
20/09/2025
Ƴan Achaba Na Cigaba Da Zanga-Zanga A Cikin Garin Bauchi
Ƴan achaba a garin Bauchi sun shiga zanga-zanga suna nuna ƙorafi kan yadda ake cafke musu babura bisa rashin lambar allo (plate number), lambar jiki (body number), da kuma takardar lasisin tuki.
Bayan sun isa ofishin hukumar da ke kula da ababen hawa domin bayyana damuwarsu, rikici ya kaure wanda ya tilasta jami’an tsaro shiga tsakani don kwantar da tarzoma.
Ƴan achaban sun bazu cikin unguwanni daban-daban na Bauchi, suna zagaye suna neman a saurare su. Hotuna daga wurin sun nuna yanda lamarin ya ɗauki hankalin jama’a da hukumomin tsaro.
Ana sa ran hukumomi za su yi duba na musamman don warware matsalar cikin lumana.