14/04/2025
KÃFIN KA YI AURE GA SHAWARA!
1) Kafin ka yi aure dole ka samu cikakken sani game da aure, ƙa'idoji da sharuɗɗan da Allah (s w a) ya shimfiɗa a cikinsa
2) Kafin ka yi aure yã dãce ka samu ilimin yadda zã ka mu'amalanci matarka gurin mu'amalar aure, don gudun faɗawa cikin jagwalgwalo
3) Dole ka san cewa kaine wanda Allah ya ɗorawa alhakin ciyar da iyalinka, ilmantar da su, tufatar da su da nema musu lafiya lokacin da suke cikin rashin lafiya
4) Ya zama dole ka samu cikakkiyar sana'ar da zaka iya ɗaukar duk wata ɗawainiyar iyalanka kafin kayi aure. Addini ma bai yarda wanda ba zai iya ɗaukar nauyin iyali ya yi aure ba
5) Idan kana son ɗorewar zaman aurenka, to sai ka samu kyakkyawar niyya game da auren, ba don sha'awa kawai ko dan abokanka sun yi aure kaima za ka yi ba
6) Ya dace ka bayyanawa wadda zaka aura ainahin ɗabi'unka, kar ka ɓoyewa wadda zaka aura ɗabi'arka, idan ɗabi'ar mara kyau ce, sai kayi ƙoƙarin gyarawa
7) Kada ka nunawa wadda zaka aura kai mai wadata ne alhalin ba haka abin yake ba, ka nuna mata gaskiyar yadda kake, idan taƙi akwai wadda zata soka a yadda kake
8)Ya dãce ka fahimci ɗabi'ar wadda zaka aura kafin ka aureta, domin ka san yadda za ka zauna da ita
9) Kada ka yi doguwar soyayya kafin aure, idan kuka fahimci kuna son junanku kuma kun fahimci junanku sai kuyi aure, doguwar soyayya tafi k**a da yaudara
10) Ka nunawa wadda zaka aura kana girmama iyayenka da ƴan uwanka, kuma kaima ka girmama iyayenta ta ƴan uwanta.
Ya Allah kabamu abokanzama nagari, ka bamu ikon kyautatamusu, suma ka basu ikon kyautatamana Ya Hayyu Ya Qayyum.
Guzuri Domin Makoma ✍️