26/08/2025
Galatasaray na son Bissouma, Isak bazai sake bugawa Newcastle wasa ba, United zata iya sayar da Bruno, Spurs na son Simons, Chelsea Zata biya kudin Garnacho, an kawowa Madrid tayi Mai gwabi kan Vinicius, City Zata ci gaba da Jiran Donnarumma
Yves Bissouma na shirin komawa Galatasaray yayin da ake tattaunawa da Tottenham a matakin karshe. An riga an cimma sharuΙΙa tsakanin Bissouma da Galatasaray. (Fabrice Hawkins)
Alexander Isak bashi da wani shirin sake bugawa Newcastle United wasa. (x/JacobsBen)
Manchester United na iya farfado da sha'awarta ta siyan Carlos Baleba Idan an sayar da Bruno Fernandes zuwa Saudi Arabiya, Mafi karancin farashin Brighton kan dan wasan shine fam miliyan Β£100m. (The Guardian)
Tottenham na zawarcin dan wasan da Chelsea ke zawarci Xavi Simons, wanda ake sa ran zai bar RB Leipzig kafin a rufe kasuwar musaya. (CaughtOffside)
Chelsea na son biyan kayyadadden farashin fam miliyan Β£35m akan Alejandro Garnacho, amma Manchester United na son fam miliyan Β£50m akan dan kasar Argentinan.
Blues na iya Kari zuwa fam miliyan Β£40M gami da Ζari, wanda suke fatan za a iya cimma yarjejeniyar. (Jacob Steinberg)
Wata kungiya da ba a bayyana sunanta ba a kasar Saudi Arabiya tana shirin kai tayin fam miliyan β¬130m akan Vini Jr domin gwada kudirin Real Madrid C.F na rike shi.
Dan wasan na Brazil ya burgesu bayan da ya taso a bencin Madrid a karshen makon da ya gabata. (Defensa Central)
Man City sun shirya jira har zuwa watan Janairu kafin su yi yunΖurin Ιaukar Gigio Donnarumma, saboda kudin siyan zai kasance ya yi Ζasa sosai, ko kuma su jira zuwa bazarar gaba idan Ιan wasan zai zama free agent.
A halin yanzu, Man City ta bayar da tayin β¬15M ne kawai, wanda ya yi Ζasa da tsammanin PSG, wadda ke neman β¬25Mββ¬30M. (The Athletic)
Wanna Dan wasane ya k**ata kungiyar ku ta dauka??? SANNAN KADA AMANTA AYI FOLLOW DOMIN Kawo labaran kwallon kafa masu mahimmaci kuyi follow