Nura A Lawal TV

Nura A Lawal TV wannan shafin zaidinga ilimantar daku da fadakarwa,gami da nisha dantarwa

19/09/2026
18/09/2026

Muna rokon allah ya jikan Su

18/09/2026

Allah ya saka ma wadan da aka zalinta #

Gwamna Radda Ya Halarci Babban Maulidin Zagaye a KatsinaGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci babba...
14/09/2026

Gwamna Radda Ya Halarci Babban Maulidin Zagaye a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya halarci babban taron Maulidin Zagaye da ake gudanarwa a cikin garin Katsina.

Gwamna Radda ya kasance Babban bako da ya halarci taron, wanda ya samu halartar malamai da al’ummar Musulmi domin tunawa da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

Gwamnan ya samu rakiyar Kakakin majalisar dokokin jihar Katsina Rt.Hon Nasir Yahaya Daura, Kwamishinan Addinai Ishaq Shehu Dabai, tare da wasu daga cikin makusanta sa.

MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government

September 13, 2026.
Allah ya kara soyayyan annabi muhammad (s a w).

Gwamna Radda Ya Tsaya Ya Gaishe da Masu Zagayen Maulidi a JigawaGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON,...
13/09/2026

Gwamna Radda Ya Tsaya Ya Gaishe da Masu Zagayen Maulidi a Jigawa

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ya tsaya a kan hanyarsa ta tafiya domin gaisawa da mahalarta zagayen Maulidi da ya gudana a ƙaramar hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa.

Gwamna Radda ya nuna girmamawa da ƙauna ga masu gudanar da zagayen, inda ya tsaya ya gaishe da su tare da yi musu fatan alheri. Muna jinjina ma dikko Ummaru Radda.

Assalamu Alaikum warahmatullah.Ina son in yi wannan bayani domin kwantar da hankalin masoyana da kuma gyara wasu labaran...
10/09/2026

Assalamu Alaikum warahmatullah.

Ina son in yi wannan bayani domin kwantar da hankalin masoyana da kuma gyara wasu labaran da ake yaɗawa ba tare da tabbatacciyar hujja ba.

Alhamdulillah, sama da watanni biyu kenan da muka baro asibiti. Gaskiya ne na yi rashin lafiya, kuma hakan ba abin kunya ba ne. Cuta daga Allah take, kuma Shi ne mafi cancanta a sanar da komai, domin tun farko Shi Ya sani, Shi Ya jarabce ni da ita, kuma Alhamdulillah Shi ne Ya yaye min ita.

Abin da yake bani mamaki shi ne yadda wasu ke ta yaɗa labarai da cewa har yanzu ina cikin wani hali, alhali kuwa babu wanda ya taɓa ganin hotona ko bidiyona a lokacin da nake jinya. Ko a lokacin da nake asibiti ban bari a ɗauke ni hoto ko bidiyo ba, hatta ni kaina ban ɗauki hoto ko bidiyo da wayata ba. Saboda haka duk wanda yake cewa ya gan ni a asibiti ko yana da wani sahihin bayani daga lokacin jinyata, ya san abin da yake faɗa.

Alhamdulillah, na yi rashin lafiya kuma na warke. Amma ba dole ba ne in fito in bayyana irin cutar da na yi ga mutane. Tunda Allah ne Ya ɗora min ita, Shi ne mafi cancanta da ya san sirrinta. Da zafin cuta da sauƙinta duk daga Allah suke, kuma Shi kaɗai ne Mai ikon jarabtar bayinsa da abin da Ya ga dama.

Kwanaki uku da s**a gabata na saki sabuwar waƙata ta siyasa mai suna "Tabare", wadda manufarta ita ce wayar da kan al'umma da jawo hankalinmu kan muhimman abubuwan da s**a shafe mu. Wannan shi ne abin da nake yi yanzu, kuma ina ci gaba da aikina cikin ƙoshin lafiya.

Ina kuma jan hankalin gidajen jaridu da masu wallafa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin labari kafin su yaɗa shi.

Ga masoyana kuma, ina roƙonku da ku kwantar da hankalinku. Wannan jarabawa ce daga Allah, kuma Allah yana jarabtar bayinsa. Idan har annabawa sun fuskanci jarabawa, to wanene ni da ba zan fuskanci tawa ba? Alhamdulillah, Allah Ya bani ikon cin wannan jarabawa, kuma ina ci gaba da gode Masa a kowane hali.

A ƙarshe, duk abin da yake faruwa a rayuwa yana daga wani ɓangare na ɗaukaka. Domin idan ba a san mutum ba, ba a cika magana a kansa ba. Ina gode wa Allah a kowane hali.

Nagode da addu'o'inku, ƙaunarku da goyon bayanku.

Alhamdulillah ina lafiya 🤍

Innalillahi wa inna ilaihi raji'unCikin Alhini muke kara sanar da al'ummar wannan masarauta rasuwar daya daga cikin iyay...
10/09/2026

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un

Cikin Alhini muke kara sanar da al'ummar wannan masarauta rasuwar daya daga cikin iyaye, kuma diya ga Sarki Muhammadu Sani kanwa ga marigayi sarkin Gumel Alhaji Ahmad Muhammad Sani II con.

Allah Kaji kan mairam Dada kayi mata Rahma ka kyautata makwancin ta, Allah ka bamu ikon juriya da hakuri akan wannan jarabawar da kayi mana.
Allah ka gafarta masu tare da sauran al'ummar musulmi da s**a rigamu, idan ta mu tazo ka sa mu cika da kyau da Imani,Amin nura a lawal tv.

Zainab Abdullahi wadda aka fi sani da Zee Diamond ta rasu ne a jihar Kaduna bayan fama da rashin lafiya.Jarumar ta yi fi...
08/09/2026

Zainab Abdullahi wadda aka fi sani da Zee Diamond ta rasu ne a jihar Kaduna bayan fama da rashin lafiya.

Jarumar ta yi fice ne a shirin dogon zango na Labarina inda ta fito a matsayin Talatuwa.Allah ya jikan ta da rahama Amin.

08/09/2026

Allah ya Kara mana son manzon allah (s a w)

Address

Minna
920101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nura A Lawal TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category