Auwal Mustapha Mahuta

Call Contact the business

Auwal Mustapha Mahuta Alhamdulillah for everything ��

YANZU-YANZU: Dangote Refinery Ta Bude Siyar da Hannun Jari Na Naira Triliyan Biyu A NGXMatatar Dangote ta buɗe tayin say...
14/09/2026

YANZU-YANZU: Dangote Refinery Ta Bude Siyar da Hannun Jari Na Naira Triliyan Biyu A NGX

Matatar Dangote ta buɗe tayin sayar da hannun jari na kimanin ₦2.15 triliyan a kasuwar hannun jari ta Najeriya.

Farashin kowane hannun jari ya kasance ₦525, yayin da mafi ƙarancin adadin da mutum zai iya saya shi ne hannu 10, wanda darajarsu ta kai ₦5,250.

Za a ci gaba da sayar da hannun jarin har zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2026, a cewar sharuɗɗan tayin.

AKWAI LAUJE CIKIN NADI NA SAYAR DA HANNUN JARI A MATATAR MAN FETUR NA DANGOTE Atiku Abubakar Yace Da Zaran Yaci Zabe Zai...
13/09/2026

AKWAI LAUJE CIKIN NADI NA SAYAR DA HANNUN JARI A MATATAR MAN FETUR NA DANGOTE

Atiku Abubakar Yace Da Zaran Yaci Zabe Zai dawo da tallafin man fetur da Tinubu ya cire. wannan maganar ta Yi ma Tinubu zafi sosai

A zargin APC ta sanya DANGOTE ya sayarma dukkan talakawa da masu kudin Nigeria hannun jarin matatar man fetur dinsa domin ayi siyasa da abun a Kuma yaki kudurin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur.

Ta yadda za a yaki kudurin Atiku Abubakar da sayar da hannun jarin DANGOTE shi ne sai 'yan Nigeria sun gama zuba kudinsu a hannun jarin, sai a ce ma su idan Kuka zabi Atiku Abubakar zai dawo da tallafin man fetur Dan haka za ku Yi asarar kudadenku da Kuka sayi hannun jarin.

Dan haka talakan da ya sayi hannun jarin na 50k ko 100k ko 150k ko 200k ba zai so yayi asarar kudinsa ba zai yaki Atiku ya samama kudinsa kariya.

A yanzu za a sayar maka da hannun jarin akan ₦525 duk daya a lokacin da litar Mai ke ₦1450, idan Atiku Abubakar ya dawo da tallafin man fetur, misali duk Lita daya ta dawo ₦500 ko 800 naira ka ga asarar nawa za ka yi cikin Hannun Jari Da kasiya Na Dangote ? kila abinda ka saya ₦525 zai iya dawowa 100 ko 150 naira kowane Hannun Jari.

Hannun jarin DANGOTE Ina zargin siyasa ce yaudara ce irin ta APC, sun ga ba yadda 'yan Nigeria za su zabe su, shiyasa s**a fito da wannan yaudarar Dan haka a kiyaye wallahi. Kada ka Yi Wasa da dukiyarka. wannan tunanina.

Sannan Idan Ka Mallaki Hannun Jari A Dangote Refinary Kasani Cewa Ka zama Daya Daga Cikin Wanann Mutanen Either Risk bearer Or Profit Earner Gobe Kuma 14th September Za afara siyan Shares, Har yanzu Muna cikin sarkakiya Akan abinda Atiku Ya Fada Cewa Zai dawo Da Tallafin Man Fetur in Har Yaci Zabe

Ayayin Da Shikuma Dangote Yakara kudin man fetur, Kuma Yake so Ya Bude Bada damar Saka Hannun Jari a Matatar man fetur dinsa

Yakamata muyi tinani sosai Kamin muzuba dukiyarmu, bance Kada Ku zuba kudinkuba Yana Da kyau Kowa yayi tinani Da Kansa, don Nima zubawa zanyi Amman Bazan Zuba sosaiba.

Gobe, Litinin kamfanin Dangote Refinery zai bude mallakar siyan hannun jari ga jama’a.Za a sayar da Share guda kan duk S...
13/09/2026

Gobe, Litinin kamfanin Dangote Refinery zai bude mallakar siyan hannun jari ga jama’a.

Za a sayar da Share guda kan duk Share 1 akan ₦525
Mafi ƙaranci = Shares 10
Wacce take farawa daga ₦5,250

Wato, ₦5,250 ne mafi ƙarancin kuɗin da za a fara da shi wajen sayen hannun jarin kamfanin.

Da ɗumi-ɗumi: Ba fa zan taɓa Dawo da Tallafin Man fetur Ba a gwamnatina gwanda kowa ma ya haƙura  –Shugaba Tinubu Gwamna...
13/09/2026

Da ɗumi-ɗumi: Ba fa zan taɓa Dawo da Tallafin Man fetur Ba a gwamnatina gwanda kowa ma ya haƙura –Shugaba Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba, tana mai jaddada cewa cire tallafin wani muhimmin mataki ne na gyaran tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Mai Bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce shirin da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana na dawo da tallafin mai idan aka zaɓe shi a 2027 ba zai yi wa ƙasar alheri ba.

A cewarsa, dawo da tallafin zai rusa sauye-sauyen da aka aiwatar a ɓangaren man fetur, sannan zai jawo matsalolin doka da na kuɗaɗen gwamnati.

Onanuga ya kuma yi gargadin cewa hakan na iya rage sha'awar masu zuba jari a harkar tace mai a Najeriya, ciki har da Matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai.

Me Zakuce?

13/09/2026
12/09/2026

Dan'uwa saurara kaji

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, sun bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai r...
07/09/2026

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, sun bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da ya janye wani zargi da ya yi kan tsohon gwamnan, ko kuma ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin. Ko kuma ya fuskanci matakin shari'a.

A cikin wata sanarwa da Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan, sun bayyana matuƙar damuwa kan kalaman da Janar Christopher Musa ya yi a ranar 3 ga Satumba, 2026, yayin wata hira kai tsaye a shirin Politics Today na Channels Television.

A yayin shirin, an bayyana cewa Ministan Tsaron ya zargi Nasir El-Rufai da hannu wajen tsarawa da shirya kashe-kashen mutane a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar.

APC ta ƙaddamar da ƙungiyoyin magoya bayan Tinubu a KanoJam’iyyar APC ta gudanar da taron ƙaddamar da ƙungiyoyin magoya ...
05/09/2026

APC ta ƙaddamar da ƙungiyoyin magoya bayan Tinubu a Kano

Jam’iyyar APC ta gudanar da taron ƙaddamar da ƙungiyoyin magoya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kano, wani mataki da ke cikin ƙoƙarin ƙara haɗa kan magoya bayan shugaban da kuma ƙarfafa tsarin yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar ta bayyana shirin tantancewa da haɗa ƙungiyoyin da ke yi wa Tinubu kamfen a faɗin ƙasar, domin samar da tsari guda da kuma kauce wa saƙonni masu karo da juna.

A Kano, jam’iyyar ta kuma ƙara mayar da hankali kan ƙarfafa tsarin jam’iyya daga matakin ƙasa, musamman wajen wayar da kan masu zaɓe da kuma tattara ƙuri’u domin zaɓen 2027.

Address

Minna

Telephone

+2349161384345

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Auwal Mustapha Mahuta posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Auwal Mustapha Mahuta:

Shortcuts

Share