05/08/2026
YANZU-YANZU: Sarkin Musulmi Ya Nemi A Gudanar Da Binciki Kan Ki*san Kanal Abdussalam Ude
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da rundunar sojin Nijeriya su gaggauta gudanar da bincike kan kis*an Kanal Abdussalam Ude tare da hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
Ya kuma yi Allah-wadai da nuna ƙiyayya da wariya ga Musulman Igbo a Kudu maso Gabas, yana kira ga ƴan Nijeriya su rungumi zaman lafiya, haƙuri da haɗin kai, k**ar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito.
An ka*she Kanal Ude ne yayin wani hari da ake zargin masu garkuwa da mutane ne s**a kai gidansa a Jihar Nasarawa, yayin da ƴansanda s**a tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin.