Muryar Jahar Neja

Muryar Jahar Neja An kafa sashen Hausa na Muryar Jahar Neja ran 15 ga watan Junairu, shekara ta 2017, domin watsa Labarai Da Dumi Duminsu

WAYE HON ABUBAKAR Lado Suleja :  Allah Sarki Rayuwa Tsohon Dan Majalisar Tarayya me Wakiltar Suleja Tafa Gurara Federal ...
05/08/2026

WAYE HON ABUBAKAR Lado Suleja : Allah Sarki Rayuwa Tsohon Dan Majalisar Tarayya me Wakiltar Suleja Tafa Gurara Federal Constituency ya bayyana yadda ya hadu da Kalubalalen Rayuwa a Jahar sa ta Niger da yadda yasha Tsangwama akai ta kulla masa Sharri.

Hon Suleja yace anyi wani Lokaci da komai akai sai ace LADO ne ko Mace ce tayi Tuntube ko yaro ba Lafiya ko akai wa Wata Ciki sai ace Lado ne kai ko tari Mutum yayi aka kaisa Asibiti sai ace ai lado ne Amma yayi ya Wuce.

Yace an taba dasa B0m a Jahar Niger State Mutane da yawa sun Rasa Rayuwar su akace Lado ne yasa B0m din aka kamasa aka Kullesa akai Kasa DSS aka ajesa a Underground Wata da watanni tare da Handcuff Hannu da Kafa a rufe masa Ido in za'a kaisa Interrogation Upstairs.

Haka yayi Wata da watanni a Wannan wajen a rufe Kuma ya kara da Cewa yana ciki ya Musuluntar da Mutane babu iyaka a headquarter na DSS inda aka ajesa a Wannan underground din haka akace masa yayi Hakuri Siyasa ne yace ba Komai.

Wanda s**ai masa ma ya yafe musu Duniya da Lahira duk da yace yasansu Wanda s**a kukla Masa Wannan sharrin amma ya yafe musu an riga an wuce Wannan wajen yazama Tarihi Yanzu kuma Sabida haka shi ya yafe Musu.

Haka Yace 2019 ma aka kamasa aka Kullesa shi Wannan Lokacin ma yana Dan Majalisar Tarayya yana Kan Kujera aka kamasa aka Kullesa aka Shirya da wani IG a Lokacin akace wai yayi Kidnaping Chairman din Local Government aka kamasa aka Kullesa.

Ashe wai anyi hakane setup ne domin a rikesa kar'a Sakesa sai an gama Submitted din suna a INEC yacce bashi da dama Shiga Zabe yace yana Wajen Yan SAS ya biya aka basa Waya Kira daya kawai yayi aka turo Masa yan Majalisu Guda 9 kwara 2 ne kawai ya Arewacin Nigeria.

Gaba daya Sauran guda 7 din Yan Kudancin Nigeria ne Yarabawa da kuma Inyamurai aka zo Majalisa tayi Shutdown taba da 24 hours in Ba'a Sakesa ba, nan da nan aka Sakesa Sabida me Sabida dama duk Siyasa ce Sabida haka yace ya saba Gani Sharri Mutane kai'di da Makirci duk ya saba Gani.

Kuma duk akan Siyasa ne Amma alhamdulillah duk irin haka inta faru dashi da zarar ya fita sai Allah ya dagasa a Karshe Hon Abubakar LADO yace indai Zuciya Lafiya lau take to karka damu da masu kullaa maka Sharri ko sunyi Allah zai wankeka.

Ance LADO Dan'ta'adda ne ance Dan kaza ne Amma a haka duk Lokacin dana fito Takara sai Al umma sun Zabe kunga kuwa koda Asiri ne ya kamata ace ya karya tun tuni Sabida haka komai zakai ka rike Allah ka rabu da sharrin masu Sharri inji Tsohon Dan Majalisar Tarayya Hon Abubakar LADO SULEJA.

Address

Maitumbi David Mark Road
Minna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Jahar Neja posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share