Comrade Nazeer Adamu Mashegu

Comrade Nazeer Adamu Mashegu Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Comrade Nazeer Adamu Mashegu, Media/News Company, Minna.

SHEKARU 63 NA KUNCI DA BAKINCIKI?....Shekaru 63 na bakinciki da takaicin halin da uwa take ciki, ya sanya ƴaƴanta da yaw...
01/10/2023

SHEKARU 63 NA KUNCI DA BAKINCIKI?....

Shekaru 63 na bakinciki da takaicin halin da uwa take ciki, ya sanya ƴaƴanta da yawa sun zama barayi, 'yan ta'adda, Mazambata, maciya amana, 'yan rashawa, saboda rashin iya shubancin ubannin gidanta, tare da rashin bawa ƴaƴanta kulawar data dace.

Wannan ta sanya nake ganin babu wani abun farinciki, ko murna da jin daɗi a lokacin da ake sace ya'yan wannan uwa, ake kashe su, ake bautar dasu, ake wulakanta mutuncinsu, ake sace dukiyarsu, rayuwarsu tai tsada, babu tsaro, lafiya, ilimi,, t**i, lalacewar kasuwanci da harkar tafiyar da shugabancin wannan uwa mai kukan jini.

Lallai lokaci ne daya kamata, ƴaƴan wannan Uwa, su nema mata hanyar tsira da yanci na gaskiya, bana bazambata da barayi tattalin arzikinta ba, domin dai shi yanci yana nufin a komai a ganshi, hatta a abincin da zaka kai bakinka, amma idan har babu shi a kowanne bangaren rayuwa, hakan yana nuna bai da amfani yin ƙaryar akwai shi, kuma hakan yana nuna cewa lallai bai samu ba, kawai a baki ne da rubutu yake yanci kamar yanda marasa kan gado daga ya'yan wannan Uwa suke tayata murnar ci baya da kara taɓarɓarewa 😭

Wannan tasa bamu da abinda zamuyiwa wannan uwa murna dashi, sai dai mu tayata takaici da kaicon halin da take ciki, wanda kusan shekaru 63 ta kasa samun damar tsayawa da kafarta, saboda haihuwar ya'ya marasa kishinta da kokarin ganin ta samu ingantacciyar rayuwa.

Yaku ƴaƴan wannan Uwa lokaci yaya da jinin dake malala a cikinki zai tsaya, kuyi duk yanda zakuyi ku kawo sauki tun daga harkar tsaronta da tattalin arzikin da take da shi, tun kafin wankin hula ya kaiku dare!.

Yana da kyau a nemawa wannan Uwa, hanyar tsira da addu'ar sake salon tafiyar da rayuwar ƴaƴant, tun kafin a kaita kushewa.

Alhamdulillah, Barka da zuwa shafin Comrade Nazeer Adamu.
11/08/2023

Alhamdulillah, Barka da zuwa shafin Comrade Nazeer Adamu.

Address

Minna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Comrade Nazeer Adamu Mashegu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share