya bayyana.
"Ku sani, daga yau, komai tsakanina daku, sai yaki da tsinin mashi, ba yaudara, bawani boye boye, domin ba mayaudari sai matsoraci, ku shirya gani nan zuwa gareku "
Mataki biyu s**a dauka, na farko sunyi kokarin bada cin hanci ga Sarki Yaji, amma yaki karba, yace a maida musu baya so. Na biyu, sai s**a koma ga Tsumburbura, domin neman nasara, amma ta gaya musu, cewa wannan yaki ba nasara, domin lokacin karshen addininsu a kasar Kano yazo.
Acikin watan dai, rundunar musulmi s**a fuskanci, rundunar maguzawa, a gefen Dutsen Dala, inda s**a hadu, aka gwabza. A wannan lokacin ne, Jarmai Bajere ya samu nasarar Kutsa kai cikin shigifar Tsumburbura, inda ya samu wani halitta na tsaye, rike da maciji a hannunsa, ya daga mashi ya bugawa halittar nan, tayi kuwwa ta fito a guje. Nan da nan s**a bita, inda ta nufi kofar ruwa, ta fada cikin ruwan Dankwai. Wannan Shi ya kawo karshen Tsumburbura, da kuma addinin maguzawa a garin KanoTakutaha
Samuwar wannan Nasara, ba karamin abu bane a wurin musulman Kano. Wanda aka shafe sama da shekaru 100 ana nema. A dalilin haka ne, ya sanya musulman kanawa duk shekara, s**an taru su hau Dutsen Dala domin tunawa da wannan nasara da musulunci yayi akan Maguzanci. Su nunawa duniya cewa, addinin Allah yau ya shafe addinin kafirai. Domin kafin zuwan musulunci, ba mai hawa Dala in ba Babban limamin addinin ba. Amma zuwan musulunci, yanzu kowa ma sai ya hau, ya yi kashi ma aka. Wannan shine dalilin da ya sanya ake takutaha a duk shekara a Kano, Wanda wasu da basu san tarihin ba, ke ganin jahilci ne, ko kuma abu ne, da ya sabawa musulunci.
Allah ya sa mu dace Amin.