25/09/2025
MU YAWAITA SALATI A GARESHI (S.A.W) ❤️
"Wannan shine daren juma'a, dare ne da ake son yawaita yin salati ga Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama a daren sa da kuma ranar Juma'a"
"Kada mu yi ƙasa a guiwa wajen yawaita yi masa salati a bisa cancantarsa da hakan, domin lallai duk wanda ya yi salati ɗaya a gareshi, shima Allah zai yi masa guda goma madadinsa"
"Kuma lallai ka sani! Tabbas babu wani Musulmin da zai yawaita salati ga Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallama, face sai Allah Ya haskaka zuciyarsa, kuma ya gafarta masa zunubansa, kuma ya yalwata ƙirjinsa, sannan kuma ya sauƙaƙa masa dukkanin lamuransa, to ku yawaita salati a gareshi, tsammaninku Allah Ya sanya ku daga cikin tafarkin daidai, kuma Ya gafarta muku zunubanku"
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ٠
اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ٠