MGC Hausa

MGC Hausa Kafar yada Labarai da rahotanni, wasannin da kuma shirye-shirye masu ilmantarwa da debe kewa daga shafin MGC hausa a ko ina a fadin Duniya.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar...
30/05/2026

Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Najeriya, Rabe Abubakar, tare da matarsa a yankin Matazu da ke Jihar Katsina.

An ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar yayin da tsohon jami'in sojan da matarsa ke kan hanyarsu ta zuwa birnin Katsina, inda maharan s**a tare motarsu s**a yi awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa direban motar ya samu raunin harbin bindiga lokacin harin, amma ya yi nasarar tserewa daga hannun maharan.

Haka kuma an gano motar tsohon jami'in sojan, wata jan motar Peugeot 504, wadda aka kai ofishin rundunar 'yan sanda na Matazu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina da kuma hedkwatar rundunar sojojin Najeriya ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da sace tsohon janar ɗin da matarsa ba.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun fara bincike da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.

Lamarin ya sake jawo damuwa kan matsalar tsaro da hare-haren ’yan bindiga da ke ci gaba da addabar wasu yankuna na Arewa maso Yammacin Najeriya, musamman a Jihar Katsina.

Ina miƙa saƙon barka da Sallah ga ɗaukacin ma’aikatan MGC HAUSA tare da al’ummar Musulmi a faɗin duniya baki ɗaya, Allah...
27/05/2026

Ina miƙa saƙon barka da Sallah ga ɗaukacin ma’aikatan MGC HAUSA tare da al’ummar Musulmi a faɗin duniya baki ɗaya, Allah Ya maimaita mana wannan lokaci cikin ƙoshin lafiya, zaman lafiya da yalwar arziki.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ibadunmu, Ya yafe mana kura-kuranmu, Ya sanya wannan Sallah ta zama sanadin haɗin kai, soyayya da ci gaban al’umma.

Barkanmu da Sallah, Allah Ya maimaita mana Amin.

Tsohon Ministan Sadarwa na Najeriya Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu kuri’u 12,120 a zaɓen fidda gwani na kujerar gwamna...
22/05/2026

Tsohon Ministan Sadarwa na Najeriya Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu kuri’u 12,120 a zaɓen fidda gwani na kujerar gwamnan Jihar Gombe ƙarƙashin jam’iyyar APC domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Gombe Ismaila Uba Misilli ya fitar, an bayyana cewa Pantami ya zo matsayi na biyu a zaɓen bayan Dr. Jamilu Isiyaku Gwamna wanda ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye na kuri’u 247,161.

Sanarwar ta ƙara da cewa Pantami ya fafata ne tare da wasu manyan ‘yan takara, ciki har da tsohon Ministan Sufuri Sa’id Ahmed Alkali wanda shi ma ya samu kuri’u 11,612 a sakamakon zaɓen.

Shugaban Kwamitin Gudanar da Zaɓen Fidda Gwanin APC a jihar Sani Danladi ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da bin ƙa’idoji da dokokin jam’iyyar da kuma na hukumar zaɓe.

A wani jawabi da aka rawaito cewa ya gabatar, Babangida ya bayyana damuwarsa kan yadda manyan dattawan Arewa da malamai ...
21/05/2026

A wani jawabi da aka rawaito cewa ya gabatar, Babangida ya bayyana damuwarsa kan yadda manyan dattawan Arewa da malamai da shugabanni ke raguwa sakamakon mutuwa, yana mai cewa akwai buƙatar sabbin shugabanni su ɗauki nauyin gyara yankin da ci gabansa.

Ya ce a lokacin mulkinsu sun yi ƙoƙarin samar da ci gaba ga Arewacin Najeriya, inda ya bayar da misalin mayar da babban birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja domin samar da daidaito da cigaban ƙasa baki ɗaya.

Babangida ya ƙara da cewa lokaci yana tafiya don haka ya kamata shugabannin Arewa su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban yankin domin amfanin al’ummar Najeriya gaba ɗaya.

Sai dai ana shawartar jama’a da su riƙa tantance bayanai da kalaman siyasa, musamman waɗanda ka iya haifar da rarrabuwar kawuna ko tayar da ƙabilanci, domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

DA DUMI-DUMI: Manyan Ƴan Takarar APC Sun Fara Janyewa daga takara.Daga cikin waɗanda s**a janye akwai Siminalayi Fubara,...
21/05/2026

DA DUMI-DUMI: Manyan Ƴan Takarar APC Sun Fara Janyewa daga takara.

Daga cikin waɗanda s**a janye akwai Siminalayi Fubara, Isa Ali Ibrahim Pantami, Saidu Alkali da kuma Sadiq Baba Abubakar.

Pantami da Sa’idu Alƙali sun zargi jam’iyyar da rashin adalci da kuma karya dokokin zaɓe, yayin da Sadiq Baba Abubakar ya bayyana cewa ya daina siyasa gaba ɗaya.

Lamarin na nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara tsananta a APC gabanin zaɓen 2026.

DA DUMI-DUMI: Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na takarar gwamnan Jihar G...
19/05/2026

DA DUMI-DUMI: Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na takarar gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin APC, bisa zargin take haƙƙin tsarin zaɓe da kuma rashin bin tanade-tanaden dokar zaɓe.

A cikin sanarwar da aka fitar, Pantami ya bayyana cewa nan gaba kaɗan za su bayyana matsayarsu ga magoya bayansu da sauran masu ruwa da tsaki.

Sanarwar ta ƙara da cewa tafiyar “Pantamiyya” na ci gaba da tsayawa kai da fata wajen tabbatar da shugabanci nagari a jihar Gombe da ma Najeriya baki ɗaya, tare da jajircewa wajen yaƙi da rashin adalci ta hanyar bin doka da oda.

Pantami ya bayyana cewa tun bayan amsa kiraye-kirayen shugabanni, matasa, mata da sauran al’umma da s**a buƙaci ya tsaya takara, ya nuna cikakken biyayya ga jam’iyyar APC ta hanyar bin dukkan ƙa’idoji, cika sharuɗɗa da kuma mutunta tsarin da jam’iyyar ta shimfiɗa domin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

Abba Sani Pantami
All Progressives Congress
Professor Isa Ali Pantami
Map Radio & Tv
BBC Hausa

Gwamnan jihar Neja Umaru Mohammed Bago, ya buƙaci alhazan jihar da su zama jakadu na gari yayin gudanar da aikin Hajjin ...
11/05/2026

Gwamnan jihar Neja Umaru Mohammed Bago, ya buƙaci alhazan jihar da su zama jakadu na gari yayin gudanar da aikin Hajjin bana a ƙasar Saudi Arabia.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake yi wa rukuni na farko na alhazan jihar bankwana kafin tafiyarsu zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Ya shawarci alhazan da su kasance masu ɗa’a, ladabi da kuma kyawawan halaye domin su wakilci jihar Neja da Najeriya ta hanya mai kyau a idon duniya.

04/05/2026

Shugabanci yana bukatar gogaggu kuma masana ta kimiyya da fasahar zamani musamman shugaba irin malam Pantami.

Abba Sani Pantami
All Progressives Congress
BBC Hausa
Gombe State
Professor Isa Ali Pantami

Address

Tunga Lowcost Minna
Minna
11

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when MGC Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share